SUNAYE MASU ALBARKA NA SHUGABANMU ANNABI
Sunan ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) da aka fi faɗa shi ne “Muhammadu”. Yana nufin “wanda aka yabe shi ƙwarai, wanda aka so shi sosai”. Wannan suna ya zo a cikin Alƙur’ani mai girma sau huɗu: Suratu Ali Imrana, 3:144; Suratul Ahzab, 33:40; Suratul Fat’hi, 48:29 da Suratu Muhammad, 47:2. Isa alaihis-salam ma, kamar yadda aka faɗa a aya ta shida mai girma ta Suratus Saff, ya sanar wa al’ummarsa, a ma’ana, cewa: “Ya Bani Isra’ila! Ni annabin Allah ne zuwa gare ku. Na zo ina mai gaskata Attaura, kuma mai bushara da wani annabi da zai zo bayana, wanda sunansa Ahmad.” Ahmad yana nufin “wanda aka fi yabo, wanda aka fi so”.
Ban da sunayen “Muhammadu” da “Ahmad”, an ambaci ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) a cikin Alƙur’ani mai girma da sunayen Mahmud, Rasul, Nabi, Shahid, Bashir, Nazir, Mubashshir, Munzir, Da’i ilallah, Siraj-i munir, Ra’uf, Rahim, Musaddiƙ, Muzakkir, Muddassir, Abdullahi, Karim, Haƙƙ, Munir, Nur, Khatamun-Nabiyyin, Rahmat, Ni’mat, Hadi, Ɗaha, Yasin… Wasu daga cikin sunayensa masu albarka an ambace su a cikin Alƙur’ani mai girma, wasu a cikin hadisai masu daraja, wasu kuma a cikin littattafai masu tsarki da aka aiko wa annabawan da suka gabata. A wasu hadisai masu daraja sunayen Annabinmu sun zo kamar haka: Mahi, Aƙib, Muƙaffi, Nabiyyur-Rahma, Nabiyyut-Tauba, Nabiyyul-Malahim, Ƙattal, Mutawakkil, Fatih, Khatam, Mustafa, Ummi, Ƙusam (wanda ya tattara kowane alheri a cikinsa). A cikin wani hadisi mai daraja Annabinmu ya ce: “Ina da sunaye biyar keɓantattu gare ni: Ni Muhammadu ne, ni Ahmad ne, ni Mahi ne, wanda Allahu Ta’ala Yake shafe kafirci ta hanyata. Ni Hashir ne, wanda a Ranar Ƙiyama za a tashi mutane a bayana. Ni Aƙib ne, wanda babu annabi bayana.”1
An ba ƙaunataccen Annabinmu laƙabi (kunya) “Abul-Ƙasim” saboda ɗansa Ƙasim, wanda Nana Khadija ta haifa masa, ya kuma rasu yana ƙarami. Haka kuma, tun kafin annabtarsa, saboda ɗimbin kyawawan halayensa da ba su ƙidayuwa, kamar gaskiya, amintaka da riƙon amana da suke tattare da shi, a cikin ƙabilar Ƙuraishawa ana kiransa da sunan “al-Amin”. Ɗaya daga cikin sunayen Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) da suka zo a cikin Alƙur’ani mai girma kuma shi ne kalmar “Yasin” da take a Suratu Yasin, wadda take zuciyar Alƙur’ani mai girma. Sayyid Abdulhakim Arwasi, ɗaya daga cikin manyan malamai masu zurfin ilimi (ulama’u rasikhin), ya ce: “Yasin yana nufin: ‘ya MasoyiNa, mai iyo a cikin tekun yaƙiniNa’, wato: ‘ya MasoyiNa, mai nutso a cikin tekun ƙaunaTa.’” Waɗanda suka ji sunan wannan teku, waɗanda suka gan shi daga nesa, waɗanda suka zo kusa da shi, waɗanda suka shiga cikinsa suka nutsa zuwa zurfin da ya zama rabonsu – dukkansu, a kowane mataki na rayuwarsu, sun yi ta ƙuna da ƙonewa da ƙaunar Manzon Allah, sun bayyana wannan ƙauna tasu da kukan ƙuna, da hawaye na zuciya da kuma baitoci masu ƙona zuciya. Ɗaya daga cikin manya-manyansu kuma shahararrunsu, wanda ya sami babban rabo daga wannan tekun ƙauna, shi ne Maulana Khalid Baghdadi. A cikin ɗaya daga cikin ƙasidunsa da ya bayyana ƙaunarsa da shauƙinsa ga Shugabanmu Manzon Allah, ya rubuta kamar haka:
“Ya Bani Isra’ila! Ni annabin Allah ne zuwa gare ku. Na zo ina mai gaskata Attaura, kuma mai bushara da wani annabi da zai zo bayana, wanda sunansa Ahmad” Saff: 6
Ya Jagoran Talikai, da ƙaunarka nake ƙuna!
Duk inda nake, kyakkyawar fuskarka nake nema.
Kai ne sarkin karagar Ƙaba Ƙausaini, ni kuwa ba kome ba ne,
Har in ce “ni baƙonka ne”, ina ganin rashin ladabi ne.
Kowane abu a duniya saboda darajarka aka halicce shi,
Idan rahamarka ta sauka a kaina ma, wannan lokaci bazarata ce.
Kowa yana zuwa Hijaz don ya yi ɗawafin Ka’aba,
Ni kuwa, da shauƙin haɗuwa da kai, duwatsu nake haurawa.
A mafarki an sa mini rawanin sa’ada a kaina,
Ina jin kamar an yayyafa ƙurar ƙafarka a fuskata.
Ya Jami, tsuntsun waƙar maƙaunata masu yabon Masoyinsu!
Waɗannan rubuce-rubuce a cikin Diwaninka su ne masu fassara mini:
“Kamar kare mai ƙaiƙayi, harshensa a rataye, mai ƙishirwa,
Ina kwaɗayin ɗigo ɗaya daga tekun falalarka.”
Ban da waƙoƙi da yabo da aka rubuta gunduwa-gunduwa don yabon Shugabanmu Annabi, an rubuta littattafai masu yawa a kansa. A cikin marubutansu, har ma waɗanda shahararsu da fasaharsu suka mamaye duniya duka da ƙarnuka, sun bayyana cewa sun kasa yabon Manzon Allah yadda ya kamata. Waɗanda suka gan shi suka ƙaunaci kyawunsa sun yi ƙoƙarin siffanta shi gwargwadon iyawar harsunansu, suka ce ƙarfin ɗan Adam ba ya isa ya bayyana wannan kyau.
A cikin littattafan malaman Musulunci an rubuta ɗaruruwan abubuwan da waɗannan maƙaunata suka sanar. Masu karantawa nan take sukan fahimci cewa Allahu Ta’ala Ya halicci ƙaunataccen AnnabinSa a cikin tsari da ba a iya tunaninsa da kuma kyawun da ba a ƙoshi da kallonsa. Ba tare da sun gan shi ba, sukan ba shi zuciyarsu. Masu ƙaunar Habibullah, a kowane numfashi, a cikin sanyin iskar da take shiga huhunsu, sukan ji daɗin ƙaunarsa. Duk lokacin da suka dubi wata, sukan ji daɗin neman ƙyallin haskokin da suka fito daga idanunsa masu albarka. Kowace zarra ta waɗanda suka sami ko ɗigo ɗaya daga tekun kyawunsa tana cewa:
Wanda ya san kyakkyawan kumatunka, ba ya ko dubin fure,
Wanda ya narke a cikin ƙaunarka, ba ya neman magani!
A cikin wani hadisi mai daraja da aka riwaito daga Anas ɗan Malik an ce: “Babu ɗayanku da ya yi imani har sai na fi ƙaunatuwa a wurinsa fiye da ɗansa, da ubansa da dukkan mutane.”2 Wata rana Sayyidina Umar ya ce wa Shugabanmu Annabi: “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Allahu Ta’ala, ban da raina, kai ne mafi ƙaunatuwa a wurina fiye da kowane abu.” Sai Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Babu ɗayanku da ya yi imani har sai na fi ƙaunatuwa a wurinsa fiye da ransa.” Da jin haka Sayyidina Umar ya ce: “Ya Manzon Allah! Ina rantsuwa da Allahu Ta’ala, wanda Ya aiko maka Alƙur’ani mai girma, kai ne mafi ƙaunatuwa a wurina fiye da raina.” Sai Annabinmu ya ce: “Ya Umar, yanzu (imaninka) ya cika.”
Zamanin sararin samaniya, kwamfutoci,
Abubuwan zamani masu yawa –
Asalinsu duka yana cikin Alƙur’ani,
Kai rahama ne, ya Manzon Allah.
Ka ba da muhimmanci ga gwaji,
Ga koyon ilimi da fasaha,
Ka nuna hanya zuwa gaba,
Kai haske ne, ya Manzon Allah.
Wanda yake ƙaunarka, masoyinmu ne,
Ba tare da kai ba, duniya ta yi mana ƙunci,
Kowane abu saboda kai yake,
Kai ni’ima ne, ya Manzon Allah.
Daga gare ka aka ɗauko tunani,
Ilimi, fasaha da sana’a,
Gabas da Yamma sun amfana,
Kai jagora ne, ya Manzon Allah.
Duk abin da ka faɗa ya tabbata gaskiya,
Tun ƙarni goma sha biyar da suka wuce,
Kai ne Muhammadul-Amin,
Kai adali ne, ya Manzon Allah.
A cikin kyautatawa, a cikin adalci,
A cikin karamci, a cikin daraja,
A cikin jin ƙai, a cikin falala,
Kai abin koyi ne, ya Manzon Allah.
“Babu ɗayanku da ya yi imani har sai na fi ƙaunatuwa a wurinsa fiye da ransa” Hadisi mai daraja
Yadda ake ganin “Ƙubba-i Khadra / Koren Ƙubba” ta masallaci mai albarka na Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) daga waje
