TAWASSULI DA SHUGABANMU ANNABI
A kowane lokaci an yi tawassuli1 da Shugabanmu Annabi – kafin a halicce shi, bayan an halicce shi, a rayuwarsa ta duniya da bayan wafatinsa, a duniyar barzahu (kabari) –, kuma za a yi a Ranar Ƙiyama, bayan tashi daga kabari, a filin Arasat da a Aljanna. Wasila ita ce duk abin da Allahu Ta’ala Ya sanya sanadin kusanci a wurinSa da biyan buƙatu. Tawassuli da Manzo Mafi Daraja, wato riƙon Shugabanmu Manzon Allah tsani (wasila) a wurin Allahu Ta’ala, da neman taimakonsa da cetonsa, halal ne. Waɗannan suna daga cikin abubuwan da magabata na gari (Sahabbai, Tabi’ai da Taba’ut-Tabi’ai), malamai da sauran Musulmi suka yi. Babu wani daga cikin Musulmi da ya ga wannan mummuna. Har zuwa yanzu ba a sami wanda bai karɓi waɗannan ba, in ban da masu ɓatacciyar aƙida. Uban mutane, Adamu alaihis-salam, lokacin da aka saukar da shi doron ƙasa, ya riƙi Shugabanmu Annabi tsani. Ƙaunataccen Annabinmu ya ba da labarin wannan a cikin wani hadisi mai daraja kamar haka: “Lokacin da aka fitar da Adamu (alaihis-salam) daga Aljanna saboda zamewarsa, ya ce: ‘Ya Ubangijina! Ka gafarta mini saboda darajar Muhammadu.’ Allahu Ta’ala Ya ce: ‘Ya Adamu! Ta yaya ka san Muhammadu, alhali Ni ban riga Na halicce shi ba?’ Adamu (alaihis-salam) ya ce: ‘Ya Ubangijina! Lokacin da Ka halicce ni, Ka ba ni rai, da na buɗe idona na duba, na ga a gefen Al’arshi an rubuta: “La ilaha illallah, Muhammadun Rasulullah”. Wanda Ka so sunansa tare da sunanKa, shi ne.’ Allahu Ta’ala Ya ce: ‘Ka faɗi gaskiya, ya Adamu! Daga cikin halittuNa, shi ne wanda Na fi so. Saboda ka nemi gafara saboda darajarsa, Na gafarta maka.’”2 Bisa wata ruwaya kuma Ya ce: “Shi annabi ne da zai zo daga zuriyarka. Da ban halicce shi ba, da ban halicce ka ba, kai da ƴaƴanka. Saboda ka gabatar da shi mai ceto, Na gafarta maka, Na yafe maka.”3
Game da wannan akwai misalai dubbai. Ƴan kaɗan daga cikinsu ga su nan a ƙasa. Wani mutum makaho, wanda idanunsa biyu ba sa gani, ya roƙi Shugabanmu Manzon Allah addu’a domin idanunsa su buɗe. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) kuma ya ce: “Idan kana so, zan yi addu’a. Amma idan ka yi haƙuri, ka jure, ya fi alheri a gare ka.” Musulmin makaho ya ce: “Ba ni da sauran ƙarfin haƙuri. Ina roƙon ka yi addu’a.” Sai Annabinmu ya ce masa: “To, idan haka ne, ka yi alwala, ka karanta wannan addu’a!”:
“Allahumma inni as’aluka wa atawajjahu ilaika bi-Nabiyyika Muhammadin Nabiyyir-rahma. Ya Muhammad! Inni atawajjahu bika ila Rabbi fi hajati hazihi, li-tuƙda li. Allahumma shaffi’hu fiyya.”
Imam Nasa’i, ɗaya daga cikin malaman hadisi, yana sanar da cewa, da wannan mutum ya karanta wannan addu’a, Allahu Ta’ala Ya karɓa, idanunsa suka buɗe. Game da riƙon Shugabanmu Manzon Allah tsani, Sayyidina Usman ɗan Hunaif yana ba da labarin wannan al’amari: “Lokacin da Usman ɗan Affan yake halifa, wani mutum mai babban ƙunci, saboda yana jin kunyar fitowa gaban halifa, ya kawo mini ƙorafinsa. Ni kuma na ce masa: ‘Yi alwala nan take! Je Masjid-i Sa’adat! Ka yi addu’ar da aka ambata a sama, ka faɗi buƙatarka.’ Mutumin nan, bayan ya yi addu’a, ya tafi wurin da halifa yake, aka kai shi gabansa. Halifa ya zaunar da shi a kan sallayarsa, ya saurari ƙorafinsa, ya karɓa. Mutumin nan, da ya ga buƙatarsa ta biya farat ɗaya, ya zo wurina cikin farin ciki, ya ce: ‘Allahu Ta’ala Ya yarda da kai! Da ba ka faɗa wa halifa ba, da ban kuɓuta daga wannan ƙunci ba.’ Ya yi tsammanin cewa ni na yi magana da halifa.”
“(Ya Adamu!) Shi annabi ne da zai zo daga zuriyarka. Da ban halicce shi ba, da ban halicce ka ba, kai da ƴaƴanka. Saboda ka gabatar da shi mai ceto, Na gafarta maka, Na yafe maka” Hadisi ƙudusi
Lokacin da Sayyidina Umar yake halifa, an yi fari. Bilalu ɗan Haris, ɗaya daga cikin Sahabbai masu girma, ya tafi hubbaren Manzon Allah, ya ce: “Ya Manzon Allah! Al’ummarka tana gab da mutuwa saboda yunwa. Ina roƙon ka zama tsani domin a yi ruwan sama.” A wannan dare Shugabanmu Manzon Allah ya bayyana gare shi a mafarki, ya ce: “Je wurin halifa! Ka gaishe shi daga gare ni! Ya fita yin sallar roƙon ruwa!” Da Sayyidina Umar ya fita yin sallar roƙon ruwa, ruwan sama ya fara zuba. Allahu Ta’ala Yakan karɓi addu’o’i saboda waɗanda Yake so. Allahu Ta’ala Ya sanar da cewa Yana son Muhammadu alaihis-salam ƙwarai. Saboda haka, idan wani ya yi addu’a yana cewa: “Allahumma inni as’aluka bi-jahi Nabiyyikal-Mustafa”, ba za a ƙi addu’arsa ba. Duk da haka, riƙon Manzon Allah tsani domin ƙananan al’amuran duniya bai dace da ladabi ba. Burhanuddin Ibrahim Maliki ya ce: “Wani talaka mai tsananin yunwa ya tafi Hujra-i Sa’adat, ya ce: ‘Ya Manzon Allah! Ina jin yunwa.’ Bayan ɗan lokaci wani ya zo, ya kai talakan gidansa, ya ƙosar da shi. Da talakan ya faɗa cewa an karɓi addu’arsa, sai wancan ya ce: ‘Ɗan’uwana! Ka rabu da iyalinka, ka zo daga hanyoyi masu nisa, kana shan wahala, domin ka ziyarci Manzon Allah. Ya dace a fito gaban Manzon Allah saboda loma ɗaya ta gurasa? A wannan gaba maɗaukakiya, ya kamata ka nemi Aljanna da ni’imomi na har abada! Abubuwan da ake nema a nan, Allahu Ta’ala ba Ya ƙin su.’ Waɗanda suka sami darajar ziyarar Manzon Allah, su yi addu’a domin ya yi musu ceto a Ranar Ƙiyama.” Wata rana Imam Abubakar al-Muƙri yana zaune a Masjid-i Sa’adat tare da Imam Ɗabarani da Abush-Shaikh. Da yake kwanaki da dama ba su ci komai ba, yunwa ta tsananta musu. Imam Abubakar, da bai iya jurewa ba, ya ce: “Ina jin yunwa, ya Manzon Allah!”, ya koma wani gefe. Wani mutum daga cikin sayyidai ya zo da barori biyu, ya ce: “Ƴan’uwana! Kun nemi taimako daga kakana Manzon Allah saboda yunwa. Ya umarce ni in ƙosar da ku.” Suka ci abin da ya kawo tare. Ragowar ya bar musu, ya tafi. Ɗaya daga cikin malaman Musulunci, Abu Abdullahi ɗan Nu’uman Marrakushi Tilimsani (683 / 1284 Miladiyya), a littafinsa mai daraja “Misbahuz-Zalam”, ya yi dogon rubutu a kan ɗaruruwan Musulmi da suka sami buƙatunsu da riƙon Shugabanmu Manzon Allah tsani, da addu’o’insu. Ɗaya daga cikin waɗanda suka sami buƙatunsu da riƙon Manzon Allah tsani shi ne Muhammadu ɗan Munkadir. Yana ba da labari kamar haka: “Wani mutum ya ajiye wa babana zinariya tamanin, ya tafi jihadi. Ya ce: ‘Ka adana waɗannan! Kana kuma iya taimakon mai tsananin buƙata da su.’ An yi fari a Madina. Babana ya rarraba zinariyar duka ga waɗanda yunwa ta matsa wa. Mai zinariyar ya zo, ya nema. Babana ya ce: ‘Zo bayan dare ɗaya.’ Ya tafi Hujra-i Sa’adat, ya roƙi Manzon Allah har gari ya waye. A tsakiyar dare wani mutum ya zo, ya ce: ‘Miƙa hannunka!’ Ya ba shi jakar zinariya, sannan ya ɓace daga wurin. Babana, a gida, ya ƙidaya zinariyar, da ya ga tamanin ce, ya yi farin ciki, ya mayar wa mai ita nan take.”
Sayyidina Abu Abdullahi Tilimsani, a wannan littafinsa, yana ba da labarin wani al’amari da ya same shi kamar haka:
“A shekara ta 637 (1239 Miladiyya), mun fita daga kagarar Sadr tare da wata jama’a ta zaɓaɓɓun mutane. A tare da mu akwai wani mutum da yake jagorantarmu. Bayan mun yi tafiya na ɗan lokaci, ruwanmu ya ƙare. Muka fara neman ruwa. Ni kuma a lokacin na tafi domin in biya buƙata. A wannan lokaci wani barci mai tsanani ya kama ni. Na ce: ‘Ko ta yaya, idan za su tafi za su tashe ni’, na kwantar da kaina a ƙasa.
Da na farka, sai na tarar da kaina ni kaɗai a tsakiyar hamada. Abokaina sun manta da ni, sun tafi. Kaɗaici ya sa ni cikin babban tsoro. Na fara tafiya a hamada, dama da hagu. Ban san inda nake ba, ban san inda zan tafi ba. Ko’ina yashi ne sumul. Bayan ɗan lokaci duhu ya yi. Babu ko alamar ayarin da muke tafiya tare. Ni kaɗai nake a cikin duhun dare. Tsorona ya ƙara tsananta. Cikin ruɗu na fara tafiya da sauri. Bayan na yi tafiya na ɗan lokaci, na faɗi ƙasa cikin tsananin ƙishirwa, gajiya da kasala. Na riga na yanke ƙauna da rayuwata, na fara jin cewa mutuwata ta kusa. Ina cikin wani zafi da ba a iya siffantawa; baƙin cikina da damuwata sun kai matuƙa. Farat ɗaya wani tunani ya zo mini. A cikin duhun dare, na tattara dukkan ƙarfina, cikin gaskiya da ikhlasi, na yi nishi a karo na ƙarshe: ‘Ya Manzon Allah! Agaji! Ina roƙon ka taimake ni, da izinin Allahu Ta’ala!’ Da na gama faɗar waɗannan kalmomi kawai, na ji wani yana kirana. Da na kalli gefen da muryar take zuwa, sai na ga, a cikin duhun dare, wani mutum da yake watsa haske a kewayensa, sanye da fararen tufafi tas, wanda ban taɓa ganinsa ba har zuwa wannan lokaci, yana kirana. Ya kusance ni, ya kama hannuna. A wannan lokaci dukkan gajiyata da ƙishirwata suka ɓace. Na zama kamar an sake haifata. Zuciyata ta ƙaunace shi nan take. Muka yi tafiya hannu da hannu na ɗan lokaci. Na ji cewa ina cikin ɗaya daga cikin mafi daɗin lokutan rayuwata. Da muka haye wani tudun yashi, na ga fitilun ayarin da nake tafiya tare da shi, na ji muryoyin abokaina. Muka kusance su. Dabbar da nake hawa tana bin su a baya-baya. Farat ɗaya ta zo, ta tsaya a gabana. Da na ga abin hawana a gabana, na yi sowar farin ciki. Da na yi sowa, mutumin da ya zo tare da ni ya janye hannunsa daga hannuna. Sannan ya kama hannuna, ya ɗora ni a kan abin hawana. Sannan ya ce: ‘Wanda ya nemi wani abu daga gare mu, wanda ya nemi taimakonmu, ba ma mayar da shi hannu wofi’, ya juya, ya tafi. A lokacin na fahimci cewa shi Shugabanmu Manzon Allah ne. Yana juyawa yana tafiya, ana ganin nurin da yake watsawa a kewayensa yana hawa sama a cikin duhun dare. Da ya ɓace daga idona, farat ɗaya hankalina ya dawo jikina. Na yi ta nadama, ina cewa: ‘Yaya ya kasance ban sumbaci hannuwa da ƙafafun Shugabanmu Manzon Allah ba!’, amma lokaci ya wuce, dama ta kuɓuce.” Abul-Khair al-Aƙɗa’ ya yi kwana biyar da yunwa a Madina. Ya zo kusa da Hujra-i Sa’adat, ya yi wa Manzon Allah sallama. Ya sanar da cewa yana jin yunwa. Ya koma wani gefe, ya yi barci. A mafarki ya ga Manzon Allah yana zuwa. A damansa Abubakar as-Siddiƙ yake, a hagunsa Umar al-Faruƙ, a gabansa kuma Aliyu al-Murtada.
Sayyidina Aliyu ya zo, ya ce: “Ya Abul-Khair! Tashi; me ya sa kake kwance? Ga Manzon Allah yana zuwa!” Ya tashi nan take. Manzon Allah ya zo, ya ba shi babbar gurasa. Abul-Khair yana cewa: “Da yake ina da tsananin yunwa, na fara ci nan take. Da na ci rabinta, na farka. Na tarar da sauran rabin a hannuna.”
“Duk wanda wani abu ya cutar da shi, ya yi alwala cikakkiya, ya yi salla raka’a biyu! Sannan ya ce: ‘Ya Ubangijina! Ina roƙonKa. Ina roƙonKa ina riƙon AnnabinKa Muhammadu alaihis-salam, wanda yake rahama ga talikai, tsani. Ya Muhammadu! Ina riƙon ka tsani a wurin Ubangijina domin Ya karɓi buƙatata. Ya Ubangijina! Ka sanya shi mai ceto a gare ni!’” Hadisi mai daraja
Haka kuma an ba da labari a littafin “Misbahuz-Zalam”: Ahmad ɗan Muhammadu Sufi yana cewa: “A hamadar Hijaz ban rage da komai ba. Na zo Madina. A kusa da Hujra-i Sa’adat na yi wa Manzon Allah sallama. Na zauna a wani gefe, na yi barci. Shugabanmu Manzon Allah ya bayyana, ya ce: ‘Ka zo, Ahmad? Buɗe tafin hannunka!’ Ya cika mini tafin hannu da zinariya. Na farka. Hannuwana cike suke da zinariya.” Imam Samhudi ma, a littafinsa mai suna “Tarihin Madina”, yana ba da labarin wani al’amari da ya same shi kamar haka: “Na zubar da makullin ƙofata. Ban same shi ba. Na zo gaban Hujra-i Sa’adat, na ce: ‘Ya Manzon Allah! Na zubar da makullina, ba zan iya shiga gidana ba!’ A wannan lokaci wani yaro ya zo. Yana nuna makullin da yake hannunsa, ya ce: ‘Na sami wannan. Ko naka ne?’”
Kilisli Mustafa Işkî Efendi yana cewa a littafinsa na tarihi “Mevârid-i Mecîdiyye”: “Na zauna a Makka shekara ashirin. Na tara zinariya sittin, a shekara ta 1247 bayan Hijira (1831 Miladiyya) na zo Madina tare da iyalina. Kuɗin sun ƙare a hanya. Na sauka a gidan wani da na sani, na zo Hujra-i Sa’adat. Na nemi taimako daga Manzon Allah. Bayan kwana uku, wani mutum mai daraja ya zo gidan da muke, ya ce ya yi mini hayar wani gida. Ya sa aka kai kayana can. Ya biya kuɗin haya na shekara ɗaya. Bayan ƴan watanni, na yi rashin lafiya, na kwanta wata ɗaya. A gida ba a rage da abin ci ko abin sayarwa ba. Da taimakon matata, na so in hau rufin gida, in fuskanci hubbaren Manzon Allah, in faɗa masa ƙuncina, in nemi taimako. Da na ɗaga hannuwana, sai na ji kunyar neman abin duniya. Ban iya faɗar komai ba. Na sauka ɗakina. Washegari wani ya zo, ya ce wane mutum mai daraja ya aiko mini da waɗannan zinariya kyauta. Na karɓi jakar. Ko da yake rayuwarmu ta daidaita, ban kuɓuta daga rashin lafiya ba. Da taimako na zo gaban Hujra-i Sa’adat, na nemi waraka daga Manzon Allah. Na fita daga masallaci, na yi tafiya zuwa gida ba tare da na nemi taimakon kowa ba. Ina shiga gida, ba a rage da ko alamar rashin lafiya ba. Domin kada idon mutane ya same ni, na fita titi na ƴan kwanaki ina jingine da sanda. Amma kuɗi sun ƙare. Na bar iyalina cikin duhu, na zo Masallacin Annabi. Bayan sallar isha’i na faɗa wa Manzon Allah ƙuncina. A hanya, wani mutum da ban sani ba ya zo wurina, ya sanya mini wata jaka a hannu. A cikinta akwai zinariya arba’in da tara, kowace ta kuruş tara. Na sayi kyandir da abubuwan da ake buƙata, na koma gida.”
A juzu’i na biyu na fassarar littafin “Şakâyık-i Nu’mâniyye” an ce: babban malamin Musulunci Maulana Shamsuddin Muhammad ɗan Hamza Fanari, Shaikhul-Islam na farko na Daular Usmaniyya kuma mujaddadin zamaninsa, labule ya rufe idanunsa. Ya zama ba ya gani. Wata rana da dare, Shugabanmu Manzon Allah ya ce masa a mafarki: “Ka yi tafsirin Suratu Ɗaha!”, sai ya ce: “Kamar yadda ba ni da ƙarfin yin tafsirin Alƙur’ani mai girma a gabanka maɗaukaki, idanuna ma ba sa gani.” Shugabanmu Manzon Allah, likitan annabawa, ya ciro ɗan auduga daga khirƙarsa mai albarka, ya jiƙa shi da yawunsa mai albarka, ya sanya a kan idanunsa. Mulla Fanari ya farka, ya tarar da audugar a kan idanunsa, ya ɗauke ta, ya fara gani. Ya gode wa Allahu Ta’ala, ya yi yabo gare Shi. Ya adana zaren audugar, ya yi wasiyya a sanya shi a kan idanunsa idan ya rasu. Da ya rasu a Bursa a shekara ta 834 (1431 Miladiyya), suka cika wasiyyarsa.
Halifan Abbasiyawa Abu Ja’afar Mansur yana magana da Imam Malik a cikin Masallacin Annabi. Imam Malik ya ce: “Ya Mansur! Wannan Masjid-i Sa’adat ne! Ka yi magana a hankali! Allah Maɗaukaki, da cewarSa a Suratul Hujurat, a ma’ana: ‘Kada ku ɗaga muryoyinku sama da muryar Manzon Allah!’4, Ya tsawata wa wata jama’a. Da aya mai girma ‘Waɗanda suke runtse muryoyinsu a wurin Manzon Allah…’5 kuma, Ya yabi masu magana a hankali. Nuna girmamawa ga Manzon Allah bayan wafatinsa, kamar nuna masa girmamawa yana raye ne.” Mansur, yana sunkuyar da kansa, ya tambaya: “Ya Abu Abdullahi! In fuskanci alƙibla ne, ko kuwa in fuskanci Ƙabr-i Sa’adat?” Imam Malik ya ce: “Kada ka juya fuskarka daga Manzon Allah! Wannan Annabi maɗaukaki (sallallahu ta’ala alaihi wa sallam), mai ceton Ranar Ƙiyama, a Ranar Ƙiyama zai zama tsani domin kuɓutarka, kai da ubanka Adamu alaihis-salam. Ya kamata ka fuskanci Ƙabr-i Sa’adat, ka riƙe ruhin Manzon Allah mai albarka, ka nemi ceto! A aya mai girma ta sittin da huɗu ta Suratun Nisa’i an ce, a ma’ana:
“Da waɗanda suka zalunci kawunansu (suka cutar da kansu) sun zo maka, suka nemi gafara daga Allahu Ta’ala, kuma ManzoNa ma ya nema musu gafara, da sun sami Allahu Ta’ala Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai.” Wannan aya mai girma tana yin alkawarin cewa za a karɓi tubar waɗanda suka riƙi Manzon Allah tsani.” Sai Mansur ya tashi daga wurin da yake, ya tsaya a gaban Hujra-i Sa’adat, ya fara roƙo: “Ya Ubangijina! A cikin wannan aya mai girma Ka yi alkawarin karɓar tubar waɗanda suka riƙi ManzonKa tsani. Ni ma na zo gaban AnnabinKa maɗaukaki, ina neman gafara daga gare Ka. Kamar yadda Ka gafarta wa bayinKa da suka nemi gafara yana raye, Ka gafarta mini ni ma! Ya Ubangijina! Ina roƙonKa ina riƙon AnnabinKa maɗaukaki, Nabiyyur-Rahma (Annabin rahama), tsani. Ya Muhammadu alaihis-salam, mafi ɗaukakar annabawa! Ina tawassuli da kai, ina roƙon Ubangijina. Ya Ubangijina! Ka sanya wannan Annabi maɗaukaki mai ceto a gare ni!” Ya yi addu’a a tsaye, bayansa ga alƙibla, fuskarsa ta fuskanci tagar Muwajaha-i Sa’adat. Mimbarin Annabi yana gefensa na hagu. Nasihar da Imam Malik ya yi wa Halifa Mansur tana nuna cewa ya wajaba masu addu’a a gaban Hujra-i Sa’adat su kasance a farke ƙwarai. An ce bai dace waɗanda ba za su iya nuna ladabi da girmamawar da suka dace da wannan wuri ba su daɗe a Madina al-Munawwara ba. Wani manomi daga ƙauyukan Anatoliya ya zauna a Madina al-Munawwara shekaru da yawa, ya yi aure, ya shiga wata hidima a Hujra-i Sa’adat. Wata rana zazzaɓi ya kama shi, ransa ya yi marmarin shan nonon tsami (ayran). Ya wuce a zuciyarsa cewa: “Da a ce ina ƙauyena, da na sa a yi mini nonon tsami da kindirmo, in sha.” A wannan dare Manzon Allah ya bayyana ga Shaikhul-Haram a mafarki, ya ba da umarnin a ba wa wani hidimar wannan mutum. Da Shaikhul-Haram ya ce: “Ya Manzon Allah! Wane, daga cikin al’ummarka, ne yake yin wannan hidima”, sai ya ce: “Ka gaya wa wannan mutum! Ya tafi ƙauyensa, ya sha nonon tsami!..” Washegari, da aka sanar da wannan umarni, manomin ya ce: “To, na ji”, ya tafi ƙasarsa.
“Da waɗanda suka zalunci kawunansu sun zo maka, suka nemi gafara daga Allahu Ta’ala, kuma ManzoNa ma ya nema musu gafara, da sun sami Allahu Ta’ala Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai” Nisa’i: 64
Da yake tunani ɗaya kawai da ya wuce a zuciya ya yi irin wannan cutarwa, ya kamata a fahimta daga nan girman cutarwar – Allah Ya kiyaye – wata magana marar dacewa, ko da ta wasa ce, ko kuwa wani aiki da bai dace da ladabi ba.
Kai ne imani a zuciyar muminin da yake ƙaunarka,
Ba ya taɓa samun baƙin ciki: kai ne maganin ciwonsa,
Yana jiran cetonka; kai ne sarkin zuciyarsa,
Mai fatan agaji lalle zai samu, ya Rasulallah.
Muhimmanci da falalar yi wa Shugabanmu Manzon Allah salati mai daraja
Yi wa Shugabanmu Annabi salati mai daraja, a matsayin nuna girmamawa da ladabi, lokacin da aka faɗi sunansa, aka ji shi ko aka rubuta shi, yana daga cikin mafi muhimmancin ayyukanmu. A cikin Alƙur’ani mai girma, a aya mai girma ta hamsin da shida ta Suratul Ahzab, an ce, a ma’ana:
“Lalle Allahu Ta’ala da mala’ikunSa suna salati ga Annabi (domin ɗaukaka darajarsa da martabarsa). Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ma ku yi masa salati da sallama, ku sallama masa da zuciya ɗaya.”
Malaman tafsiri sun sanar da cewa kalmar “salati” da aka ambata a cikin wannan aya mai girma tana nufin rahama daga Allahu Ta’ala, istigfari daga mala’iku, addu’a kuma daga muminai. Dukkan malaman Musulunci sun sanar da baki ɗaya cewa yin salati sau ɗaya a rayuwa farilla ne. A duk lokacin da aka faɗa, aka ji, aka karanta, aka rubuta, yin salati sau ɗaya wajibi ne; idan an maimaita, mustahabbi ne.
Wanda yake roƙon wani abu daga Allahu Ta’ala, ya fara yin godiya da yabo ga Allahu Ta’ala, sannan ya yi wa Shugabanmu Manzon Allah salati. Irin wannan addu’a ta cancanci karɓa ƙwarai. Addu’ar da aka yi tsakanin salati biyu (a farkon addu’a da ƙarshenta) ba a mayar da ita. Sayyidina Abu Ɗalha yana ba da labari: “Na shiga gaban Manzon Allah. Na ga a tattare da shi wani farin ciki da jin daɗi da ban taɓa gani a baya ba. Da na tambayi dalili, ya ce: ’Yaya ba zan yi farin ciki ba? Ɗazu Jibrilu (alaihis-salam) ya kawo bushara: Allahu Ta’ala Ya ce: idan wani daga cikin al’ummarka ya yi maka salati ɗaya, Allahu Ta’ala, a sakamakonsa, Zai yi masa salati goma.’”6
Wasu daga cikin hadisai masu daraja a kan wannan al’amari su ne kamar haka:
“A goge hancin wanda aka ambaci sunana a wurinsa, bai kuma yi mini salati da sallama ba, a ƙasa. A goge hancin wanda watan Ramadan ya shiga, ya fita, ba a gafarta masa zunubansa ba, shi ma a ƙasa. A goge hancin wanda ya riski tsufan iyayensa, bai iya shiga Aljanna ta hanyar samun yardarsu ba, shi ma a ƙasa.”
“Wanda aka ambaci sunana a wurinsa, bai kuma yi mini salati da sallama ba, shi ne mafi rowar marowata.” Sayyidina Abu Humaid as-Sa’idi yana sanarwa: “Wasu daga cikin Sahabbai masu girma suka tambayi Shugabanmu Manzon Allah, suka ce: ‘Ya Manzon Allah! Yaya za mu yi maka salati da sallama?’ Shugabanmu Manzon Allah ya ce: ‘Ku ce: Allahumma salli ala Muhammadin wa azwajihi wa zurriyyatihi kama sallaita ala Ibrahima wa barik ala Muhammadin wa azwajihi wa zurriyyatihi kama barakta ala Ibrahima innaka Hamidun Majid.’”7
Wasu salati masu daraja su ne kamar haka:
“Alaihis-salam”.
“Sallallahu alaihi wa sallam”.
“Alaihis-salatu was-salamu wat-tahiyya”.
“Allahumma salli ala sayyidina Muhammad”.
“Allahumma salli ala Muhammadin wa ala alihi wa sahbihi ajma’in”.
“Alaihi wa ala jami’i minas-salawati atammuha wa minat-tahiyyati aimanuha”.
“Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahim…”
Wani mutum ya ba da labari kamar haka: Ɗaya daga cikin abokaina, a wata wasiƙa da ya aiko mini, ya rubuta a duk wurin da sunan Manzon Allah mai albarka ya zo “sallallahu alaihi wa sallam tasliman kasiran kasira”. Da na gani, na tambaye shi dalili, sai ya ce: “A ƙuruciyata na rubuta littattafan hadisi. Duk lokacin da na rubuta sunan Manzon Allah mai albarka, ba na rubuta salati. Na ga Shugaban Talikai a mafarki, na je wurinsa. Ya juya fuskarsa mai albarka daga gare ni. Na koma ɗaya gefensa; ya sake juyawa. Na tsaya a gabansa, na ce: ‘Ya Manzon Allah! Don me kake juya fuskarka daga gare ni?’ Ya ce: ‘Domin kai, a littafinka, lokacin da ka rubuta sunana, ba ka yi mini salati ba!’ Tun daga wannan lokaci, kullum ina rubuta sunansa mai daraja tare da salati.”
A cikin hadisai masu daraja an ce:
“Duk wanda ya yi mini salati sau ɗaya, Allahu Ta’ala Zai yi masa salati (rahama) sau goma, Ya gafarta masa zunubai goma, Ya ɗaga darajarsa sau goma.”
“A Ranar Ƙiyama wanda ya fi kusa da ni, wanda ya fi cancantar cetona, shi ne wanda ya fi yi mini salati da sallama.” Allah Maɗaukaki Ya ce wa Musa alaihis-salam: “Ya Musa, kana son In kasance kusa da harshenka fiye da maganarka, da zuciyarka fiye da tunaninka, da jikinka fiye da ranka, da idonka fiye da haskensa?” Da ya ce: “I, ya Ubangijina!”, Allahu Ta’ala Ya ce: “To, idan haka ne, ka yi wa Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallam) salati da yawa.” Sannan Ya ce: “Ya Musa, kana son kada ka sha ƙishirwa a Ranar Ƙiyama?” Da ya ce: “I, ya Ubangijina!”, Allahu Ta’ala Ya ce: “To, idan haka ne, ka yi wa Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallam) salati da yawa.”8
Shugabanmu Annabi ya ce:
“A Ranar Ƙiyama, a kowane matsayi, wanda ya fi kusa da ni a cikinku shi ne wanda ya fi yi mini salati a duniya. Wanda ya yi mini salati ɗari a ranar Juma’a da darenta, Allahu Ta’ala Zai biya masa buƙatu ɗari: saba’in na Lahira, talatin kuma na duniya. Sannan Allahu Ta’ala Yakan sa wani mala’ika ya kawo waɗannan salati kabarina. Suna zama kamar kyautar da take zuwa muku. Wannan mala’ika yakan sanar da ni sunan wanda ya aiko, asalinsa da ƙabilarsa. Yakan rubuta shi a wata farar takarda da take wurina. Sanina bayan mutuwa kamar sanina ne ina raye.”9
“Duk wanda ya yi mini salati sau ɗaya, Allahu Ta’ala Zai yi masa salati (rahama) sau goma, Ya gafarta masa zunubai goma, Ya ɗaga darajarsa sau goma” Hadisi mai daraja
“Idan ranar Alhamis ta zo, Allahu Ta’ala Yakan aiko da mala’iku waɗanda suke riƙe da littattafan azurfa da alƙaluman zinariya. Sukan rubuta waɗanda suke yawaita salati ga Annabi a ranar Alhamis da daren Juma’a.” “Idan Musulmi biyu suka haɗu suka yi musafaha (suka gaisa da hannu) suka kuma yi salati ga Annabi, kafin su rabu, ana gafarta musu zunubansu na baya da na gaba.” “Idan ɗayanku ya shiga masallaci, ya yi sallama ga Annabi, ya ce: ‘Ya Ubangijina! Ka kiyaye ni daga shaiɗan!’”10
A cikin wata riwaya: “Lokacin da yake fita daga masallaci, ya karanta: ‘Allahumma inni as’aluka min fadlika.’”
Idan a farkon addu’a babu yabo (hamdi) ga Allahu Ta’ala da salati ga Manzon Allah, addu’ar takan tsaya a bayan shamaki. Addu’ar da a farkonta akwai yabo da salati takan karɓu. Muddin ba a yi salati ga Manzon Allah da alayensa (Âl) ba, akwai shamaki a tsakanin addu’a da sama. Idan aka yi salati, sai wannan shamaki ya yage, addu’a ta hau sama. Idan ba a yi ba, addu’a takan dawo.
Idan a wani majalisi ba a ambaci Allahu Ta’ala ba, ba a kuma yi salati ga Manzon Allah ba, akwai bulala a kan waɗanda suke wurin: idan Ya so, Yakan azabtar da su; idan Ya so, Yakan gafarta musu.
“Wanda kunnensa ya yi ƙara, ya tuna da ni, ya yi mini salati.”
“Wanda ya yi niyyar wani aiki, ya yi shawara a kan haka. Allahu Ta’ala Zai ba shi shiriya (rushdi) a cikin aikinsa. Idan mutum ya so ya faɗi wata magana amma ya manta da ita, ya yi mini salati. Domin a cikin salatin da yake yi mini akwai abin da zai maye gurbin maganarsa. Ana fatan zai tuna da ita.”11
“Idan ba a fara aiki na alheri da sunan Allah da salati gare ni ba, babu alheri a cikin wannan aiki, kuma an cire dukkan albarkarsa.”12 Lokacin da Abu Hafs Kaghidi, ɗaya daga cikin manyan Musulunci, ya rasu, wani ya gan shi a mafarki, ya tambaye shi: “Yaya Allahu Ta’ala Ya yi da kai?” Ya ce: “Ya yi mini rahama, Ya gafarta mini, Ya kuma shigar da ni Aljanna.” Ya tambaya: “Saboda me?” Sai ya amsa da cewa: “An tsayar da ni a tsakanin mala’iku. Suka ƙidaya zunubaina da salatin da na yi wa Manzon Allah, suka sami salatina ya fi yawa. Sai Allahu Ta’ala Ya ce musu: ‘Ya mala’ikuNa! Aikinku ya ƙare. Kada ku ƙara yin wani hisabi. Ku kai shi AljannaTa!’”
Wani daga cikin magabata (salaf) ya ba da labari: “Wani abokina da muka yi karatun hadisi tare ya rasu. Na gan shi a mafarki yana sanye da koren tufafin Aljanna. Da na tambaye shi dalili, sai ya ce: ‘A cikin kowane hadisi, a gefen sunan Manzon Allah da na gani, nakan rubuta sallallahu alaihi wa sallam. Allah Maɗaukaki Ya ba ni ladan haka da wannan.’”
Har ila yau wani daga cikin magabata ya ba da labari: “Wani maƙwabcina marubuci ya rasu. Na gan shi a mafarki, na tambaye shi yadda Allahu Ta’ala Ya yi da shi. Ya ce Allahu Ta’ala Ya gafarta masa. Da na tambaya saboda me, sai ya ce: ‘Saboda duk lokacin da na rubuta sunan Manzon Allah, nakan rubuta kalmomin sallallahu alaihi wa sallam tare da shi.’” Abu Sulaiman Darani ya ba da labari: “Lokacin da nake rubuta hadisi, duk lokacin da na rubuta sunansa mai daraja, nakan rubuta sallallahu alaihi, amma ba na rubuta kalmomin wa sallam. Na gan shi a mafarki. Ya ce mini: ‘Ya Abu Sulaiman! Idan ka rubuta sunana a cikin hadisi, ka rubuta kalmomin wa sallam ma tare da salatin. Haruffa huɗu ne. Kowane harafi yana da lada goma. Idan ba ka rubuta ba, wato ka bar lada arba’in ke nan.’”
Wani mutum ma yana da irin wannan ɗabi’a. Manzon Allah ya ce masa a mafarki: “Me ya same ka da ba ka rubuta mini salati cikakke?”
Abubakar as-Siddiƙ ya ce: “Wanda yake tsoron mantuwa, ya yawaita salati ga Manzon Allah.”
Muhammadu ɗan Sa’id ɗan Muɗarrif, ɗaya daga cikin manyan salihai, ya ba da labari: “Kowane dare, lokacin da zan kwanta, nakan karanta salati a ƙayyadadden adadi. Wani dare na ga Manzon Allah a mafarki. Ya shigo wurina. Ɗakina ya cika da nuri. Sannan ya zo wajena ya ce: ‘Kawo wannan bakinka da yake yawaita yi mini salati, in sumbace shi.’ Ni kuwa, da kunya ta hana ni miƙa bakina, sai na miƙa kumatuna. Ya sumbace shi da bakinsa mai albarka. Na farka cikin farin ciki. Na sami ɗakina ya cika da ƙanshin miski. Har kwana takwas wannan ƙanshi mai daɗi bai gushe daga kumatuna ba.” Lokacin da Khallad ɗan Kasir, ɗaya daga cikin manyan magabata, ya rasu, an sami wata takarda a ƙarƙashin kansa, a rubuce: “Wannan ita ce takardar kuɓutar Khallad ɗan Kasir daga Wuta.” Sai aka tambayi danginsa: “Wane aiki yake yi?” Suka ce: “Yakan yi salati a kowace ranar Juma’a.” A cikin littafin Shaikh Aini mai suna Zainul-Majalis an rubuta cewa: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “A Ranar Ƙiyama, mutane gungu uku za su kasance a ƙarƙashin Al’arshi, inda babu wata inuwa sai inuwarsa.” Aka tambaya: “Su wane ne?” Ya ce: “Waɗanda suke kuɓutar da al’ummata daga wahala, waɗanda suke raya sunnata, da waɗanda suke yawaita salati gare ni.”
Shaikh Abu Musa Dariri ya ba da labari: “Guguwa ta kama mu a teku. Kowa yana kuka saboda tsoron mutuwa. A cikin wannan hali barci ya ɗauke ni. A mafarki na ga Manzo Mafi Daraja. Ya ce mini in gaya wa waɗanda suke cikin jirgin su karanta sau dubu: ‘Allahumma salli ala sayyidina Muhammadin wa ala ali sayyidina Muhammadin salatan tunjina biha min jami’il-ahwali wal-afat, wa taƙdi lana biha jami’al-hajat, wa tuɗahhiruna biha min jami’is-sayyi’at, wa tarfa’una biha indaka a’lad-darajat, wa tuballighuna biha aƙsal-ghayati min jami’il-khairati fil-hayati wa ba’dal-mamat.’ Da muka karanta har sau ɗari uku kawai, sai guguwar ta lafa, muka tsira.” An ba da shawarar karanta wannan salati a kowane muhimmin aiki, a kowace masifa, bala’i da girgizar ƙasa.
Dare da rana salati da sallama suna kan harshena, ga ruhunka mai albarka, ya Abin Alfaharin Halittu!
A cikin littattafai amintattu akwai hadisai fiye da arba’in a kan yadda ake yin salati.
Ɗaya daga cikinsu kuma kamar haka ne:
“Wanda kunnensa ya yi ƙara, ya tuna da ni, ya yi mini salati” Hadisi mai daraja
Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammad, kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahim, wa barik ala Muhammadin wa ala ali Muhammad, kama barakta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahim, innaka hamidun majid.
Allahumma salli wa sallim wa barik warham ala sayyidina Muhammadin huwa sayyidul-arabi wal-ajam.
Wa imamil-Makkatil-mukarramati wal-Madinatil-munawwarati wal-haram. Allamal-insana ma lam ya’lam.
Asluhu nurun wa nasluhu Adam.
Ba’suhu mu’akhkharun wa khalƙuhu muƙaddam.
Ismuhush-sharifu maktubun alal-Lauhil-mahfuzi biyaƙutil-ƙalam.
Wa jismuhush-sharifu madfunun fil-Madinatil-munawwarati wal-haram.
Ya laita aktahilu turaballazi tahtal-ƙadam.
Fa ɗuba summa ɗuba liman da’a wa tabi’ahu wa liman aslama sahibash-shafa’ati lil-alamin.
Ƙa’ilan ya Rabbi! Sallim ummati, ummati, wa ummata ya zal-luɗfi wal-karam.
Fa yunadil-munadi min ƙibalir-Rahman, ƙabiltu shafa’ataka ya Nabiyyal-muhtaram.
Udkhulul-jannata la khaufun alaikum wa la huznun wa la alam.
Summa radiyallahu ta’ala an Abi Bakrin wa Umara wa Usmana wa Aliyyin zil-karam.
Wa sallallahu ala sayyidina Muhammadin wal-hamdu laka ya Rabbal-alamin.
Bihurmati Sayyidil-mursalin.
Idan iskar safiya ta taɓa gashinsa mai albarka,
sai iska ta cika da ƙanshin miski da ambar.
Da hasken haƙoransa na lu’ulu’u, da dare
ko allura ta faɗi, da an same ta.
A cikin hasken ƙirjinsa mai nuri, a dararen duhu samari da tsofaffi suna tafiya a hanya.
Da wancan ƙaunataccen Allah ya yi nuni
da yatsansa ga wata, sai wata ya tsage biyu.
Idan ya yi gumi, kowane ɗigon guminsa yakan zama fure,
mutane suna tsinkar furanni daga guminsa cikin farin ciki.
Wancan sarkin duniya ya dasa itacen dabino,
a sa’ar da ya dasa shi, nan take ya ba da ƴaƴa.
Ko da an riƙa faɗin mu’ujizozinsa har Ranar Mahshar,
ko Mahshar nawa ya wuce, ba za su ƙare ba.
Idan kuna son ku tsira daga Wuta,
da ƙauna, da shauƙi, ku yi salati!
As-salatu was-salamu alaika ya Rasulallah!
As-salatu was-salamu alaika ya Habiballah!
As-salatu was-salamu alaika ya Nura Arshillah!
