Ƙaunataccen Annabina

FALALOLIN SHUGABANMU ANNABI

Akwai ɗaruruwan littattafai da suka sanar da falalolin Muhammadu alaihis-salam. Falala tana nufin ɗaukaka. An sanar da wasu daga cikin ɗaukakokinsa a ƙasa: 1. A cikin halittu, nurin Muhammadu alaihis-salam da ruhinsa ne aka fara halitta. 2. Allahu Ta’ala Ya rubuta sunansa a Al’arshi, a Aljannoni da kuma a sammai bakwai. 3. A ganyayen wani fure da yake tsirowa a Indiya an rubuta “La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah”. 4. An ga wani kifi da aka kama a wani kogi kusa da birnin Basra, a gefensa na dama an rubuta “Allah”, a gefensa na hagu kuma “Muhammad”. Al’amura irin waɗannan suna da yawa. A shafi na ɗari biyu na littafin A History of Fishes, da aka buga a Landan a shekara ta 1975, akwai hoton kifin da a wutsiyarsa aka rubuta “Sha’nullah” da haruffan Alƙur’ani mai girma. A cikin bayanin da aka bayar, an sanar da cewa a ɗaya gefen wutsiyar ma an rubuta “La ilaha illallah”. Misalan wannan suna da yawa ƙwarai. 5. Akwai mala’ikun da ba su da wani aiki sai faɗin sunan Muhammadu alaihis-salam. 6. An umarci mala’iku su yi sujada ga Adamu alaihis-salam ne saboda nurin Muhammadu alaihis-salam da yake a goshinsa. 7. Allahu Ta’ala Ya sanar wa dukkan annabawa zuwan Muhammadu alaihis-salam; haka kuma Ya sanar musu su umarci al’ummominsu da su yi imani da shi idan sun riski zamaninsa. 8. Lokacin da zai zo duniya, an ga manya-manyan alamu, waɗanda suke a rubuce a littattafan tarihi da na maulidi. 9. Lokacin da ya zo duniya, an ga cibiyarsa a yanke, kuma an ga shi da kaciya. 10. Da ya zo duniya, shaiɗanu suka kasa hawa sama, suka kasa satar labari daga mala’iku. 11. Lokacin da ya zo duniya, dukkan gumakan da suke doron ƙasa da mutum-mutumin da ake bauta wa suka faɗi rub da ciki. 12. Mala’iku sukan girgiza gadon jaririntakarsa. 13. Lokacin da yake a gadon jaririntaka, yakan yi magana da wata da yake sama. Wata yakan karkata zuwa inda ya yi nuni da yatsansa mai albarka. 14. Ya fara magana tun yana a gadon jaririntaka. 15. Lokacin da yake yaro, idan yana yawo a fili, wani girgije yakan tafi tare da shi a daidai kansa, ya yi masa inuwa. Wannan hali ya ci gaba har zuwa farkon annabtarsa. 16. Kowane annabi yana da hatimin annabta a kan hannunsa na dama. Na Muhammadu alaihis-salam kuwa yana tsakiyar bayansa mai albarka, kusa da ƙashin kafaɗarsa na hagu, a kan zuciyarsa. Lokacin da Jibrilu alaihis-salam ya wanke zuciyarsa ya rufe ƙirjinsa, ya buga hatimi a bayansa da hatimin da ya kawo daga Aljanna.

17. Kamar yadda yake ganin abin da yake gabansa, haka yake ganin abin da yake bayansa.

18. Kamar yadda yake gani a haske, haka yake gani a duhu. 19. Yawunsa ya mayar da ruwa mai ɗaci ya zama mai zaƙi. Ya ba marasa lafiya waraka. Ya zama abinci kamar nono ga jarirai. 20. Idan idanunsa suna barci, zuciyarsa tana a farke. (Dukkan annabawa ma haka suke.) 21. A rayuwarsa bai taɓa yin hamma ba. 22. Guminsa mai albarka yana ƙanshi kamar fure. Wani talaka, lokacin da yake aurar da ƴarsa, ya nemi taimako daga gare shi. A wannan lokaci ba shi da abin da zai bayar. Ya zuba daga guminsa a cikin wata ƙaramar kwalba ya ba shi. Da yarinyar nan ta shafa shi a fuskarta da kanta, sai gidanta ya riƙa ƙanshi kamar miski. Gidanta ya shahara da sunan “gida mai ƙanshi”. 23. Duk da cewa matsakaicin tsayi ne, idan yana tare da dogaye, yakan bayyana ya fi su tsayi. 24. Idan ya yi tafiya a hasken rana da na wata, inuwarsa ba ta faɗuwa ƙasa. 25. Ƙuda, sauro da sauran ƙwari ba sa sauka a jikinsa da tufafinsa. 26. Tufafinsa na ciki, ko nawa ya sanya su, ba sa yin datti. 27. Duk lokacin da ya yi tafiya, mala’iku sukan zo a bayansa. Saboda haka yakan sa Sahabbansa su yi tafiya a gaba, ya ce: “Ku bar bayana ga mala’iku.”1 28. Idan ya taka kan dutse, sawun ƙafarsa yakan zauna a kan dutsen. Idan yana tafiya a kan yashi kuwa, ba ya barin ko alamar sawu. Idan ya yi bayan gari, ƙasa takan tsage, fitsari da makamantansa su kasance a cikin ƙasa. (Dukkan annabawa ma haka suke.) 29. A cikin mutane da mala’iku, shi aka fi ba wa ilimi. Duk da cewa shi ummiyyi ne, wato bai koyi kome daga wurin kowa ba, Allahu Ta’ala Ya sanar da shi kowane abu. Kamar yadda aka sanar wa Adamu alaihis-salam sunan kowane abu, shi ma an sanar da shi sunan kowane abu da iliminsa. 30. An sanar da shi sunayen al’ummarsa, da jikunansu, da dukkan abubuwan da za su faru a tsakaninsu. 31. Hankalinsa ya fi na dukkan mutane yawa. 32. An ba shi dukkan kyawawan halayen da za su iya samuwa a mutane. Da aka ce wa babban mawaƙi Umar Ibnul-Farid: “Don me ba ka yabi Manzon Allah ba?”, sai ya ce: “Na fahimci cewa ƙarfina ba zai isa yabonsa ba. Ban sami kalmar da zan yabe shi da ita ba.”

“Ba zan yarda wani daga cikin al’ummata ya zauna a Wuta ba” Hadisi mai daraja

33. A cikin kalmar shahada, a kiran salla, a iƙama, a tashahhudin salla, a addu’o’i masu yawa, a wasu ibadu da huɗubobi, a wurin yin nasiha, a lokutan wahala, a kabari, a Mahshar, a Aljanna da kuma a harshen kowace halitta, Allahu Ta’ala Ya sanya sunansa kusa da sunanSa. 34. Mafi ɗaukakar ɗaukakokinsa ita ce kasancewarsa Habibullah. Allahu Ta’ala Ya mai da shi masoyi, aboki gare Shi. Ya ƙaunace shi fiye da kowa, fiye da kowane mala’ika. Ya ce: “Idan Na sanya Ibrahim Khalili, kai kuwa Na sanya ka Habibi gare Ni.”

35. Aya mai girma, wadda ma’anarta: “Zan ba ka duk abin da kake so har ka yarda (har ka ce “ya isa”)”2, tana yin alkawarin cewa Allahu Ta’ala Zai ba AnnabinSa dukkan ilimomi, dukkan ɗaukakoki, hukunce-hukuncen Musulunci, taimako da rinjaye a kan maƙiyansa, buɗe-buɗe da nasarori ga al’ummarsa, a Ƙiyama kuma kowane irin ceto da bayyanuwa (tajalli). Lokacin da wannan aya mai girma ta zo, ya dubi Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ba zan yarda wani daga cikin al’ummata ya zauna a Wuta ba.” 36. Allahu Ta’ala, a cikin Alƙur’ani mai girma, Ya yi wa kowane annabi magana da sunansa; Muhammadu alaihis-salam kuwa Ya yi masa magana da “Ya ManzoNa! Ya AnnabiNa!” 37. Yakan yi magana da kowane karin harshen Larabci a sarari ƙwarai, cikin sauƙin fahimta. Masu zuwa daga wurare daban-daban su yi tambaya, yakan amsa musu da karin harshensu. Masu ji sukan yi mamaki. Yakan ce: “Allahu Ta’ala Ya tarbiyyantar da ni da kyau ƙwarai.”3

38. Yakan bayyana abubuwa da yawa da kalmomi kaɗan. Hadisansa masu daraja fiye da dubu ɗari suna nuna cewa shi “Jawami’ul-Kalim” ne.

Wasu malamai sun ce: “Muhammadu alaihis-salam ya sanar da ginshiƙai huɗu na addinin Musulunci da hadisai huɗu:

- ‘Ana ƙima ayyuka bisa niyya.’4

- ‘Halal a bayyane yake, haram a bayyane yake.’5

- ‘Ya zama dole mai ƙara ya kawo shaida, wanda ake ƙara kuma ya yi rantsuwa.’6 da kuma

- ‘Imanin mutum ba ya cika har sai ya so wa ɗan’uwansa na addini abin da yake so wa kansa.’7 Na farko daga cikin waɗannan hadisai huɗu shi ne ginshiƙin ibada; na biyu, na mu’amala (mu’amalat); na uku, na khusumat, wato al’amuran adalci da siyasa; na huɗu kuma na ilimin ladabi da ɗabi’u.”8

39. Muhammadu alaihis-salam kiyayayye (masun) ne kuma ma’asumi (kuɓutacce daga zunubi) ne. Da sani ko ba da sani ba, babba ko ƙarami, kafin shekara arba’in ko bayanta, bai taɓa aikata wani zunubi ba. Ba a taɓa ganin wani mummunan aikinsa ba. 40. An umarci Musulmi su yi wa Muhammadu alaihis-salam sallama a lokacin da suke zaune a cikin salla, ta hanyar karanta “Assalamu alaika ayyuhan-nabiyyu wa rahmatullahi”. Yin sallama ga wani annabi ko ga mala’iku a cikin salla bai halatta ba. 41. A cikin hadisi ƙudusi an ce: “Da ba kai ba, da ban halicci kome ba!”9

42. Sauran annabawa sun amsa ƙagen kafirai da kansu. Ƙagen da aka yi wa Muhammadu alaihis-salam kuwa, Allahu Ta’ala ne Ya amsa, Ya kare shi. 43. Adadin al’ummar Muhammadu alaihis-salam ya fi jimillar adadin al’ummomin sauran annabawa yawa. Sun fi su ɗaukaka kuma sun fi su daraja. An sanar a cikin hadisai masu daraja cewa kashi biyu cikin uku na waɗanda za su shiga Aljanna daga wannan al’umma ne. 44. Ladan da za a ba Manzon Allah ya fi ladan da za a ba sauran annabawa ninkin-ba-ninkin.

Wanda ya yi karɓaɓɓiyar ibada ko aikin alheri, za a ba malaminsa lada daidai da wanda aka ba shi. Za a ba malamin malaminsa ninki huɗu, malamin wannan ninki takwas, malamin wannan kuma ninki goma sha shida; ta haka, har zuwa ga Manzon Allah, za a ba kowane malami ninki biyu na ladan ɗalibinsa. Misali, za a ba malaminsa na ashirin lada 524.288. Za a ba Muhammadu alaihis-salam lada daga kowane aiki na kowane ɗaya daga cikin al’ummarsa.

Idan aka yi tunanin adadin ladan da za a ba Muhammadu alaihis-salam daga kowane aiki bisa wannan lissafi, babu wanda ya san yawan dukkansu sai Allahu Ta’ala. An sanar da cewa magabata na ƙwarai (salaf salihin) sun fi waɗanda suka zo bayansu falala da ɗaukaka. Ta fuskar adadin lada, wannan fifiko a bayyane yake. 45. An haramta kiransa da sunansa, da ɗaga murya a wurinsa, da kiransa daga nesa, da wuce gabansa a hanya. Al’ummomin sauran annabawa sukan kira annabawansu da sunayensu. 46. Ya ga Jibrilu alaihis-salam a siffar mala’ika sau biyu. Babu wani annabi da ya gan shi a ainihin siffarsa. 47. Jibrilu alaihis-salam ya zo masa sau dubu ashirin da huɗu. A cikin sauran annabawa, wurin Musa alaihis-salam ne ya fi zuwa. Wannan zuwa ya faru sau ɗari huɗu.

“Wanda ya yi ƙiyayya da Ahlul-Baitina munafuki ne” Hadisi mai daraja

48. Isra’filu alaihis-salam ma ya zo wa Muhammadu alaihis-salam sau da yawa. Sauran annabawa (alaihimus-salawatu wat-taslimat) Jibrilu alaihis-salam kaɗai ya zo musu. 49. Roƙon Allahu Ta’ala da rantsuwa da Muhammadu alaihis-salam ya halatta, amma da sauran annabawa da mala’iku bai halatta ba. 50. An haramta wa wasu auren matan Muhammadu alaihis-salam bayansa, kuma ta wannan fuska ne aka sanar da cewa su uwayen muminai ne.

Matan sauran annabawa (alaihimus-salawatu wat-taslimat) ko dai sun cutar da su, ko kuma ba su amfane su ba. Matan Muhammadu alaihis-salam masu albarka (radiyallahu ta’ala anhunna) kuwa sun zama masu taimakonsa a al’amuran duniya da Lahira, sun yi haƙuri da talauci, sun yi godiya, kuma sun yi hidima mai yawa wajen yaɗa Musulunci. 51. Dangantaka ta fuskar nasaba da sababi, wato ta fuskar jini da aure, ba ta da amfani a Ƙiyama. Amma dangin Manzon Allah ba sa cikin wannan hukunci. 52. Ɗaukar sunan Manzon Allah yana da amfani a duniya da Lahira. Muminai na gaskiya masu ɗauke da sunansa ba za su shiga Wuta ba. 53. Kowace maganarsa, kowane aikinsa daidai ne. Allahu Ta’ala Yana tabbatar da kowane ijtihadinsa. 54. Ƙaunarsa farilla ce ga kowa. Ya ce: “Wanda yake ƙaunar Allahu Ta’ala yana ƙaunata.” Alamar ƙaunarsa ita ce bin addininsa, tafarkinsa, sunnarsa da ɗabi’unsa. A cikin Alƙur’ani mai girma an umarce shi ya ce: “Idan kun bi ni, Allahu Ta’ala Zai ƙaunace ku.”

55. Ƙaunar Ahlul-Baitinsa wajibi ce. Ya ce: “Wanda ya yi ƙiyayya da Ahlul-Baitina munafuki ne.” Ahlul-Baiti su ne danginsa waɗanda aka haramta musu karɓar zakka. Waɗannan su ne matansa da muminan da suke daga zuriyar kakansa Hashim, wato waɗanda suke daga zuriyar Aliyu, da Aƙil, da Ja’afar Ɗayyar da Abbas.

56. Ƙaunar dukkan Sahabbansa wajibi ce. Ya ce: “Kada ku yi ƙiyayya da Sahabbaina bayana! Ƙaunarsu ƙaunata ce. Ƙiyayya da su ƙiyayya da ni ce. Wanda ya cutar da su, ya cutar da ni. Wanda ya cutar da ni kuwa, ya cutar da Allahu Ta’ala. Allahu Ta’ala Yana azabtar da wanda ya cutar da Shi.”

57. Allahu Ta’ala Ya halitta wa Muhammadu alaihis-salam mataimaka biyu a sama da biyu a ƙasa. Su ne Jibrilu, Mika’ilu, Abubakar da Umar (radiyallahu ta’ala anhum ajma’in).10 58. Kowane mutum, namiji ko mace, da ya mutu bayan ya balaga, za a tambaye shi a kabarinsa game da Muhammadu alaihis-salam. Kamar yadda za a ce: “Wane ne Ubangijinka?”, haka za a ce: “Wane ne Annabinka?” 59. Karanta hadisai masu daraja na Muhammadu alaihis-salam ibada ce. Ana ba mai karantawa lada.

Don karanta hadisi mai daraja, mustahabbi ne a yi alwala, a sanya tufafi masu tsabta, a shafa turare, a ajiye littafin hadisi mai daraja a wuri mai tudu, mai karantawa kada ya tashi tsaye saboda waɗanda suka shigo daga waje, masu saurare kuma kada su yi magana da juna. Fuskokin waɗanda suke karanta hadisai masu daraja kullum sukan kasance masu nuri, masu haske kuma kyawawa. A lokacin karatun Alƙur’ani mai girma ma ya zama dole a kiyaye waɗannan ladubba. 60. Azra’ilu alaihis-salam ya zo a siffar mutum don ya karɓi ruhinsa mai albarka. Ya nemi izinin shiga. 61. A cikin kabarinsa yana raye da rayuwar da ba mu sani ba. A kabari yana karatun Alƙur’ani mai girma, yana salla. (Dukkan annabawa ma haka suke.) 62. Mala’ikun da suka ji Musulman da suke yi wa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) salati a ko’ina a duniya sukan zo kabarinsa su sanar da shi. Dubban mala’iku suna ziyartar kabarinsa a kowace rana. 63. Ƙasar da take cikin kabarinsa ta fi kowane wuri, ta fi Ka’aba da Aljannoni falala. 64. Ana nuna masa ayyukan al’ummarsa da ibadunsu kowace safiya da yamma. Yakan ga masu aikata su ma, kuma yakan yi addu’a a gafarta wa masu zunubi. 65. Ziyartar kabarinsa mustahabbi ce ga mata ma. Sauran kaburbura kuwa, ya halatta su ziyarce su a lokutan da babu cunkoso kawai, da tufafin da suka dace da Musulma. 66. Kamar yadda yake a lokacin da yake raye, bayan wafatinsa ma, a ko’ina a duniya, a kowane lokaci, Allahu Ta’ala Yakan karɓi addu’ar waɗanda suke tawassuli da shi, wato waɗanda suke roƙo saboda alfarmarsa da darajarsa.

Wani mutumin ƙauye ya zo kusa da hubbarensa ya ce: “Ya Ubangijina! Ka umarci a ƴanta bawa. Wannan AnnabinKa ne. Ni ma ɗaya ne daga cikin bayinKa. Saboda alfarmar AnnabinKa, Ka ƴanta ni daga wutar Jahannama!” Sai aka ji wata murya: “Ya bawaNa! Don me ka nemi a ƴanta kai kaɗai? Don me ba ka nemi a ƴanta dukkan bayiNa ba? Tafi! Na ƴanta ka daga Wuta.”

Hatim Asam, ɗaya daga cikin shahararrun waliyyai, ya tsaya kusa da hubbaren Manzon Allah ya ce: “Ya Ubangijina! Na ziyarci kabarin AnnabinKa. Kada Ka mayar da ni hannu wofi!” Sai aka ji wata murya: “Ya bawaNa! Na karɓi ziyararka ga kabarin MasoyiNa. Na gafarta maka, kai da waɗanda suka yi ziyara tare da kai.”

Imam Ahmad Ƙasɗalani (rahmatullahi alaihi) ya ce: “Na sha fama da wata cuta shekaru da yawa, likitoci kuma suka kasa samun maganinta. Wani dare a Makka na yi ta roƙon Manzon Allah ƙwarai. A wannan dare na ga wani mutum a mafarki. A takardar da take hannunsa na karanta: ‘A nan an rubuta maganin cutar Ahmad Ƙasɗalani da izinin Manzon Allah.’ Da na farka, cutata ta gushe.” Ƙasɗalani ya ƙara da cewa: “Wata ƙaramar yarinya ta kamu da cutar farfaɗiya. Na yi ta roƙon Manzon Allah ƙwarai don ta warke. A mafarki wani mutum ya kawo mini aljanin da ya jefa yarinyar cikin cutar. Ya ce: ‘Manzon Allah ne ya aiko maka da shi.’ Na yi fushi da aljanin, na yi masa tsawa. Ya rantse mini cewa ba zai cutar da yarinyar ba, sai na farka. Na sami labarin cewa yarinyar ta warke daga cutar farfaɗiya.”

67. A Ranar Ƙiyama Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ne zai fara tashi daga kabari. A jikinsa za a sami tufafin Aljanna. Zai tafi filin Mahshar a kan Buraƙ. A hannunsa za a sami tutar da ake kira “Liwa’ul-Hamd”. Annabawa da dukkan mutane za su tsaya a ƙarƙashin wannan tuta. Dukkansu za su shiga ƙunci ƙwarai saboda jira na shekara dubu. Mutane za su je bi da bi wurin annabawa Adamu, Nuhu, Ibrahim, Musa da Isa (alaihimus-salam), su roƙe su su yi ceto don a fara hisabi. Kowannensu zai kawo uzuri, ya ce yana jin kunyar Allahu Ta’ala kuma yana tsoronSa, ya kuma ƙi yin ceto. Sannan, da suka je wurin Manzon Allah suka roƙe shi, zai yi sujada, ya yi addu’a, kuma za a karɓi cetonsa. Da farko za a yi hisabin al’ummarsa, su ne za su fara ƙetare Siraɗi, su ne za su fara shiga Aljanna. Za su haskaka duk wurin da suka je.

Lokacin da Nana Fatima take ƙetare Siraɗi, za a ce: “Kowa ya rufe idanunsa! Ƴar Muhammadu alaihis-salam tana zuwa.”

68. Sunan matsayin Manzon Allah a Aljanna Wasila ne. Wannan shi ne mafi girman daraja a Aljanna. A can ne tushen itacen Sidratul-Muntaha yake, wanda reshe ɗaya daga cikin rassansa yake kaiwa ga kowane ɗaya daga cikin mutanen Aljanna. Ni’imomi za su zo wa mutanen Aljanna ta waɗannan rassa.

69. A zamanin Adamu alaihis-salam ma, a cikin kiran salla ana faɗin sunan Muhammadu alaihis-salam.

70. A cikin Attaura, Injila da Zabura an siffanta Muhammadu alaihis-salam, da halifofinsa huɗu, da Sahabbansa da wasu daga cikin al’ummarsa da kyawawan siffofi, an kuma yabe su. Allahu Ta’ala Ya fitar da kalmar “Muhammadu” daga sunanSa Mahmud, Ya sanya wa HabibinSa suna. Allahu Ta’ala Ya ba HabibinSa ma sunayen Ra’uf da Rahim daga cikin sunayenSa. 71. Lokacin da yake ɗan shekara uku, da lokacin da aka sanar da shi annabta yana ɗan shekara arba’in, da lokacin da aka kai shi Mi’iraji yana ɗan shekara hamsin da biyu, mala’iku sun tsaga ƙirjinsa. Sun wanke zuciyarsa da ruwan Aljanna a cikin kwanon da suka kawo daga Aljanna. 72. Ya ga da idanunsa taurari bakwai da suke cikin tarin taurarin da ake kira “Suraiyya”, wanda yake kusa da taurarin Saur (sa, bijimi), ya kuma sanar da adadinsu. Ana kiran wannan tarin taurari Parwin da Ülker ma. 73. An sami waɗanda suka sha jinin ƙahonsa. Da suka sha shi, ya ce: “Wutar Jahannama ba za ta ƙone shi ba.” 74. Ɗaya daga cikin manyan mu’ujizozinsa kuma ita ce kai shi Mi’iraji. An kai shi daga Makka zuwa Ƙudus da dabbar Aljanna da ake kira Buraƙ. Daga nan aka kai shi sammai da Al’arshi. An nuna masa abubuwan al’ajabi. Ya ga Allahu Ta’ala da idon kansa, ta hanyar da ba a sani ba. (Amma wannan gani ya faru ne a wajen duniyar abin duniya, wato a duniyar Lahira.) Nan take aka dawo da shi gidansa. Ba a ba wani annabi mu’ujizar Mi’iraji ba.

75. Ya zama farilla ga al’ummarsa su yi masa salati da sallama sau ɗaya a rayuwarsu. Allahu Ta’ala da mala’iku ma suna yi masa salati da sallama.

“Ina son annabta a matsayin bawa” Hadisi mai daraja

76. Da dare, a lokacin da yake a farke, a lokacin barci, a lokacin da yake shi kaɗai, a cikin taron jama’a, a tafiya, a gida, a yaƙi, lokacin dariya, lokacin kuka, zuciyarsa mai albarka kullum tana tare da Allahu Ta’ala. A wasu lokuta kuwa, tana tare da Allahu Ta’ala kaɗai, ba da kowa ba.

Don ya iya gudanar da ayyukansa na duniya, ya kuma mayar da zuciyarsa mai albarka zuwa duniyar ƴan Adam, yakan zo wurin matarsa A’isha (radiyallahu anha) ya ce: “Ya A’isha! Ki yi magana da ni kaɗan (don in dawo hayyacina)”, bayan haka kuma ya tafi ya yi wa Sahabbansa nasiha, ya shiryar da su. Yakan yi sunnar sallar asuba a gidansa, bayan ya yi magana kaɗan da A’isha (radiyallahu anha), sai ya tafi masallaci don ya yi wa Sahabbansa limancin farilla. Wannan hali yana daga cikin abubuwan da suka keɓanta da annabta (khasa’is). Da ya fita waje ba tare da ya yi magana da A’isha (radiyallahu anha) ba, saboda bayyanuwar Allah (tajalli) da nurori, da babu wanda zai iya kallon fuskarsa. 77. Bai nemi matsayi da mulki ba, ya roƙi annabta da talauci. Wata safiya, yayin da yake magana da Jibrilu alaihis-salam, ya ce a wannan dare babu ko loma ɗaya ta abinci a gidansu. A wannan lokaci Isra’filu alaihis-salam ya zo ya ce: “Allahu Ta’ala Ya ji abin da ka faɗa, Ya kuma aiko ni. Idan ka so, kowane dutse da ka shafa da hannunka ya zama zinariya, ya zama azurfa, ya zama zumurrudu. Idan ka so, ka yi annabta a matsayin sarki.” Manzon Allah ya ce sau uku: “Ina son annabta a matsayin bawa.”

78. Sauran annabawa (alaihimus-salawatu wat-taslimat) sun yi annabta a wani ƙayyadadden zamani, a wata ƙayyadaddiyar ƙasa. Muhammadu alaihis-salam kuwa an aiko shi annabi ga dukkan mutane da aljanu da suke doron ƙasa har zuwa Ranar Ƙiyama. Akwai kuma malaman da suka sanar da cewa shi annabin mala’iku ne ma, da dabbobi, da tsirrai, da abubuwa marasa rai, a taƙaice, na dukkan halittu.

79. Rahamarsa da amfaninsa sun bazu ga dukkan halittu. Amfaninsa ga muminai a bayyane yake. Kafiran zamanin sauran annabawa (alaihimus-salawatu wat-taslimat) an azabtar da su a duniya, an halaka su. Waɗanda ba su yi imani da shi ba kuwa, ba a azabtar da su a duniya ba. Wata rana ya ce wa Jibrilu alaihis-salam: “Allahu Ta’ala Ya sanar da cewa ni rahama ne ga talikai. Shin kai ma ka sami rabo daga rahamata?” Jibrilu ya ce: “Kullum ina cikin tsoron yadda ƙarshena zai kasance a gaban girman Allah da razanarSa. Lokacin da ka kawo ayoyin da suka sanar da cewa ni amintacce ne (aya ta 20 da ta 21 ta Suratut Takwir), da wannan yabo na tsira daga wannan mummunan tsoro, na sami natsuwa. Akwai rahamar da ta fi wannan girma?” 80. Allahu Ta’ala Ya so Muhammadu alaihis-salam ya yarda. (Kamar yadda muka sanar a falala ta talatin da biyar, Allahu Ta’ala Zai ba shi abin da yake so har sai ya yarda. An sanar da wannan a Suratud Duha.)

81. A cikin littafin “Mawahib-i Ladunniyya” an ce wannan hadisi mai daraja: “Na roƙi Ubangijina kada al’ummata ta haɗu gaba ɗaya a kan ɓata (dalala). Ya karɓa” shahararre ne.

A cikin wani hadisi mai daraja kuma ya ce: “Allahu Ta’ala Ya kiyaye ku daga abubuwa uku. Na farko, Ya kiyaye ku daga haɗuwa a kan ɓata. Na biyu, wanda ya mutu da cuta mai yaɗuwa yakan sami ladan shahidi. Na uku, idan Musulmi biyu salihai suka yi shaida a kan wani Musulmi cewa: ‘Mutumin kirki ne’, wannan Musulmi zai shiga Aljanna.”

A cikin wani hadisi mai daraja ya ce: “Saɓanin Sahabbaina rahama ce a gare ku” da kuma “Saɓanin al’ummata (rabuwarsu zuwa mazhabobi a cikin aiki) rahama ce.” Al’ummarsa sukan sami saɓani yayin da suke ƙoƙarin neman gaskiya da daidai. Wannan ƙoƙari nasu kuwa yakan zama sanadin rahama. Mutane biyu ne suka musanta wannan hadisi mai daraja: ɗaya majini, na biyu mulhidi. Majini shi ne mai makirci wanda yake mayar da addini hanyar samun ribar duniya. Mulhidi kuwa shi ne ɓatacce wanda ya zama kafiri ta hanyar fassara ayoyi masu girma bisa muradun duniya. Yahya ɗan Sa’id ya ce malaman Musulunci masu sauƙaƙawa ne. A kan wani aiki, ɗaya ya ce halal ne, wani kuma ya ce haram ne. Abin da suka ce halal ne ga mutanen kirki, a zamanin ɓarna suka ce haram ne. Hadisan nan masu daraja na sama suna nuna cewa ijma’in al’umma, wato haɗuwar maganar malaman da ake kira mujtahidai, yana daga cikin adillar shari’a (hujjojin shari’a). Wato ɗaya ne daga cikin mabuɓɓugai huɗu na ilimin addini, kuma mazhabobi huɗu gaskiya ne. Mazhabobi rahamar Allahu Ta’ala ce ga Musulmi. 82. Ƴaƴan Manzon Allah mata masu albarka da matansa (radiyallahu ta’ala anhunna) su ne mafi ɗaukakar matan duniya. Dukkan Sahabbansa ma su ne mafi ɗaukakar dukkan mutane, ban da annabawa. Biranensa, Makka al-Mukarrama sannan Madina al-Munawwara, su ne mafi darajar wuraren doron ƙasa. Raka’a ɗaya ta sallar da aka yi a cikin masallacinsa mai daraja, ana rubuta mata ladan raka’a dubu. Sauran ibadu ma haka suke.

Tsakanin kabarinsa da mimbarinsa lambun Aljanna ne. Ya ce:

“Wanda ya ziyarce ni bayan wafatina kamar wanda ya ziyarce ni ina raye ne. Muminin da ya rasu a ɗaya daga cikin Haramaini za a tashe shi a Ranar Ƙiyama amintacce.” Ana kiran biranen Makka da Madina Haramaini. 83. Zuriyar kowa tana ci gaba ta ɗansa. Zuriyar Muhammadu alaihis-salam kuwa daga ƴarsa Fatima take. An sanar da wannan a cikin hadisi mai daraja ma. 84. Kowane mutum yana da wani aboki daga aljanu. Wannan shaiɗan kafiri ne. Yakan yi ƙoƙarin ƙwace imaninsa, ya sa shi aikata zunubi ta hanyar waswasi. Manzo alaihis-salam ya kawo aljanin da yake abokinsa ga imani.

85. Lokacin da Manzon Allah (sallallahu ta’ala alaihi wa sallam) zai yi wafati, Jibrilu alaihis-salam ya zo, ya kawo sallama daga Allahu Ta’ala, ya kuma ce Allah Yana tambayar halinsa. Ya sanar da cewa zai yi wafati. Ya ba da bushara masu yawa a kansa da al’ummarsa.

Ba zan karɓi duniya a maimakon ƙurar ƙafarka ba, ya Manzon Allah!
Ba zan musanya zaren gashinka da sammai bakwai ba, ya Manzon Allah!
Abin da Siddiƙ yake nema kuskurenka guda ɗaya ne kawai, ya Manzon Allah!
Muradin Irfan ya zama ƙura a ƙafarka ne, ya Manzon Allah!