Ƙaunataccen Annabina

AHKAM-I ISLAMIYYA (AHKAM-I SHAR’IYYA)

Umarni da hane-hanen da addinin Musulunci ya sanar ana kiransu “Ahkam-i shar’iyya” ko “Ahkam-i Islamiyya”. Ana kuma kiransu “Af’al-i mukallafin”.

Wane ne ake kira mukallafi

Maza da mata masu hankali, da suka shiga lokacin balaga, ana kiransu “mukallafi”. Mukallafai za a tambaye su a kan umarni da hane-hanen Allahu Ta’ala. A addininmu, an umarci mukallafi da ya fara yin imani, sannan ya yi ibada. Bayan haka, wajibi ne ya nisanci abubuwan haram da aka hana aikatawa, da kuma ayyukan makaruhi. Hankali ƙarfi ne mai fahimta. An halicce shi ne domin a rarrabe mai amfani da mai cutarwa. Lokacin balaga yana nufin shekarun isa, lokacin da alamun girma suke bayyana a jiki. Shigar yara maza lokacin balaga yana farawa ne idan sun cika shekara goma sha biyu. Akwai alamomi da suke nuna cewa yaro namiji ya shiga lokacin balaga. Idan waɗannan alamomi ba su bayyana ba [ga yaron da ba ya fitar da maniyyi], da ya cika shekara goma sha biyar, a addini ana yanke hukuncin cewa ya shiga lokacin balaga. Balagar ƴaƴa mata kuwa tana farawa ne idan sun cika shekara tara. Idan ko ɗaya daga cikin alamomin balaga bai bayyana ga yarinya ƴar shekara tara ba [wadda ba ta ga jinin al’ada (haila) ba], da ta cika shekara goma sha biyar, ana yanke hukuncin cewa ta shiga lokacin balaga.

Af’al-i mukallafin

Af’al-i mukallafin (ayyukan mukallafai) guda takwas ne: farilla, wajibi, sunna, mustahabbi, mubahi, haram, makaruhi da mufsidi. 1. FARILLA: Abubuwan da Allahu Ta’ala Ya yi umarni da aikata su a fili kuma a yanke, ta hanyar aya mai girma, ana kiransu farilla. Barin farilla haram ne. Wanda bai yi imani da ita ba, bai kuma ba aikata ta muhimmanci ba, ya zama kafiri.

Yin imani, yin alwala, yin wankan janaba (wato wanke jiki duka), yin salla sau biyar a rana, yin azumi a watan Ramadan, bayar da zakka da zuwa aikin hajji idan an wadata, da makamantansu, farilla ne.

2. WAJIBI: Umarnin da aikata su ya zama tabbatacce kamar farilla, su ake kira haka. Misali, yin sallar witiri da sallolin idi, yin layya idan an wadata, bayar da zakkar fid-da-kai (sadaƙatul-fiɗr). Hukuncin wajibi kamar na farilla yake.

3. SUNNA: Abubuwan da Allahu Ta’ala bai bayyana su a fili ba, sai dai Shugabanmu Annabi ne kawai ya yabi aikata su, ko shi kansa yakan aikata su a kai a kai, ko kuma ya ga ana aikata su bai hana ba, su ake kira “sunna”. Ƙin sunna kafirci ne. Wanda ya yarda da ita amma bai aikata ba, ba azaba a kansa. Amma wanda ya bar ta ba tare da uzuri ba, a kai a kai, ya cancanci a zarge shi, a tsawata masa, kuma ya rasa ladarta. Misali, kiran salla (azan), yin iƙama, yin sallar jam’i, sunnonin salla, sallolin sunna, amfani da asuwaki lokacin alwala, ciyar da mutane a daren aure da yi wa ɗa kaciya, da makamantansu. 4. MUSTAHABBI: Ana kuma kiransa mandubi, adabi. Hukuncinsa kamar na sunna ghairu mu’akkada ne. Su ne abubuwan da Shugabanmu Annabi ya aikata a rayuwarsa ko da sau ɗaya ko biyu ne, waɗanda ya so, ya kuma yaba. Misali, sa wa jariri suna a rana ta bakwai, yanka dabbar suna (aƙiƙa) saboda ɗa namiji da ƴa mace, sa kyawawan tufafi, shafa turare mai ƙanshi, da makamantansu. Wanda ya aikata waɗannan ana ba shi lada mai yawa. Wanda bai aikata ba, ba azaba a kansa.

5. MUBAHI: Abubuwan da ba a yi umarni da aikata su ba, ba a kuma hana su ba, ana kiransu mubahi. Idan an aikata su da kyakkyawar niyya akwai lada, idan kuma an aikata su da mummunar niyya akwai azaba. Ayyuka irin su barci, cin abinci iri-iri na halal, sa tufafi iri-iri bisa sharaɗin su kasance na halal, mubahi ne. Idan an aikata waɗannan da niyyar bin Musulunci da riƙo da umarni, sukan zama lada. Ci da sha da niyyar samun lafiya domin yin ibada, haka suke.

“Ku nemi ilimi! Neman ilimi ibada ce. Mai koyar da ilimi da mai koyonsa suna da ladar jihadi” Hadisi mai daraja

6. HARAM: Su ne abubuwan da Allahu Ta’ala Ya hana a fili a cikin Alƙur’ani mai girma, da cewa: “Kada ku aikata!” An hana aikata abubuwan haram da amfani da su gaba ɗaya. Wanda ya ce haram halal ne, ko ya ce halal haram ne, imaninsa ya tafi, ya zama kafiri. Barin abubuwan haram da nisantarsu farilla ne. Kisan kai, zina, luwaɗi, caca, shan giya da kowane irin abin sha mai maye, ƙarya, sata, cin naman alade, jini da mushe, da fitar mata da ƴanmata zuwa kan titi da kawunansu, hannuwansu da ƙafafunsu a buɗe, haram ne, kuma manyan zunubai ne. Idan mutum, yayin da yake aikata waɗannan zunubai, ya karanta basmala, ko ya ƙudurce cewa halal ne, ko kuma bai ba muhimmanci ga haramta su da Allahu Ta’ala Ya yi ba, ya zama kafiri. Idan ya yi imani cewa haram ne, ya aikata su yana tsoro, ba ya zama kafiri. Amma ya cancanci azabar Wuta. Idan ya nace a kan zunubin, ya mutu ba tare da tuba ba, hakan yakan zama sanadin tafiyarsa ba tare da imani ba. 7. MAKARUHI: Abubuwan da Allahu Ta’ala da Muhammadu alaihis-salam ba su so ba, waɗanda suke gusar da ladar ibadu, ana kiransu makaruhi. Makaruhi iri biyu ne: Makaruhi tahrimi: shi ne barin wajibi. Su ne makaruhan da suke kusa da haram. Aikata su yakan jawo azaba. Misali, yin salla lokacin da rana take fitowa, lokacin da take tsaka da lokacin da take faɗuwa. Makaruhi tanzihi: su ne ayyukan da suke kusa da mubahi, wato ayyukan halal, ko kuma waɗanda rashin aikata su ya fi aikata su. Misali, rashin aikata sunnoni ghairu mu’akkada ko mustahabbai.

8. MUFSIDI: A addininmu, su ne abubuwan da suke ɓata wani aiki halattacce (mashru’i) ko wata ibada da aka fara. Kamar ɓata imani da salla, aure (nikahi) da hajji, zakka, saye da sayarwa. Misali, zagin Allah da Littafi kafirci ne, yana ɓata imani. Dariya a cikin salla tana ɓata alwala da salla. Ci ko sha da gangan yayin da ake azumi yana ɓata azumi. Wanda ya aikata farillai, wajibai da sunnoni, ya nisanci haram da makaruhi, ana ba shi sakamako, wato lada. Wanda ya aikata haram da makaruhi, bai kuma aikata farillai da wajibai ba, ana rubuta masa zunubi. Ladar nisantar haram guda ɗaya ta ninka ladar aikata farilla guda ɗaya sau da yawa. Ladar farilla guda ɗaya ta fi ladar nisantar makaruhi guda ɗaya. Ladar nisantar makaruhi kuma ta fi ladar sunna.

Menene ibada?

Ibada ita ce aiwatar da umarni da hane-hanen Allahu Ta’ala, wanda Ya samar da mu da dukkan halittu daga babu, Yake tsayar da su a cikin wanzuwa a kowane lokaci, Yake kare su daga masifu da bala’o’i bayyanannu da ɓoyayyu, kuma a kowane lokaci Yake renon su da ni’imomi da alheri iri-iri. Godiya ga Allahu Ta’ala, wanda Ya aiko wa mutum ni’imomi marasa adadi, gwargwadon ƙarfinsa, aikin ɗan’adam ne. Aiki ne, bashi ne, da hankali yake umarta. Amma mutane, da hankalinsu mai nakasa da gajeriyar ganinsu, ba sa iya samo abubuwan da za su zama godiya da girmamawa ga Allahu Ta’ala. Matuƙar Allahu Ta’ala bai sanar da ayyukan da suke amfani wajen godiya da nuna girmamawa ba, abubuwan da ake zaton yabo ne suna iya zama zagi.

Ga shi, bashin godiya da ayyukan bauta da ya wajaba mutane su aikata ga Allahu Ta’ala da zuciya, da harshe da jiki, su kuma yi imani da su, Allahu Ta’ala ne Ya sanar da su, kuma ƙaunataccen AnnabinSa ne ya isar mana da su. Wato, wajibi ne ga masu hankali su bi Muhammadu alaihis-salam domin su gode wa Allahu Ta’ala, su yi maSa ibada. Wanda ya bi Muhammadu alaihis-salam Musulmi ne. Gode wa Allahu Ta’ala, wato bin Muhammadu alaihis-salam, shi ma ana kiransa “yin ibada”.

Sassan Musulunci

Musulunci kashi biyu ne: A. Sharuɗɗan da ya wajaba a ƙudurce su a zuciya, a yi imani da su. B. Ibadun da ake yi da jiki da zuciya.

Sharuɗɗan da ya wajaba a ƙudurce su a zuciya, a yi imani da su

Imani shi ne: sanin daidai cewa Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) annabin Allahu Ta’ala ne, zaɓaɓɓe ne daga gare Shi, annabi mai isar da labari, a faɗi hakan da imani; a yi imani a taƙaice da abubuwan da ya sanar a taƙaice daga wurin Allahu Ta’ala, a kuma yi imani dalla-dalla da waɗanda ya sanar dalla-dalla, sannan a faɗi kalmar shahada da harshe gwargwadon iko. Imani mai ƙarfi kuwa haka yake: kamar yadda mutum ya yi imani a yaƙinance cewa wuta tana ƙonawa, maciji yana saran mutum ya kashe shi, haka ya ɗaukaka Allahu Ta’ala da siffofinSa a zuci gaba ɗaya, ya yi gaggawa zuwa ga yardarSa da kyawunSa (jamaliSa), ya gudu daga fushinSa da jalalarSa, kuma ya kafa imani a zuciyarsa kafaffe kamar rubutun da aka zana a kan dutsen marmara.

Imani yana da sharuɗɗa shida da dole ne mu yi imani da su.

Su ne:

1. Yin imani da samuwar Allahu Ta’ala da ɗayantakarSa. 2. Yin imani da mala’ikunSa.

3. Yin imani da littattafanSa. 4. Yin imani da annabawanSa. 5. Yin imani da Ranar Lahira. 6. Yin imani da ƙaddara, wato cewa alheri da sharri (kyakkyawa da mummuna) daga Allahu Ta’ala suke.

Ibadun da ake yi da jiki da zuciya

Kowane Musulmi yana da ayyukan da dole ne ya aikata a matsayin ibada. Waɗannan ayyuka ana kiransu sharuɗɗan Musulunci, kuma biyar ne: 1. Faɗin kalmar shahada.

2. Yin salla sau biyar a kowace rana idan lokacinta ya yi. 3. Bayar da zakkar dukiya. 4. Yin azumi a kowace rana a watan Ramadan.

5. Yin aikin hajji sau ɗaya a rayuwa ga mai iko.

“Ƙaramar ibada da aka yi da sani ta fi ibada mai yawa da aka yi ba tare da sani ba” Hadisi mai daraja

Masoyan da suke ƙaunarKa,
Idanunsu ba sa kallon wani,
Waɗanda suka maishe Ka nufinsu,
Ba sa tuna duniya da Lahira.
Waɗanda suka ba Ka zuciyarsu,
Waɗanda ilimi ya isar da su gare Ka,
Waɗanda idanunsu suka gan Ka,
Sa’arsu ba ta taɓa mutuwa.
Ran masoyi ba ya mutuwa,
Jikinsa ba ya ruɓewa har abada,
Duk wanda so ya kashe shi,
Ƙarewa ba ta isa gare shi.
Waɗanda suka sunkuyar da kai ga umarninKa,
Waɗanda suka kai ga haɗuwa da Kai,
Waɗanda suke waƙa kamar tsuntsun bilbilo,
Babu wanda ya san harshensu.
Waɗanda suka san juna da sonKa,
Waɗanda suka so juna saboda Kai,
Waɗanda suka kai ga keɓewa da Kai,
Ba sa tsoron mutuwa ko kaɗan.
In kana da hankali, ya ɗan’uwana,
Son Gaskiya ya zama aikinka,
Wanda bai ɗanɗani zaƙin so ba,
Zuciyarsa ba ta zama tsarkakakkiya.