Ƙaunataccen Annabina

MANYAN ZUNUBAI

Manyan zunubai saba’in da biyu su ne:

1. Kashe mutum ba bisa haƙƙi ba.

2. Yin zina.

3. Yin luwaɗi.

4. Shan giya da kowane irin abin sha mai maye. [Shan biya haram ne.]

5. Yin sata.

6. Ci da shan abubuwan maye don jin daɗi.

7. Karɓar dukiyar wani da ƙarfi, wato ƙwace.

8. Yin shaidar ƙarya. [Shaidar zur].

9. Cin azumin Ramadan a gaban Musulmi ba tare da uzuri ba.

10. Karɓa da bayar da riba.

11. Yawan rantsuwa.

12. Saɓa wa iyaye, tayar musu.

13. Barin sadar da zumunci [ziyara] ga dangi salihai da suke mahrami.

14. Barin yaƙi a lokacin yaƙi da gudu daga gaban maƙiya.

15. Cin dukiyar maraya ba bisa haƙƙi ba.

16. Rashin amfani da ma’auni da mudu bisa gaskiya.

17. Yin salla kafin lokacinta ko bayan lokacinta.

18. Ɓata wa ɗan’uwa mumini rai. [Zunubi ne mafi girma fiye da rushe Ka’aba. Bayan kafirci, wanda ya fi ɓata wa Allahu Ta’ala rai, babu babban zunubi kamar ɓata wa zuciya rai.]

19. Faɗar maganar da Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) bai faɗa ba, da danganta ta gare shi.

20. Karɓar cin hanci.

21. Gujewa shaidar gaskiya.

22. Rashin bayar da zakkar dukiya da ushurinta.

23. Mai iko, idan ya ga mummuna, ya ga mai aikata zunubi, bai hana ba.

24. Ƙona dabba mai rai a wuta.

25. Mantawa da karatun Alƙur’ani mai girman ɗaukaka bayan an koye shi.

26. Yanke ƙauna daga rahamar Allah Mai girman ɗaukaka.

27. Cin amanar mutane, Musulmi ne ko kafiri.

28. Cin naman alade.

29. Rashin son ko ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah (ridwanullahi ta’ala alaihim ajma’in) da zaginsa.

30. Ci gaba da cin abinci bayan ciki ya ƙoshi.

31. Mata, gudu daga shimfiɗar mijinta.

32. Mata, zuwa ziyara ba tare da izinin mijinta ba.

33. Kiran mace mai mutunci karuwa.

34. Annamimanci, wato ɗaukar magana tsakanin Musulmi. 35. Nuna wa wani al’aura. [Al’aurar namiji tsakanin cibiya da gwiwa ce; ta mace kuwa, gashinta, hannunta da ƙafarta.] Kallon al’aurar wani ma haram ne.

36. Cin mushe da ciyar da wani da shi. 37. Cin amana. 38. Yin gulmar Musulmi. 39. Hassada.

40. Yin shirka da Allah Mai girman ɗaukaka. 41. Yin ƙarya. 42. Girman kai, ganin kai fiye da wasu.

43. Marar lafiya da yake gab da mutuwa ya ɓoye dukiya daga magada. 44. Zama marowaci, mai tsananin rowa.

45. Son duniya.

46. Rashin jin tsoron azabar Allahu Ta’ala. 47. Rashin yin imani da cewa haram haram ne.

48. Rashin yin imani da cewa halal halal ne. 49. Gaskata duban bokaye da labarin gaibi da suke bayarwa. 50. Barin addini, zama murtaddi.

51. Kallon matar wani ko ƴarsa ba tare da uzuri ba. 52. Mata, sa tufafin maza. 53. Maza, sa tufafin mata. 54. Aikata zunubi a Haramin Ka’aba. 55. Kiran salla da yin salla kafin lokaci ya yi.

56. Saɓa wa umarnan ma’aikatan gwamnati da dokoki, tayar musu.

57. Kamanta al’aurar matarsa da al’aurar uwarsa. 58. Zagin uwar matarsa.

59. Nuna wa juna makami.

60. Ci da shan ragowar kare. 61. Gori da kyautar da ya yi. 62. Sa alharini [ga maza]. 63. Dagewa a kan jahilci. [Rashin koyon aƙidar Ahlus-Sunna, farillai, haramai da kowane ilimi da ya zama dole.]

64. Yin rantsuwa da wani abu ban da Allahu Ta’ala da sunayen da Musulunci ya sanar.

65. Gujewa ilimi.

66. Rashin fahimtar cewa jahilci masifa ce.

67. Dagewa a kan maimaita ƙaramin zunubi. 68. Yawan dariya da ƙyalƙyali ba tare da larura ba.

69. Zama da janaba har tsawon lokacin da sallar wani lokaci za ta kuɓuce. 70. Kusantar mata a lokacin haila da jinin haihuwa.

71. Rera waƙa. Rera waƙoƙin lalata, amfani da kiɗa da kayan kiɗa. 72. Kashe kai, wato mutum ya kashe kansa.

Kyawawan ɗabi’u

Musulunci yana umarni da yin ado da kyawawan ɗabi’u, da tsarkake nafsi daga miyagun halaye, da zama mai kyawawan halaye, da kamun kai da kunya ta kowace fuska. Ilimin da yake koyar da waɗannan ilimomi da hanyoyi ana kiransa tasawwufi.

Kamar yadda ilimin likitanci yake koyar da ilimomin da suka shafi lafiyar jiki, haka ma ilimin tasawwufi yake koyar da kuɓutar zuciya da ruhi daga miyagun halaye. Yana nisantar da mutum daga miyagun ayyuka, waɗanda suke alamomin cutar zuciya, yana kuma sa a aikata kyawawan ayyuka da ibada saboda neman yardar Allah.

Musulunci yana umarni da fara koyon ilimi, sannan yin aiki da ibada daidai da abin da aka koya, kuma dukkan waɗannan su kasance saboda neman yardar Allah; a taƙaice: ilimi, aiki da ikhlasi. Idan aka kamanta ɗaukakar mutum ta ruhaniya da samun farin cikin duniya da na Lahira da tashin jirgin sama, imani da ibada su ne kamar jikinsa da injinansa.

Ci gaba a tafarkin tasawwufi kuwa shi ne abin da yake ba shi ƙarfi, wato man fetur ɗinsa. Domin isa ga manufa ana samun jirgin sama, wato ana samun imani da ibada. Domin tashi kuma ana buƙatar ƙarfi, wato ci gaba a tafarkin tasawwufi.

Tasawwufi yana da manufofi biyu:

Ta farko ita ce imani ya zama na zuciya, wato ya kafu a zuciya, kada ya girgiza da tasirin abubuwan da suke kawo shakka. Imanin da aka ƙarfafa da hankali, da dalili da hujja ba ya zama ƙarfaffa haka. Allahu Ta’ala Ya ce a cikin Alƙur’ani mai girma, a aya ta ashirin da takwas ta Suratur Ra’ad, a ma’ana: “Kafuwar imani a zukata, samunsa gindin zama, yana samuwa ne kawai da zikiri.” Zikiri yana nufin tunawa da Allahu Ta’ala a kowane aiki da kowane motsi, da yin aikin da ya dace da yardarSa.

Manufa ta biyu ta tasawwufi ita ce a yi ibadojin da ilimin fiƙihu ya sanar cikin sauƙi da so, da kuma kawar da kasala da wahalhalun da suke tasowa daga nafsi mai umarni da mummuna (nafs-i ammara). Yin ibada cikin sauƙi da so, da nisantar ayyukan da suke zunubi ana ƙyamarsu, yana yiwuwa ne kawai ta hanyar koyon ilimin tasawwufi da ci gaba a wannan tafarki.

Riƙo da tasawwufi ba domin ganin abubuwan da kowa bai sani ba ne, ba domin ba da labarin gaibi ba, ba kuma domin ganin nurori, ruhohi da mafarkai masu daraja ba.

Domin samun ma’arifofi, ilimomi da halayen da ake samu ta tasawwufi, ya wajaba a fara gyara imani, a koyi umarni da hane-hanen Musulunci, a yi aiki da ibada daidai da su. Ai, matuƙar ba a yi waɗannan ukun ba, tsarkake zuciya, wanke ta daga miyagun halaye, da tsarkake nafsi (tazkiya) da horar da shi ba zai yiwu ba.