Ƙaunataccen Annabina

HILYA-I SA’ADAT

Ana kiran siffar zahiri ta Habibi Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) “Hilya-i Sa’adat”. Malaman Musulunci sun rubuta a sarari, da hujjoji da takardun shaida, dukkan gaɓoɓin Muhammadu alaihis-salam da ake gani, da siffarsa, da halayensa, da kyawawan ɗabi’unsa, da dukkan rayuwarsa har zuwa mafi ƙanƙantar bayanai. An tattaro waɗannan bayanai daga hadisai masu daraja, waɗanda su ne maganganun Shugabanmu Annabi da kansa, da kuma labaran da Sahabbansa suka sanar. Ana kiran littattafan da suka ƙunshi waɗannan littattafan sira. A cikin dubban littattafan sira, mafi shaharar littattafan da suka sanar da hilya-i sa’adat ta Shugabanmu Annabi su ne “Ash-Shama’ilur-Rasul” na Imam Tirmizi, “Shifa-i Sharif” na Ƙadi Iyad, littattafan “Dala’ilun-Nubuwwa” na Imam Baihaƙi da na Abu Nu’aim Isfahani, da kuma littafin Imam Ƙasɗalani mai suna “Mawahib-i Ladunniyya”. A cikin hadisai masu daraja da kuma labaran da Sahabbai masu girma suka sanar, an bayyana hilya-i sa’adat ta ƙaunataccen Annabinmu kamar haka: “Fuska mai albarka ta Abin Alfaharin Halittu da dukkan gaɓoɓinsa masu daraja da muryarsa mai albarka sun fi fuskokin dukkan mutane da gaɓoɓinsu da muryoyinsu kyau.

Fuskarsa mai albarka ɗan zagaye take, a lokacin da yake cikin farin ciki kuwa takan haskaka kamar wata.1 Farin cikinsa yakan bayyana a goshinsa mai albarka.

Yadda Shugabanmu Manzon Allah yake gani da rana, haka yake gani da dare. Kamar yadda yake ganin waɗanda suke gabansa, haka yake ganin waɗanda suke bayansa. Idan zai duba gefe ko baya, yakan juya da dukkan jikinsa ya duba. Yakan fi duban ƙasa fiye da sama. Idanunsa masu albarka manya ne, gashin idanunsa dogaye ne. A cikin idanunsa masu albarka akwai ɗan ja, ƙwayar idanunsa baƙa ƙirin ce, kuma da dare yakan shafa kwalli a idanunsa. Goshin Abin Alfaharin Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) a buɗe yake.

Girarsa masu albarka sirara ne, tsakanin girarsa biyu a buɗe yake. Jijiyar da take tsakanin girarsa biyu takan kumbura idan ya yi fushi. Hancinsa mai albarka kyakkyawa ne ƙwarai, tsakiyarsa ɗan ɗagagge ne. Kansa mai albarka babba ne. Bakinsa mai albarka ba ƙarami ba ne. Haƙoransa masu albarka farare ne, na gaba kuma a tazarce suke. Idan ya yi magana, kamar nuri yake fita daga tsakanin haƙoransa. A cikin bayin Allahu Ta’ala ba a ga wanda ya fi shi fasaha da daɗin magana ba.

Da Abin Alfaharin Talikai ya kai shekara arba’in,
Aka ɗora masa rawanin manzanci a kansa.
Kullum murya take zuwa: “Ya Amin,
Na sanya ka rahama ga talikai.”

“Na tambayi babban fadan kowace coci da na shiga game da siffofin Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) da hilyarsa (siffarsa ta zahiri), na kuma ajiye dukkansu ɗaya bayan ɗaya a cikin ƙwaƙwalwata. Da na koma Madina, na ba Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) labarin dukkansu. Ya ji daɗin haka” Mughira ɗan Shu’uba (radiyallahu anhu)

Alƙur’ani mai girma ya sauka aya bayan aya da hujjoji bayyanannu,
Mu’ujizozi iri-iri masu yawa suka bayyana.
Ko da yake wancan tsarkakke duka nuri ne,
A kowace gaɓarsa akwai mu’ujizozi.
Da farko dai, inuwar jikinsa mai albarka
Ba ta taɓa faɗuwa ƙasa ba.
Jikinsa daga kai har ƙafa nuri ne,
A bayyane yake: nuri ba ya da inuwa.
Haka kuma, a kan kansa mai albarka, a kowane lokaci,
Wani girgije yakan zama masa inuwa.
Duk inda ya tafi, shi ma yakan tafi tare da shi,
Kullum yakan tsaya a kan kansa.
Mu’ujizar da take cikin idanunsa masu albarka,
Yadda take, ita ma in faɗa muku.
Kamar yadda yake gani a sarari a gabansa,
Haka nan yake gani a bayansa nan take.
Ku ji kuma game da hancinsa mai albarka,
Ku dubi yadda mu’ujiza take a cikinsa.
Lokacin da Jibrilu Amin ya sauko da wahayi,
A sa’ar da ya rabu da sama nan take,
Yakan ji ƙanshin Jibrilu,
Yakan san cewa ya sauko da wahayi.
Idan wancan mai fuska kamar wata ya motsa leɓensa,
Faifan rana a sama ma yakan motsa.

Maganganunsa masu albarka suna da sauƙin fahimta ƙwarai, suna ɗaukar zukata, suna jan rayuka. Idan ya yi magana, kalmomi sukan jeru kamar lu’ulu’u. Da mutum ya so ya ƙidaya, zai iya ƙidaya kalmominsa. Wani lokaci yakan maimaita sau uku don a fahimta sosai. (A Aljanna za a yi magana kamar yadda Muhammadu alaihis-salam yake magana.) Muryarsa mai albarka takan isa inda muryar kowa ba ta isa. Abin Alfaharin Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) mai sakin fuska ne. Yakan yi dariya da murmushi, haƙoransa na gaba masu albarka su bayyana.

Idan ya yi dariya, nurinsa yakan haska a kan bangwaye. Kukansa ma, kamar dariyarsa, mai sauƙi ne. Ba ya dariya da ƙarfi, ba ya kuma kuka da babbar murya. Amma idan ya yi baƙin ciki, hawaye sukan zubo daga idanunsa masu albarka, a kuma ji ƙara daga ƙirjinsa mai albarka. Yakan yi kuka idan ya yi tunanin zunuban al’ummarsa, saboda tsoron Allahu Ta’ala, idan ya ji Alƙur’ani mai girma, wani lokaci kuma yayin da yake salla. Yatsun Abin Alfaharin Talikai masu albarka manya ne, hannuwansa masu albarka masu nama ne. Cikin tafukansa masu albarka faɗaɗɗu ne. Ƙanshin dukkan jikinsa ya fi miski daɗi. Jikinsa mai albarka mai laushi ne kuma mai ƙarfi. Anas ɗan Malik ya ce: “Na yi wa Manzon Allah hidima shekara goma. Hannuwansa masu albarka sun fi alharini laushi.”

Fatarsa mai albarka ta fi miski da furanni ƙanshi. Hannuwansa, ƙafafunsa da yatsunsa masu albarka dogaye ne. Yatsun ƙafafunsa masu albarka manya ne, tafukan ƙafafunsa ba su da zurfi sosai, kuma masu laushi ne. Cikinsa mai albarka faɗaɗɗe ne, yana daidai da ƙirjinsa. Ƙasusuwan kafaɗunsa manya ne, ƙirjinsa mai albarka faɗaɗɗe ne. Zuciyar Shugabanmu Manzon Allah mai daraja wurin duban Allah ce. Manzo Mafi Daraja ba dogo sosai ba ne, ba kuma gajere ba ne. Idan wani dogo ya zo kusa da shi, sai ya fi shi tsawo. Idan ya zauna, kafaɗarsa mai albarka takan fi na dukkan mazauna tsayi.

Gashin kansa mai albarka da gemunsa ba masu tsananin murɗewa ba ne, ba kuma miƙaƙƙu sosai ba, a halitta masu ɗan lanƙwasa ne. Gashin kansa mai albarka dogo ne; da farko yakan bar gashin goshi, daga baya kuma ya fara raba shi biyu. Gashin kansa mai albarka, wani lokaci yakan bar shi ya yi tsawo, wani lokaci kuma yakan yanke, ya gajarta shi. Ba ya rina gashin kansa da gemunsa. Lokacin da ya yi wafati, adadin furfura a gashin kansa da gemunsa bai kai ashirin ba. Yakan rage gashin bakinsa mai albarka. Tsawon gashin bakinsa da siffarsa daidai suke da girarsa masu albarka. Yana da wanzamai na musamman da suke yi masa hidima.

Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ba ya rabuwa da asuwakinsa da matsefinsa. Idan yana tsefe gashin kansa mai albarka da gemunsa, yakan duba madubi. Abin Alfaharin Halittu yakan yi tafiya da sauri yana duban gabansa, kuma idan ya wuce ta wani wuri, ana sanin haka ta ƙanshinsa mai daɗi. Shugabanmu Manzon Allah Balarabe ne. Wato fuskarsa fara ce gauraye da ja, kyakkyawa ƙwarai, mai nuri kuma mai sanyin gani.” Wanda ya ce Shugabanmu Annabi baƙi ne, ya zama kafiri. “Arab” a lugga yana nufin “kyakkyawa”. Misali, “lisanul-arab” yana nufin “kyakkyawan harshe”. A ma’anar isɗilahi kuwa, wato a ilimin ƙasa, Balarabe yana nufin wanda aka haife shi ya girma a yankin da ake kira Ƙasar Larabawa, ya tashi da yanayin wurin, iskarsa, ruwansa da abincinsa, kuma yake daga jinin mutanen wurin. Kamar yadda ake kiran waɗanda suka fito daga jinin Anatoliya Turkawa, waɗanda aka haifa suka girma a Bulgariya Bulgariyawa, waɗanda suke Jamus kuma Jamusawa, haka nan Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ma Balarabe ne, domin an haife shi a Yankin Larabawa. Larabawa farare ne, masu launin alkama. Musamman ma zuriyar Annabinmu farare ne kuma kyawawa ƙwarai. Tun asali kakansu Ibrahim alaihis-salam ma fari ne, kuma ɗan wani mumini fari mai suna Taruh ne, daga mutanen birnin Basra. Azar kafiri ba uban Ibrahim alaihis-salam ba ne, baffansa ne kuma uban riƙonsa.

“Na yi wa Manzon Allah hidima shekara goma. Hannuwansa masu albarka sun fi alharini laushi. Fatarsa mai albarka ta fi miski da furanni ƙanshi” Anas ɗan Malik (radiyallahu anhu)

Kyawun Abdullahi, uban ƙaunataccen Annabinmu, ya bazu har zuwa Masar, kuma saboda nurin da yake a goshinsa, ƴanmata kusan ɗari biyu sun zo Makka don su aure shi. Amma nurin Muhammadu alaihis-salam ya zama rabon Amina. Baffansa Abbas da ɗan Abbas, Abdullahi, su ma farare ne. Zuriyar Annabinmu har zuwa Ranar Ƙiyama ma kyawawa ne kuma farare. Sahabban Manzon Allah ma farare ne kuma kyawawa. Usman (radiyallahu anhu) fari ne, gashinsa yana da launin zinariya. Dihya Kalbi, jakadan da Shugabanmu Manzon Allah ya aika zuwa ga gwamnatin Hiraƙl, Sarkin Rum, kyakkyawa ne ƙwarai, kuma idan ya bi tituna, ƴanmatan Rum sukan fito don su ga fuskarsa. Jibrilu alaihis-salam sau da yawa yakan zo a siffar Dihya (radiyallahu anhu). Ƴan asalin Masar, Sham, Afirka, Sisiliya da Sifen ba Larabawa ba ne. Amma da yake Larabawa sun fito daga Yankin Larabawa suka zo waɗannan wurare don yaɗa Musulunci a duniya, a yau su ma suna nan a waɗannan wurare. Haka nan suna nan a Anatoliya, a Indiya da wasu ƙasashe. Amma a yau ba daidai ba ne a kira mutanen ko ɗaya daga cikin waɗannan ƙasashe Larabawa.

Mutanen Masar masu launin ruwan ƙasa ne. Mutanen Habasha baƙaƙe ne. Ana kiran waɗannan Habashawa. Ana kiran mutanen Zanjibar Zanjawa. Su ma baƙaƙe ne. Ƙaunar dangin Annabinmu da jikokinsa da girmama su ibada ce. Kowane Musulmi yana ƙaunarsu. Baƙaƙen fallahai, Habashawa da Zanjawa da suka zo Anatoliya a matsayin baƙi sun gabatar da kansu a matsayin Larabawa don a girmama su a kuma karrama su; Musulman Anatoliya masu tsarkin zuciya kuwa suka gaskata maganarsu, suka ƙaunace su. Domin a cikin wannan ƙauna babu bambancin baƙi da fari. Musulmi baƙi ya fi kafiri fari ɗaukaka, daraja da ƙaunatuwa sau da yawa. Kasancewar mutum baƙi ba ya rage darajar imani. Sayyidina Bilalu Habashi da Usama, wanda Manzon Allah yake ƙauna ƙwarai, baƙaƙe ne. Kafirai Abu Lahab da Abu Jahal, waɗanda kowa ya san mugunta da ƙasƙancinsu, farare ne. Allahu Ta’ala ba launin mutum Yake ba wa daraja ba, ƙarfin imaninsa da taƙawarsa Yake ba wa daraja. Amma gabatar da kai da baƙaƙe suka yi a matsayin Larabawa ya amfani maƙiyan Musulunci, Yahudawa. A gefe ɗaya, sun gabatar da baƙaƙen mutane a matsayin ƙasƙantattu kuma abin ƙyama. Sun yi amfani da su a matsayin bayi.

A ɗaya gefen kuma, suna kiran baƙaƙen kuliyoyi da karnuka da “Arab, Arab”, suna kiran baƙaƙen hotuna da zane-zanen barkwanci da suka yi a jaridu da mujallu Larabawa, suka yi ƙoƙarin nuna wa matasa cewa Balarabe baƙi ne, ta haka kuma su nisantar da ƴaƴan Musulmi daga Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam).

Dukkan kyawawan ɗabi’u sun tattaru a cikin ƙaunataccen Annabinmu. Kyawawan ɗabi’unsa na baiwa ne (wahbi), wato Allahu Ta’ala ne Ya ba shi su, ba na neman kai ne (kasbi) ba, wato ba daga baya ya same su ta hanyar ƙoƙari ba. Bai taɓa la’antar wani Musulmi da ambaton sunansa ba, kuma bai taɓa dukan kowa da hannunsa mai albarka ba. Yakan yi ramuwa saboda Allah; saboda kansa kuwa bai taɓa rama wa kowa ba. Yakan yi wa danginsa, Sahabbansa da masu yi masa hidima kyakkyawar mu’amala da tawali’u. A cikin gida mai tausasawa ne ƙwarai kuma mai sakin fuska. Yakan je ziyarar marasa lafiya, yakan halarci jana’izu. Yakan taimaki Sahabbansa a ayyukansu, yakan ɗauki ƴaƴansu a hannunsa. Amma zuciyarsa ba ta shagala da waɗannan. Ruhunsa mai albarka yana duniyar mala’iku ne. Wanda ya ga Shugabanmu Manzon Allah ba zato, tsoro yakan kama shi. Da ba don shi da kansa yana tausasawa ba, saboda halayen annabta, da babu wanda zai iya zama a wurinsa, ko ya sami ƙarfin jin maganarsa. Alhali shi kuwa, saboda kunyarsa (haya), ba ya kallon fuskar kowa da idanunsa masu albarka.

Abin Alfaharin Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) shi ne mafi karamcin mutane. Ba a taɓa ganin ya ce “babu” ga abin da aka roƙe shi ba. Idan abin da aka roƙa yana nan, yakan bayar; idan babu, ba ya amsawa.

Yana da kyautatawa masu yawa, falaloli masu yawa, har ma sarakunan Rum da sarakunan Farisa, ko wani sarki ko ɗaya, ba su iya yin falala irin tasa ba. Amma shi da kansa yana son rayuwa cikin ƙunci; yakan yi irin rayuwar da ci da sha ba sa ma zuwa ransa. Ba ya cewa: “Ku kawo abinci mu ci” ko “Ku dafa abinci kaza”. Idan aka kawo abinci yakan ci, kowane irin ƴaƴan itace aka ba shi yakan karɓa. Wani lokaci har watanni yakan ci kaɗan, yana son yunwa. Wani lokaci kuma yakan ci da yawa. Ba ya shan ruwa a ƙarshen cin abinci. Yakan sha ruwa a zaune.2 Idan yana cin abinci tare da wasu, yakan janye hannunsa bayan kowa.3 Yakan karɓi kyautar kowa. Yakan ba wa wanda ya kawo kyauta ninkin-ba-ninkin fiye da kyautarsa.

Sanya tufafi iri-iri ɗabi’arsa ce. Idan jakadun ƙasashen waje suka zo, yakan yi ado, ya sanya tufafi masu daraja kuma kyawawa, ya nuna fuskarsa kyakkyawa. Yakan sanya zoben azurfa mai dutsen aƙiƙ, ya kuma yi amfani da shi a matsayin hatimi. A kan zobensa an rubuta “Muhammadun Rasulullah”. Shimfiɗarsa ta fata ce, cikinta cike da zaren itacen dabino. Wani lokaci yakan kwanta a kan wannan shimfiɗa, wani lokaci a kan fatar da aka shimfiɗa a ƙasa, wani lokaci kuma a kan tabarma ko busasshiyar ƙasa. Yakan kwanta a gefensa na dama, ya sanya tafin hannunsa mai albarka a ƙarƙashin kumatunsa na dama.4 Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ba ya karɓar dukiyar zakka, ba ya cin abubuwa kamar ɗanyen albasa da tafarnuwa, ba ya kuma faɗar waƙa. Idanun Shugabanmu Annabi masu albarka suna barci, amma zuciyarsa mai daraja ba ta barci. Yakan kwanta da yunwa, ya tashi da ƙoshi. Bai taɓa yin hamma ba. Jikinsa mai albarka mai nuri ne, inuwarsa ba ta faɗuwa ƙasa. Ƙuda ba ya sauka a kan tufafinsa, sauro da sauran ƙwari ba sa shan jininsa mai albarka.

Bayan Allahu Ta’ala Ya sanar da cewa shi Manzon Allah ne, shaiɗanu suka kasa hawa sammai su ɗauko labari, bokaye ma suka kasa yin bokanci. Jagoran Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) a yanzu ma yana raye da wata rayuwa da ba mu sani ba. Jikinsa mai daraja ba ya ruɓewa har abada. Wani mala’ika yana tsaye a kabarinsa, yana sanar da shi salati mai daraja da al’ummarsa take yi masa. Ana kiran tsakanin mimbarinsa da kabarinsa mai daraja Rauda-i Muɗahhara. Wannan wuri yana daga cikin lambunan Aljanna. Ziyartar kabarinsa mai daraja ita ce mafi girman ɗa’a kuma mafi darajar ibadu. Manyan Sahabbai masu girma sun bayyana kyawun Shugabanmu Annabi kamar haka. Abu Huraira ya ce: “Ban taɓa ganin wanda ya fi Manzon Allah kyau ba. Kamar rana ce take haskakawa a fuskarsa da dukkan haskenta. Idan ya yi dariya, haƙoransa sukan baza haske a kan bangwaye.”

“Waɗanda suka fi ƙaunata a cikin al’ummata su ne waɗanda za su zo bayana, waɗanda suke sadaukar da iyalansu da dukiyoyinsu don su gan ni” Hadisi mai daraja

Ibn Abi Hala ya ce: “Fuskar Shugabanmu Annabi mai albarka takan haskaka kamar wata a daren goma sha huɗu.” Sayyidina Aliyu ya ce: “Wanda ya gan shi ba zato, tsoro yakan kama shi saboda kwarjininsa. Wanda ya zauna da shi ya san shi kuwa, nan take yakan saba da shi, ya ƙaunace shi.”

Jabir ɗan Samura ya ce: “Manzon Allah ya shafa fuskata da hannunsa mai albarka. A hannunsa na ji ƙanshi mai daɗi da sanyi, kamar an fito da shi yanzu-yanzu daga jakar ɗan aɗɗari, wato mai sayar da turare. Idan Shugabanmu Manzon Allah ya taɓa hannun wani da hannunsa don musafaha, duk yini wannan ƙanshi mai daɗi ba ya gushewa daga hannun mutumin.”5

Uwarmu Nana A’isha ta ce: “Idan Manzon Allah ya shafa kan wani yaro, a cikin sauran yara wannan yaro yakan bayyana nan take saboda ƙanshinsa mai daɗi.”6

Wata rana Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yana barci a gidansa. Ummu Sulaim, uwar Anas ɗan Malik, ta zo. A lokacin barcin, ɗigo-ɗigon gumi suka bayyana a fuskar Shugabanmu Manzon Allah mai albarka. Ummu Sulaim ta fara tattara gumin Shugabanmu Annabi mai albarka. Da ya farka ya tambayi dalili, sai Ummu Sulaim, wadda take ƴar’uwar uwar Shugabanmu Annabi ta shayarwa, ta ce: “Muna haɗa shi da turarenmu. Guminka shi ne mafi kyau kuma mafi daɗin ƙanshin turare.”7

Abu Huraira ya ce: “Ban taɓa ganin wanda ya fi Manzon Allah sauri a tafiya ba. Kamar ƙasa ce take naɗewa a gabansa. Idan muna tafiya tare da shi, mukan yi amfani da dukkan ƙarfinmu, muna tilasta kanmu.”

Shugabanmu Annabi yakan yi magana kyakkyawa ƙwarai. Ya san inda za a fara magana da inda za a ƙarasa ta a mafi kamalar hanya. Maganganunsa, ta fuskar furuci, bayyanannu ne, masu tsananin fasaha da balaga. A cikin maganganunsa da kalmominsa kullum akwai daidaiton ma’ana; da yake ƙarfin bayaninsa yana da matuƙar girma, ba ya gajiya ko kaɗan yayin magana, ba ya kuma shan wahala.

Kyawun Shugabanmu Annabi

Manyan malaman Musulunci da ake kira “ulama’u rasikhin”, waɗanda malamai ne a ilimin zahiri da na baɗini, kuma magadan Shugabanmu Annabi, sun gan shi da dukkan kyawunsa, suka ƙaunace shi. A gaba-gabansu akwai Abubakar as-Siddiƙ. Shi, da ya ga nurin annabta da yake tattare da Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), ya fahimci ɗaukakarsa, kyawunsa da girmansa, ya ƙaunace shi, kuma ya ci gaba a cikin wannan ƙauna har ya kai matsayin da babu wanda ya kai shi. Sayyidina Abubakar a kowane lokaci, duk inda ya duba, yakan ga Shugabanmu Manzon Allah. Wata rana ya bayyana halinsa da cewa: “Ya Manzon Allah! Duk inda na duba, kai nake gani.” Wata rana kuma ya ce: “Da zan musanya dukkan kyawawan ayyukana da kuskurenka (sahwi) guda ɗaya.” Ɗaya daga cikin waɗanda suka fi gani da fahimta da bayyana kyawun Shugabanmu Manzon Allah ita ce uwar muminai, uwarmu Nana A’isha. Nana A’isha malama ce, mujtahida, mai hankali, mai basira, kuma mai iya adabi. Takan yi magana da tsananin balaga da fasaha. Ta san ma’anonin Alƙur’ani mai girma, halal da haram, waƙoƙin Larabawa da ilimin lissafi sosai. Tana da waƙoƙin yabon Manzon Allah. Waɗannan baitoci biyu uwarmu Nana A’isha ce ta faɗe su:

“Idan Manzon Allah ya shafa kan wani yaro, a cikin sauran yara wannan yaro yakan bayyana nan take saboda ƙanshinsa mai daɗi” Nana A’isha (radiyallahu anha)

Wa lau sami’u ahlu Misra ausafa khaddihi,
Lama bazalu fi saumi Yusufa min naƙdin.
Lawa’imu Zalikha lau ra’aina jabinahu,
La’asarna bil-ƙaɗ’il-ƙulubi alal-aidi.
Ma’anarsa:
Da mutanen Masar sun ji kyawun kumatunsa,
Da ba su ba da ko kwabo ɗaya a cinikin Yusufu alaihis-salam ba.
(Da sun ajiye dukkan dukiyoyinsu don su iya ganin kumatunsa.)
Da matan da suka zargi Zulaikha sun ga goshinsa mai haske,
Da sun yanke zukatansu a maimakon hannuwansu (ba za su kuma ji zafinsa ba).

Uwarmu Nana A’isha ta ce: “Wata rana Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yana cire madaurin takalmansa masu albarka, ni kuma ina kaɗin zare. Na dubi fuskarsa mai albarka. Gumi yana ɗiga daga goshinsa mai haske. Kowane ɗigon gumi yana baza nuri ko’ina, yana ɗaukar idanuna. Na yi mamaki har na kasa motsi. Ya dube ni ya ce: ‘Me ya same ki da kika tsaya kina shagala haka?’ Na ce: ‘Ya Manzon Allah! Na rasa kaina ina kallon haskakar nurin fuskarka mai albarka da haskokin da ɗigo-ɗigon gumin da suke goshinka mai albarka suke bazawa.’ Manzon Allah ya tashi ya zo wurina. Ya sumbace ni a tsakanin idanuna, ya ce: ‘Ya A’isha! Allahu Ta’ala Ya ba ki alheri! Kamar yadda kika faranta mini rai, ban iya faranta miki ba.’” Wato ya ce: “Faranta mini rai da kika yi ya fi faranta miki rai da na yi.” Sumbatar da ya yi wa Nana A’isha a tsakanin idanunta masu albarka saboda ta ga Shugabanmu Manzon Allah ne da ƙauna, tana fahimtar kyawunsa. Saboda haka aka yaba mata aka kuma karrama ta.

Layin waƙa:

Albarka ta tabbata ga idanuna, da suke iya ganin kyawunka!

Baiti kuma:

Madalla da waɗancan idanu da suke kallon kyakkyawa!
Madalla da waccan zuciya mai sa’a da take ƙuna saboda shi!

Kyawawan siffofi na zahiri da suka tattaru a jikin Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) mai albarka, waɗanda suke nuna kyawawan siffofin baɗini, ba su taɓa tattaruwa a jikin wani mutum ɗaya ba.

Imam Ƙurɗubi ya riwaito kamar haka: “Kyawun Manzo Mafi Daraja bai bayyana gaba ɗaya ba. Da kyawunsa na haƙiƙa ya bayyana, da Sahabbai masu girma ba za su sami ƙarfin kallonsa ba. Da ya nuna kyawunsa na haƙiƙa, da babu wanda zai jure kallonsa.”

Yusufu alaihis-salam ya bayyana ga mutane da kyawunsa na zahiri, Shugabanmu Manzon Allah kuwa da kyawunsa na baɗini. Da aka ga kyawun Yusufu alaihis-salam, hannuwa suka yanku. Da kamalar Shugabanmu Manzon Allah kuwa, ɗamarun kafirci suka yanku, gumaka suka farfashe, gizagizan kafirci suka watse. Sahabbai masu girma suka tambayi Shugabanmu Annabi: “Ya Manzon Allah! Kai ne ka fi kyau, ko Yusufu alaihis-salam ne ya fi kyau?” Shugabanmu ya amsa da cewa: “Ɗan’uwana Yusufu ya fi ni kyau (sabih), ni kuwa na fi shi sanyin gani (malih). Kyawunsa da ake gani ya fi kyawuna da ake gani yawa.”

A cikin wani hadisi mai daraja Shugabanmu Annabi ya ce: “Kowane annabi da Allahu Ta’ala Ya aiko mai kyakkyawar fuska ne, mai kyakkyawar murya. Annabinku kuwa shi ne mafi kyawun fuska kuma mafi kyawun murya a cikinsu.”

Wani mutum ya zo wurin Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ya Manzon Allahu Ta’ala! Yaushe Ƙiyama za ta tashi?” Shugabanmu Annabi ya ce: “Me ka shirya domin Ƙiyama?” Mutumin ya ce: “Gaskiya, ban shirya wa Ƙiyama da yawan salla, da azumi, da sadaka ba. Amma ina ƙaunar Allahu Ta’ala da ManzonSa.” Sai Shugabanmu Annabi ya ce: “Mutum yana tare da wanda yake ƙauna.”8

Ƙaunar Manzon Allah farillar aini ce a kan dukkan Musulmi.

Idan ƙaunar wancan Jagora ta zauna a cikin wata zuciya, sai rayuwa bisa Musulunci da kaiwa ga daɗin imani da Musulunci, daɗin da ba a ƙoshi da shi, su zama masu sauƙi ƙwarai. Wannan ƙauna takan zama sanadin cikakken bin Shugaban Duniya da Lahira. Da wannan ƙauna ake samun darajar kaiwa ga ni’imomi da albarkoki marasa iyaka, waɗanda ba a iya bayyanawa, waɗanda Allahu Ta’ala Ya karrama HabibinSa da su. Malaman Ahlus-Sunna da littattafansu, waɗanda suke kai kowane Musulmi, ƙarami da babba, kai tsaye zuwa ga ƙaunar Manzon Allah, su ne hujjojin waɗannan albarkoki.

Ya wajaba ga muminin da ya ambaci ko ya ji sunan Manzo alaihis-salam mai albarka ya kasance cikin natsuwa, ladabi da girmamawa da zuciya da jiki, kamar yana zaune a majalisin Manzon Allah mai daraja.

Idan aka sanar da wani abu daga maganganun Shugabanmu Manzon Allah masu albarka ko ayyukansa, mayar da martani gare shi da abin da zai ɗaukaka darajarsa girmamawa ce da mutuntawa gare shi. Rashin siffanta Manzon Allah da kalmomin da ake amfani da su a tsakanin mutane don matsayi ƙasƙantacce kuma maras daraja ma girmamawa ce gare shi.

Misali, ba a ce wa Manzon Allah talaka. Ba a ce masa makiyayi. Idan aka ce: “Shugabanmu Manzon Allah yana son abu kaza”, rashin cewa “Ni kuwa ba na son sa” girmamawa ce gare shi. Haka nan, ga maganar Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam): “Ni ba na cin abinci ina jingine, ina dogara da wani abu”,9 kada a mayar da martani da cewa: “Ni kuwa ina ci ina dogara da wani abu”, sannan a ci abinci a jingine. Kiyaye waɗannan yana cikin girmamawa ga Manzon Allah. Rashin kiyaye su da gangan, da niyyar rashin ba su muhimmanci, yana buɗe ƙofofin kafirci.

Rashin sanya wani littafi ko wani kayan gida a kan Alƙur’ani mai girma da littattafan hadisai masu daraja ma yana cikin girmama Allahu Ta’ala da ManzonSa. Share ƙurar da take a kansu, da rashin zubar da takardar da sunan Allahu Ta’ala mai daraja ko sunayen Shugabanmu Manzon Allah masu albarka suke a cikinta, girmamawa ce ga Allahu Ta’ala da ManzonSa. Ba a yaga irin waɗannan takardu. Ya zama dole a ƙara girmama takardun da aka rubuta da haruffan Musulunci. Idan littattafai da takardun da sunan Allahu Ta’ala mai daraja da ayoyi masu girma suke a cikinsu suka yage saboda tsufa, ya kamata a naɗe su a cikin tsaftataccen zane a binne su a ƙasa, ko a wanke su da ruwa a shafe rubutun da yake kansu, ko a ƙone su. Idan aka ƙone, ana binne tokarsu. Ƙonawa ta fi wankewa da shafe rubutun. Domin ana iya taka ruwan da aka yi amfani da shi wajen wankewa.

Girmamawa da mutunta Madina al-Munawwara, wadda take haramin Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), da nisantar abubuwan da aka haramta a cikinta (ko aikata zunubi), da kuma karrama mutanen Madina al-Munawwara, su ma ana ƙidaya su a cikin girmama Manzon Allah.

Kai ne sarkin mulkin jikina,
Babu shakka, kai ne masoyin raina,
Sezâî ya shafe dukkan abin da yake da shi yanzu,
Falalar da take nan kaɗai, kai ne.
Hasan Sezâî

“Ɗan’uwana Yusufu ya fi ni kyau (sabih), ni kuwa na fi shi sanyin gani (malih). Kyawunsa da ake gani ya fi kyawuna da ake gani yawa” Hadisi mai daraja