Ƙaunataccen Annabina

ISTIGFARIN SHUGABANMU ANNABI1

Kamar yadda Shugabanmu Annabi yake mafi ɗaukakar halittu, haka ma shi ne wanda ya fi sanin Allahu Ta’ala yadda ya kamata, kuma ya fi tsoronSa. Duk da cewa Allah Maɗaukakin Sarki Ya kiyaye shi daga aikata zunubi, yakan yi ibada ba fasawa, yana addu’a, yana istigfari ga Allahu Ta’ala. Yakan yi barci a farkon dare (bayan sallar isha’i), a ƙarshensa kuma ya yi ibada. Ibn Abbas ya ba da labari kamar haka: “Wani dare na kwana a gidan uwar muminai Nana Maimuna a matsayin baƙo. Manzon Allah ya yi barci har tsakiyar dare, ko kafin haka kaɗan ko bayan haka kaɗan. Sannan ya farka ya zauna, ya goge alamun barci daga fuskarsa da hannunsa. Ya tashi ya ɗauki butar ruwan da take rataye, ya yi alwala. Ya karanta ayoyi goma masu girma daga ƙarshen Suratu Ali Imrana, ya tsaya salla. Ni ma na tashi na yi alwala kamar yadda Manzon Allah ya yi, na tsaya kusa da wancan Jagora a cikin salla. Manzon Allah ya yi salla raka’a biyu. Sannan ya ƙara raka’a biyu. Bayan haka kuma ya sake yin raka’a biyu. Sannan ya tsaya sallar witiri. Bayan haka ya kwanta har sai da aka yi kiran sallar asuba. Sannan ya tashi ya sake yin salla raka’a biyu, ya fita masallaci ya yi farillar sallar asuba.”2 Uwarmu Nana A’isha ta ba da labari: “Wani dare Shugabanmu Manzon Allah ya yi barci. Da ya farka ya ce: ‘Ya A’isha, idan kin yarda, bari in shagala da ibadar Ubangijina a wannan dare.’ Sannan ya tashi. Ya karanta Alƙur’ani mai girma, ya yi kuka. Har gwiwoyinsa biyu suka jiƙe da hawaye. Ya ci gaba da karatu; yayin da yake karatu, hawayensa masu albarka suka jiƙa duk inda suka taɓa a jikinsa. Wannan hali ya ci gaba har zuwa safiya.

Da safe, Bilalu Habashi ya zo, da ya ga wannan hali, sai ya ce: ‘Uwata da ubana su zama fansa gare ka, ya Manzon Allah! Shin Allahu Ta’ala bai gafarta maka kurakuranka na baya da na gaba ba?’ Manzon Allah ya ce: ’Ya Bilalu! Yaya ba zan zama bawa mai godiya ba, alhali Allahu Ta’ala a wannan dare3 Ya saukar da aya ta ɗari da casa’in mai girma ta Suratu Ali Imrana, wadda ma’anarta: “Lalle a cikin halittar sammai da ƙasa da sauyawar dare da rana bi da bi akwai ayoyi, alamomi masu yawa ga ma’abuta hankali”?’” A cikin hadisi mai daraja da aka sanar a “Muslim” ma ya ce: “Wasu abubuwa sukan zo zuciyata, har nakan yi istigfari ga Allahu Ta’ala saboda su sau saba’in a kowace rana da dare.” Da kuma: “Shamaki yakan samu a zuciyata (wanda yake hana zuwan nurorin Allah). Saboda haka nakan yi istigfari sau 70 a kowace rana.” Da kuma: “Nakan yi istigfari ga Allahu Ta’ala sau ɗari a kowace rana.”4

Tsoron Allahu Ta’ala na Shugabanmu Annabi ya yi yawa ƙwarai, har ba a taɓa ganin ya yi dariya da ƙarfi ba. A cikin hadisi mai daraja da Imam Tirmizi ya riwaito daga Abu Zarr a matsayin marfu’i5, an ce: “Babu shakka ina ganin abin da ba ku gani, ina jin abin da ba ku ji. A sama babu wani wuri wofi ko na yatsu huɗu da mala’iku ba su yi sujada a kai ba. Wallahi, da kun san abin da na sani, da kun yi dariya kaɗan, kun yi kuka da yawa. Da kun fita kan hanyoyi, kuna roƙon Allahu Ta’ala da babbar murya iyakar ƙarfinku.”6

A cikin hadisi mai daraja da Abu Huraira ya riwaito, Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Aikin kowa ba zai kai shi Aljanna ba.” Da aka tambaya: “Kai ma, ya Manzon Allah?”, sai ya ce: “Na’am, ni ma aikina ba zai kai ni Aljanna ba. Sai dai falalar Allahu Ta’ala da rahamarSa su rufe ni.”

Ibn Umar ya ba da labari: “Lokacin da muke tare da Manzon Allah a wani majalisi, mukan ƙidaya yana cewa sau ɗari: ‘Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ka karɓi tubata. Kai ne Mai karɓar tuba kuma Mai jin ƙai.’”7

Anas ɗan Malik ya riwaito: “Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) kullum yakan ce: ‘Allahumma ya muƙalliball-ƙulub, sabbit ƙalbi ala dinik.’”8 A cikin hadisi mai daraja da Tirmizi ya riwaito daga Abu Sa’id Khudri, Shugabanmu Annabi ya ce: “Wanda ya ce sau uku a lokacin da ya shiga shimfiɗarsa: ‘Astagfirullahal-azim allazi la ilaha illa huwal-hayyul-ƙayyum wa atubu ilaih’, ko da zunubansa sun yi yawa kamar kumfar teku, ko yashin ƙasar Tamim, ko adadin ganyayen itatuwa, ko kwanakin duniya, Allahu Ta’ala Zai gafarta masa zunubansa.”

Kamar yadda Bukhari da Muslim suka riwaito, Manzon Allah yakan yi istigfari kamar haka: “Allahummagfirli khaɗi’ati wa jahli wa israfi fi amri wa ma anta a’lamu bihi minni.” (Ya Allah! Ka gafarta mini kurakuran da Ka sani, waɗanda na aikata (da sani ko) ba da sani ba ta hanyar wuce iyakata!)

Kamar yadda aka riwaito daga Abu Musa Ash’ari (radiyallahu anhu), Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) yakan yi istigfari haka ma:

“Allahummagfirli hazli wa jiddi wa khaɗa’i wa amdi wa kullu zalika indi. Allahummagfirli ma ƙaddamtu wa ma akhkhartu wa ma asrartu wa ma a’lantu wa ma anta a’lamu bihi minni, antal-muƙaddimu wa antal-mu’akhkhiru wa anta ala kulli shai’in ƙadir.”9 (Ya Allah! Ka gafarta mini dukkan kurakuran da wataƙila na aikata da wasa, da gaske, da mantuwa da kuma da sani. Ya Allah! Ka gafarta mini abin da na gabatar da abin da na jinkirta, abin da na aikata a ɓoye da a bayyane, kowane irin kurakurana da Ka sani. Kai ne Mai gabatarwa, Kai ne Mai jinkirtawa. Kai ne Mai iko a kan kowane abu.)

Manzon Allah da rana yakan kasance mai azumi,
Da dare kuma yakan tsaya cikin salla.
Idan kai al’ummar wancan Zaɓaɓɓe ne,
Ka kula da sunna da makaruhi kullum.

“Shamaki yakan samu a zuciyata (wanda yake hana zuwan nurorin Allah). Saboda haka nakan yi istigfari sau 70 a kowace rana” Hadisi mai daraja