WAFATIN SHUGABANMU ANNABI
Shekara ta goma sha ɗaya bayan Hijira ce. Lokacin da Jibrilu alaihis-salam ya zo a wannan shekara, ya karanta wa ƙaunataccen Annabinmu Alƙur’ani mai girma sau biyu daga farko har ƙarshe. Alhali a shekarun da suka gabata sau ɗaya kawai yake karanta Alƙur’ani mai girma. Bayan Jagoran Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) ya saurari Suratun Nasr, wadda ita ce ta ƙarshe da Jibrilu alaihis-salam ya isar, wadda ma’anarta: “Idan taimakon Allahu Ta’ala da ranar nasara suka zo, ka kuma ga mutane suna shiga addinin Allahu Ta’ala (Musulunci) jama’a-jama’a, ka yi tasbihi ga Ubangijinka tare da godiya! Ka nemi gafara daga gare Shi! Domin Shi koyaushe Yana karɓar tuba”1, ya ce: “Ya Jibrilu! Ina ji a cikina cewa mutuwata ta kusa.” A kan haka Jibrilu alaihis-salam ya karanta waɗannan ayoyi masu girma, a ma’ana: “Lahira ce mafi alheri a gare ka daga duniya. Ubangijinka Zai ba ka duk abin da kake so, har ka ce: ‘Na yarda.’”2
A shekara ta goma sha ɗaya bayan Hijira, a ranar ashirin da bakwai ga watan Safar, kan Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) mai albarka ya fara ciwo. Ya tafi ɗakin matarsa mai girma Nana A’isha (radiyallahu anha). Ya sa aka kira Abdurrahman ɗan Abubakar, ya sanar da shi cewa zai sa a rubuta wasiyya domin a zaɓi Abubakar as-Siddiƙ halifa a bayansa, ya umarce shi ya kawo tawada da alƙalami. Yayin da Abdurrahman, ɗan Sayyidina Abubakar, yake tafiya domin ya aiwatar da umarninsa, sai ya ce masa: “Za ka kawo daga baya, yanzu a bari!”, sannan ya tafi masallaci mai daraja. Ƙaunataccen Annabinmu ya aika da saƙo ga dukkan Sahabbai masu girma da suke Madina a wannan rana su taru a masallaci a sallar azahar. Bayan ya yi limancin sallar, Jagoran Talikai ya hau mimbari, ya yi huɗuba. Ya yi wa Sahabbansa nasiha, ya nemi su yafe masa. Sannan ya bayyana fifikon Abubakar as-Siddiƙ a cikin Sahabbai, darajarsa, da kuma yadda yake matuƙar yarda da shi. Huɗuba ce irin wadda dukkan zukatan da suka ji ta suka yi rawar jiki, hawaye suka zuba daga idanu. Bayan haka, da ya ce: “Ya ku mutane! Yaya kuka same ni a matsayin Annabinku?”, Sahabbai masu girma suka ce: “Ya Manzon Allah! Allahu Ta’ala Ya saka maka da alheri mai yawa a madadinmu. Ka kasance a gare mu kamar uba mai tausayi ƙwarai, kamar ɗan’uwa mai tausayi mai yin nasiha. Ka cika aikin annabta da Allahu Ta’ala Ya yi maka falalarsa. Ka isar mana da abin da aka yi maka wahayi. Ka yi kira, ka gayyata zuwa tafarkin Ubangijinka, zuwa Musulunci, da hikima da kyakkyawar nasiha. Allahu Ta’ala Ya ba ka sakamako mafi kyau da mafi ɗaukaka.”
Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya ku muminai! Saboda Allah, duk wanda yake da wani haƙƙi a kaina, ya tashi ya zo ya karɓa a nan, kafin Ƙiyama.”
Amma babu wanda ya tashi ya zo domin ya karɓi haƙƙinsa. Shugabanmu Manzon Allah, yana ambaton sunan Allahu Ta’ala, ya ce a karo na biyu da na uku: “Mai haƙƙi ya zo ya karɓa.” A kan haka Sayyidina Ukkasha, tsoho dattijo daga cikin Sahabbai masu girma, ya tashi. Ya zo gaban Manzon Allah. Sannan ya ce: “Uwata da ubana su zama fansa a gare ka, ya Manzon Allah! A yaƙin Tabuk ina tare da kai. A lokacin da muke barin Tabuk, raƙumina da naka sun zo gefe da gefe. Na sauka daga raƙumina. Na kusance ka. Manufata ita ce in sumbaci jikinka mai albarka; a lokacin ne ka buge ni a bayana da bulala. Ban san don me ka buge ni ba.”
“Lahira ce mafi alheri a gare ka daga duniya. Ubangijinka Zai ba ka duk abin da kake so, har ka ce: ‘Na yarda’” Duha: 4–5
Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya Ukkasha! Allahu Ta’ala Ya kiyaye a ce ManzonSa ya buge ka da gangan”, ya kuma umarta: “Ya Bilalu! Tafi gidan ƴata Fatima. Kawo mini wannan bulala.” Sayyidina Bilalu ya fita daga masallaci. Ya sa hannu a kansa, yana cikin mamaki: “Manzon Allah zai sa a yi masa ƙisasi!” Da ya isa gidan, ya ƙwanƙwasa ƙofa, ya ce: “Ya ƴar Manzon Allah! Ba ni bulalar Manzon Allah!” Uwarmu Nana Fatima ta tambaya: “Ya Bilalu! Yanzu ba lokacin hajji ba ne, ba kuma na yaƙi ba! Me babana zai yi da bulala?” Sayyidina Bilalu ya ce: “Ya Fatima! Ba ki ji ba ne? Za a yi wa Manzon Allah ƙisasi da ita!”
Uwarmu Nana Fatima ta yi wa Sayyidina Bilalu gargaɗi mai tsanani: “Ya Bilalu! Wa zuciyarsa za ta yarda ya karɓi haƙƙinsa daga Manzon Allah da ƙisasi? Tun da ya nema, zan bayar. Amma ka faɗa wa Hasan da Husaini: duk wanda zai karɓi haƙƙinsa, su sa a yi ƙisasin a kansu. Bari wannan mutum ya karɓi haƙƙinsa daga gare su. Kada ko kaɗan su bar a yi wa Manzon Allah ƙisasi.” Sayyidina Bilalu ya zo masallaci, ya ba Shugabanmu Manzon Allah bulalar, shi kuma ya ba Sayyidina Ukkasha. Da Sayyidina Abubakar da Sayyidina Umar suka ga wannan hali, suka roƙa: “Ya Ukkasha! Ga mu nan a shirye a gabanka, ka karɓi haƙƙinka daga gare mu. Muna roƙonka, kada ka karɓa daga Manzon Allah!” A kan haka Shugabanmu Annabi ya ce wa Sayyidina Abubakar: “Ya Abubakar! Kai ka bari, ka ja gefe. Ya Umar! Kai ma ka ja gefe. Allahu Ta’ala Ya san darajarku maɗaukakiya.” Sannan Sayyidina Aliyu ya tashi, ya ce: “Ya Ukkasha! Zuciyata ba ta yarda ka bugi Manzon Allah ba. Ga bayana da cikina, zo ka karɓi haƙƙinka daga gare ni, in ka so ka buge ni sau ɗari. Amma kada ka taɓa Manzon Allah!” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya Aliyu! Kai ma ka zauna. Allahu Ta’ala Ya san matsayinka maɗaukaki da halinka ma.” A wannan karo Sayyidina Hasan da Husaini suka tashi, suka ce: “Ya Ukkasha! Kai ma ka sani cewa mu jikokin Manzon Allah ne. Saboda haka ƙisasi a kanmu, ƙisasi ne a kan Manzon Allah. Ka karɓi haƙƙinka daga gare mu, muna roƙonka, kada ka bugi Manzon Allah!” Shugabanmu Annabi ya ce musu: “Ku ma ku zauna, ya farin cikin idanuna biyu.” Sannan ya ce: “Ya Ukkasha! Zo ka buga!”
Ukkasha ya ce: “Ya Manzon Allah! Lokacin da ka buge ni, jikina a buɗe yake.” Sai ƙaunataccen Annabinmu ya buɗe bayansa mai albarka. A wannan lokaci aka ji shassheƙa daga Sahabbai masu girma, suna cewa: “Ya Ukkasha! Za ka bugi bayan Manzon Allah mai albarka ne?” Kowa yana jira cikin baƙin ciki. Da Sayyidina Ukkasha ya ga hatimin annabta a bayan Shugabanmu Manzon Allah mai albarka, farat ɗaya ya ce: “Uwata da ubana su zama fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Wa zai iya samun ƙarfin halin bugun wannan bayanka mai albarka, ya yi maka ƙisasi domin ya karɓi haƙƙinsa?”, sai ya sumbaci hatimin annabta mai albarka na Sarkin Halittu. A kan haka Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce masa: “A’a; ko dai ka buga, ko kuma ka yafe.” Sayyidina Ukkasha ya ce: “Raina ya zama fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Na yafe. Shin Allahu Ta’ala ma Zai yafe mini a Ranar Ƙiyama?” Shugabanmu Annabi ya ce: “Wanda yake son ya ga abokina a Aljanna, ya kalli wannan tsoho dattijo.” Sahabbai masu girma da suka ji wannan magana mai albarka ta Shugabanmu Manzon Allah suka fara sumbatarsa a tsakanin idanunsa biyu. Dukkansu suna cewa: “Albishirinka, albishirinka! Ya Ukkasha! Saboda darajar kasancewa tare da Manzon Allah, ka sami daraja maɗaukaka a Aljanna.”3
Naɗa Usama ɗan Zaid kwamanda
Kwanakin ƙarshe na watan Safar ne. Shugaban Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) yana son, kafin Daular Rum ta arewa ta zama babban haɗari ga Musulmi, ya sake gayyatar Rumawa zuwa Musulunci, idan ba su yarda ba kuma ya yaƙe su, ya shigar da su ƙarƙashin umarnin Daular Musulunci. Saboda haka ya umarci Sahabbansa jarumai su shirya domin yaƙi da Rumawa. Sahabbai masu girma suka watse domin su yi shiri. Manzo Mafi Daraja ya sa aka kira Sayyidina Usama ɗan Zaid, ya ce: “Ya Usama! Tafi da sunan Allahu Ta’ala da albarkarSa har zuwa Sham, har iyakar Balƙa, har Darum da yake Falasɗinu, wurin da aka yi wa ubanka shahada. Ka sa dawakai su tattaka waɗannan wurare. Na naɗa ka babban kwamandan wannan runduna. Ka far wa mutanen Ubna ba zato ba tsammani, ka kai musu hari kamar walƙiya. Ka yi tafiya da sauri ta yadda labari ba zai isa wurin da za ka je kafin ka isa ba. Ka ɗauki masu nuna hanya tare da kai, ka sa ƴan leƙen asiri da masu tsaro su yi gaba. Idan Allahu Ta’ala Ya ba da nasara, ka zauna a tsakaninsu kaɗan.” Ya umarce su su kafa sansani a Jurf, ya ɗaure tuta da hannuwansa masu albarka, ya miƙa masa.4
Ya hau mimbari a masallaci, ya ce: “Ya Sahabbaina! Kamar yadda Zaid, uban Usama, ya cancanci kwamandanci, kuma ya kasance mafi soyuwa a wurina, haka nan, bayansa, ɗansa Usama ma ya cancanci kwamandanci. Usama yana cikin mafi soyuwar mutane a wurina.”
A cikin waɗanda za su tafi yaƙi ƙarƙashin jagorancin Sayyidina Usama akwai manyan Sahabbai ma, kamar Sayyidina Abubakar, Sayyidina Umar, Sayyidina Abu Ubaida ɗan Jarrah da Sayyidina Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas.
Amma saboda washegari Sarkin Halittu ya kamu da rashin lafiya farat ɗaya, tafiyar rundunar ta jinkirta har bayan Shugabanmu Annabi ya koma Lahira. Ƙaunataccen Annabinmu ya kamu da ciwon zazzaɓi (humma) mai tsanani. Zazzaɓinsa yana ƙara ƙaruwa, ciwon yana ƙara tsananta.
Wani dare da ciwonsa ya ragu, da tsakar dare, ya tashi daga shimfiɗarsa. Ya sa tufafi, ya shirya tafiya. Da uwarmu Nana A’isha ta ga haka, ta tambaya: “Uwata da ubana da raina su zama fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Ina za ka?” Jagoran Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “An umarce ni in nemi gafara (istigfari) ga waɗanda aka binne a maƙabartar Baƙi’. Can zan je.”
Ya ɗauki Abu Muwaihib da Abu Rafi’ tare da shi, ya tafi. A maƙabartar ya yi addu’a mai tsawo, ya roƙi Allahu Ta’ala afuwa da gafara a gare su. Da ganin wannan roƙo mai naci na Shugabanmu Annabi, Sahabban da suke tare da shi suka ce: “Da mu ma yanzu a nan aka binne mu, da mun sami darajar samun wannan addu’a ta Shugabanmu Manzon Allah!” Ƙaunataccen Annabinmu ya juya ga Abu Muwaihib, ya ce: “Ya Abu Muwaihib! An ba ni ƴancin zaɓi tsakanin taskokin duniya da ni’imomin Lahira. Aka ce mini: ’In ka so, ka zauna a duniya, sannan ka tafi Aljanna; in ka so kuma, Liƙa’ullah (haɗuwa da Allahu Ta’ala) ya samu, ka shiga Aljanna.’ Ni na zaɓi Liƙa’ullah, sannan Aljanna.”
“Ya ku muminai! Saboda Allah, duk wanda yake da wani haƙƙi a kaina, ya tashi ya zo ya karɓa a nan, kafin Ƙiyama” Hadisi mai daraja
Wata rana kuma ya fita domin ya nemi gafara ga shahidan da suke a Uhud. Ya yi musu addu’a, yana roƙon Allahu Ta’ala na dogon lokaci. Sannan ya zo masallaci, ya ce wa Sahabbai masu girma: “Ni ne zan fara isa ga tafkin Kausar a cikinku, ni ne zan tarbe ku. Wurin haɗuwarmu da ku a can ne… Ni ba na tsoro a kanku cewa bayana za ku koma ga shirka. Sai dai ina tsoron ku ruɗu da duniya, saboda ita ku yi wa juna hassada, ku kashe juna. A ƙarshe ina tsoron ku ɓace ku tafi, kamar yadda waɗanda suke kafinku suka ɓace suka tafi…” Sannan ya albarkaci gidansa mai albarka da zuwansa. Ciwonsa ya tsananta. Matansa masu albarka suka sanar wa ƙaunataccen Annabinmu cewa suna son ya zauna a gidan uwarmu Nana A’isha, sun kuma bar mata haƙƙoƙinsu. Ya yi farin ciki da wannan sadaukarwa ta matansa tsarkaka, ya yi wa dukkansu addu’a, ya fara yin kwanakinsa na bayan haka a gidan uwarmu Nana A’isha. Zazzaɓin Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya ƙaru ƙwarai. Saboda tsananin zazzaɓin, sai ya kasance yana ta juyi daga wannan gefe zuwa wancan a shimfiɗarsa. Yana cikin wannan hali, Sahabbai masu girma suna zuwa ziyara, suna matuƙar baƙin ciki da tsananin wahalar da Shugabanmu yake sha. Abu Sa’id Khudri ya ba da labari: “Na tafi gaban Manzon Allah mai albarka. A kansa akwai wani mayafi na karammiski. Zafin zazzaɓin yana fita ta mayafin, saboda zafin ba mu iya taɓa mayafin da hannunmu ba. Shugabanmu Manzon Allah, da ya ga mamakinmu da baƙin cikinmu, ya ce:
‘Mafi tsananin bala’i yakan sami annabawa. Duk da haka, farin cikin annabi da bala’o’i ya fi farin cikinku da ni’imomin da ake ba ku.’”
Ummu Bishr ƴar Bara’ ta ba da labari: “Na tafi ziyarar Manzon Allah. Jikinsa mai albarka yana ƙuna kamar wuta. Na ce: ‘Raina ya zama fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Ban taɓa ganin ciwo mai tsanani irin wannan ba!…’ Ya ce: ‘Ya Ummu Bishr! Tsananin zazzaɓin domin ladana ya yi yawa ne. Wannan ciwo sakamakon naman da aka sa wa guba ne da na ɗanɗana a Khaibar. Kullum ina jin raɗaɗin wannan nama. Gubar da na ci a wannan rana yanzu tana yanke abharina, wato babbar jijiyar jinina.’”5
Ƙaunataccen Annabinmu ya kuma ce wa Sayyidina Abdullahi ɗan Mas’ud: “Babu wani Musulmi da ciwo ya kama shi, face Allahu Ta’ala Ya zubar da kurakuransa da zunubansa, kamar yadda ganyen itace yake zubewa!”6 Ciwon yana ƙara tsananta kowace rana. Sahabbai masu girma suna matuƙar baƙin ciki da wannan hali, ba sa iya samun nutsuwa a gidajensu. Suka taru a masallaci. Suka aika Sayyidina Aliyu gaban Shugabanmu Annabi domin ya tambayi halinsa. Shugaban Talikai ya tambaya da ishara: “Me Sahabbaina suke cewa?” Shi kuma ya ce: “Suna matuƙar baƙin ciki da damuwa, suna cewa: ‘Idan Manzon Allah ya tafi daga cikinmu!…’” Ƙaunataccen Annabinmu, wanda tausayinsa ga Sahabbansa ya fi nasu yawa nesa ba kusa ba, ya jure wa tsananin ciwonsa, ya tashi, ya zo masallaci yana jingina ga Sayyidina Aliyu da Sayyidina Fadl ɗan Abbas. Ya hau mimbari, bayan ya yi godiya da yabo ga Allahu Ta’ala, ya ce wa Sahabbai masu girma:
“Ya Sahabbaina! Na ji kuna tunanin mutuwata, kuna fargaba. Shin akwai wani annabi da ya dawwama har abada a cikin al’ummarsa, har ni ma in dawwama a cikinku har abada? Ku sani, zan haɗu da Ubangijina. Nasihata a gare ku ita ce: ku girmama manyan Muhajirun! Ya ku Muhajirun! Wasiyyata a gare ku kuma ita ce: ku kyautata wa Ansar! Su sun kyautata muku. Sun ba ku masauki a gidajensu. Duk da cewa rayuwarsu tana cikin ƙunci, sun fifita ku a kan kansu. Sun sanya ku abokan tarayya a dukiyoyinsu. Duk wanda ya zama mai mulki a kan Ansar, ya kula da su; idan akwai waɗanda suka yi kuskure a cikinsu, ya yafe musu.” Sannan ya yi musu nasihohi kyawawa masu ratsa zuciya, ya ce: “Allahu Ta’ala Ya bar wani bawanSa da zaɓi a tsakanin zama a duniya da haɗuwa da Ubangijinsa. Wannan bawa kuwa ya zaɓi haɗuwa da Ubangijinsa.” Sayyidina Abubakar ya fahimci cewa da waɗannan kalmomi Shugabanmu Manzon Allah yana nuni ne ga wafatinsa, sai ya fara kuka, yana cewa: “Rayukanmu su zama fansarka, ya Manzon Allah!” Tekun rahama, ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam), ya ce masa: “Kada ka yi kuka, ya Abubakar!”, ya umarce shi da yin haƙuri da jurewa. Hawaye suna zuba daga idanunsa masu albarka. Ya ce: “Ya Sahabbaina! Na yarda ƙwarai da Abubakar, wanda ya sadaukar da dukiyarsa a tafarkin addinin Musulunci da gaskiya da ikhlasi. Da a ce ana iya riƙon aboki don tafiyar Lahira, da shi na zaɓa.” Sannan ya ba da umarni: “Ku rufe dukkan ƙofofin da suke buɗewa zuwa masallaci, ban da ta Abubakar!”
Daga nan ya sauko daga mimbari, ya koma ɗakin uwarmu Nana A’isha. Sahabbai masu girma suka fara kuka. Sai Shugabanmu Annabi, yana jingine a hannuwan Sayyidina Aliyu da Fadl ɗan Abbas, ya sake zuwa masallaci. Ya tsaya a kan matakin ƙasa na mimbari, ya ce wa Sahabbai masu girma: “Ya ku Muhajirun da Ansar! Gaggawa don isa ga abin da lokacinsa ya ƙayyadu ba ta da amfani. Allahu Ta’ala ba Ya gaggawa saboda wani bawa. Duk wanda ya yi ƙoƙarin sauya ƙaddara da hukuncin Allahu Ta’ala (ƙada da ƙadara), ya nemi ya ɗaukaka kansa a kan nufinSa, Allah Zai ƙasƙantar da shi, Ya halaka shi.
Wanda ya so ya yi wa Allahu Ta’ala makirci, ya yaudare Shi, al’amuransa za su ɓaci, shi kansa kuma zai yaudaru. Ku sani, ni mai tausayi ne, mai jin ƙai a gare ku. Ku ma za ku haɗu da ni. Wurin da za ku haɗu da ni shi ne bakin tafkin Kausar. Duk mai son shiga Aljanna, ya haɗu da ni, kada ya yi maganar banza. Ya ku Musulmi! Zama kafiri da aikata zunubi suna zama sanadin sauyawar ni’ima da raguwar arziki. Idan mutane suka yi ɗa’a ga umarnin Allahu Ta’ala, shugabannin gwamnati, hakimai da gwamnoni sukan nuna musu rahama da tausayi. Idan kuwa suka shiga fasiƙanci da fajirci da ƙetare iyaka, suka aikata zunubai, ba za su sami shugabanni masu rahama ba. Kamar yadda rayuwata ta kasance alheri a gare ku, mutuwata ma alheri ce da rahama. Idan na taɓa dukan wani ba da haƙƙi ba, ko na faɗa masa mummunar magana, na yarda ya yi mini irin haka ya ɗauki haƙƙinsa; idan na karɓi wani abu daga wurin ɗayanku ba da haƙƙi ba, na yarda ya nemi a mayar masa, kuma a shirye nake in nemi yafiya. Domin azabar duniya tana da sauƙi ƙwarai a kan azabar Lahira. Jure wa wannan ya fi sauƙi.” Kamar yadda a baya ya bayyana yardarsa da Sayyidina Abubakar, a wannan huɗuba ma ya bayyana yardarsa da Sayyidina Umar, ya ce: “Umar yana tare da ni, ni ma ina tare da shi. Bayana, gaskiya tana tare da Umar.”
“Mafi tsananin bala’i yakan sami annabawa. Duk da haka, farin cikin annabi da bala’o’i ya fi farin cikinku da ni’imomin da ake ba ku” Hadisi mai daraja
Bayan wannan huɗuba Shugabanmu Manzon Allah ya sauko daga mimbari. Bayan salla ya sake hawa mimbari, ya yi wasiyya da nasiha, sannan ya ce: “Na danƙa ku ga Allahu Ta’ala”, ya rabu da Sahabbansa, ya koma ɗakinsa. Wata rana da zafin cutarsa ya yi tsanani, Shugaban Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) ya sa aka kira Sayyidina Bilalu Habashi, domin ya nemi yafiya daga Sahabbai masu girma, kada ya tafi Lahira da haƙƙin bayi a kansa. Ya ce masa: “Ka kira mutane! Su taru a masallaci. Ina son in yi musu wasiyyata ta ƙarshe!…”
Sayyidina Bilalu ya tara Sahabbai a masallaci. Ƙaunataccen Annabinmu ya zo masallaci yana jingine a kan Sayyidina Aliyu da Fadl. Ya zauna a kan mimbari, bayan ya yi godiya da yabo ga Allahu Ta’ala, ya ce: “Ya Sahabbaina! Ku sani cewa rabuwata da ku ta kusa. Duk wanda yake da wani haƙƙi a kaina, ya nema daga gare ni. Wanda nake ƙauna, ya nemi haƙƙinsa daga gare ni, ko kuma ya yafe mini, domin in haɗu da Ubangijina da rahamarSa ina mai biyan waɗannan haƙƙoƙi.” Sannan ya sauko daga mimbari, ya jagoranci sallar azahar. Bayan salla ya sake hawa mimbari, ya maimaita abin da ya faɗa kafin salla. A lokacin rashin lafiyarsa, duk lokacin da aka yi kiran salla, Shugabanmu Annabi yakan fito zuwa Masallaci mai daraja, ya zama limamin Sahabbai masu girma, ya yi salla a jam’i.7 Sauran kwana uku ga wafatin ƙaunataccen Annabinmu, rashin lafiyarsa ta tsananta. Bai iya fitowa masallaci ya jagoranci sallar jam’i ba. Sallar farko da bai iya yi a jam’i ba, ita ce sallar isha’i.
Sayyidina Bilalu, kamar kullum, ya zo bakin ƙofa a wannan lokaci, ya ce: “As-salat, ya Rasulallah!” Saboda rauni, ƙaunataccen Annabinmu ba shi da ƙarfin zuwa masallaci. Ya ce: “Ku gaya wa Abubakar! Ya jagoranci Sahabbaina salla.” Uwarmu Nana A’isha ta ce: “Raina ya zama fansarka, ya Manzon Allah! Babana mai taushin zuciya ne, kuma mai saurin tausayawa. Idan ya tsaya a matsayinka, bai gan ka a wurin ba, ba zai iya karatu ba saboda kuka. Ba za ka umarci Umar ya tsaya a limanci ba?” Shugabanmu Annabi ya sake cewa: “Ku gaya wa Abubakar! Ya zama limamin Sahabbaina, ya jagorance su salla.” Sayyidina Bilalu ya sanar da Abubakar as-Siddiƙ wannan al’amari. Da Sayyidina Abubakar bai ga Shugabanmu Manzon Allah a mihirabi ba, sai ya zama kamar wanda aka soki zuciyarsa, hankalinsa ya kusa tashi. Ya yi kuka!… ya yi kuka!… Sahabbai masu girma ma suka fara kuka. Da Habibullah ya tambayi ko mene ne wannan kuka da yake zuwa daga masallaci, sai uwarmu Nana Fatima ta bayyana masa al’amarin: “Raina ya zama fansarka, ya Manzon Allah! Sahabbanka suna kuka ne saboda ba su iya jure wa rabuwa da kai!…”8 Tekun rahama, ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam), ya shiga damuwa ƙwarai. Domin ya sanyaya wa Sahabbansa zuciya, duk da tsananin rashin lafiyarsa, ya tashi da ƙyar. Ya zo masallaci yana jingine a kan Sayyidina Aliyu da Sayyidina Abbas. Bayan salla ya ce: “Ya Sahabbaina! Kuna cikin kiyayewar Allahu Ta’ala, kuma na danƙa ku amana ga Allahu Ta’ala! Ku kasance a kan taƙawa. Ku ji tsoron Allahu Ta’ala. Ku riƙe umarnin Allahu Ta’ala, ku yi ɗa’a. Ni dai, yanzu zan rabu da wannan duniya.”
Sauran kwana uku ga wafatin ƙaunataccen Annabinmu. Jibrilu alaihis-salam ya zo ziyarar Shugabanmu Manzon Allah, ya ce: “Ya Rasulallah! Allahu Ta’ala Yana gaishe ka. Duk da cewa Ya san halinka, Yana tambayar yadda kake, da yadda kake jin kanka.” Shugaban Talikai kuwa ya ce: “Ina cikin baƙin ciki!” Jibrilu alaihis-salam ya sake zuwa ranar Lahadi, ya faɗi irin waɗannan kalmomi. Shugabanmu Annabi ya sake ba da amsar da ya bayar a baya. Jibrilu alaihis-salam kuma ya ba da labarin cewa an kashe Aswad al-Ansi, wanda ya yi da’awar annabta a Yaman. Manzo Mafi Daraja ya sanar da Sahabbansa. Kafin rashin lafiyarsa, an kawo masa ƴan zinariya kaɗan; ya ba talakawa wasu daga cikinsu, wasu kuma ya ba Nana A’isha. Ranar Lahadi, rashin lafiyar Manzon Allah ta tsananta. Kwamandan runduna, Sayyidina Usama, da ya zo wurinsa, bai ce masa komai ba. Amma ya ɗaga hannuwansa masu albarka, ya shafa a kansa. Aka fahimci cewa yana yi masa addu’a. Rana ta goma sha uku ta rashin lafiyarsa, ita ce ta ƙarshe… Wannan rana, kamar ranar da ƙaunataccen Annabinmu ya albarkaci duniya da zuwansa, ita ce ranar goma sha biyu ga watan Rabi’ul-Awwal, ranar Litinin. Sarkin Halittu ya ji ɗan sauƙi a jikinsa mai albarka… Lokacin da Sahabbai masu girma suke gab da yin sallar asuba a bayan Sayyidina Abubakar as-Siddiƙ, Shugaban Talikai ya zo Masallaci mai daraja. Ya ga al’ummarsa a jere sahu-sahu suna ibada. Ya yi murmushi cikin farin ciki. Sahabbai masu girma ma, da suka ga Manzon Allah a masallaci, suka yi farin ciki, suna tsammanin cutar ta wuce. Abubakar as-Siddiƙ (radiyallahu anhu), da ya fahimci cewa ƙaunataccen Annabinmu ya zo, ya so ya ja da baya. Shugabanmu ya yi masa alama mai ma’anar “Tsaya a wurinka!” Shi kansa ya bi Sayyidina Abubakar, ya yi salla a bayansa.9 Ta haka, da umarnin Manzon Allah, Sayyidina Abubakar ya jagoranci Sahabbai masu girma salla sau goma sha bakwai. Bayan salla Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya koma ɗakin Nana A’isha, ya kwanta. Ya ce: “Ina son in tafi gaban Allahu Ta’ala ba tare da na bar dukiyar duniya ba. Zinariyar da ta rage a wurinki ma, ki rarraba wa talakawa!” Sannan zazzaɓinsa ya ƙaru. Bayan ɗan lokaci ya sake buɗe idanunsa, ya tambayi Nana A’isha ko ta rarraba zinariyar. Ta ce za ta rarraba. Sai ya ba da umarni a rarraba su nan take. Da aka rarraba su nan take, aka sanar da shi, sai ya ce: “Yanzu na huta.” Bayan ya ɗan huta a kan shimfiɗarsa, ya kira Sayyidina Aliyu zuwa wurinsa. Ya sanya kansa mai albarka a cinyarsa. Goshinsa mai albarka ya yi zufa, launinsa mai albarka ya sauya. Uwarmu Nana Fatima, da ta ga ubanta mai albarka a wannan hali, ba ta iya jure kallo ba, sai ta tafi wurin ƴaƴanta Sayyidina Hasan da Sayyidina Husaini. Ta kama hannuwansu, ta fara kuka: “Ya babana! Wa zai kula da ƴarka? Ga wa za ka danƙa Hasan da Husaini amana? Kaico, babana! Raina ya zama fansarka! Bayanka, me zai zama halina? Bayan fuskarka mai albarka, ga wa idanuna za su kalla?” Da Shugabanmu Manzon Allah ya ji waɗannan kalmomin ƴarsa masu ƙona zukata, ya buɗe idanunsa masu albarka, ya kira ta zuwa wurinsa, ya yi addu’a: “Ya Ubangijina! Ka ba ta haƙuri.” Sannan da ya ce: “Ya Fatima! Ya nurin idona! Babanki yana cikin halin fitar rai!”, sai kukanta da nishi mai ratsa zuciya ya ƙaru. Da Sayyidina Aliyu ya ce: “Ya Fatima! Don Allah ki yi shiru, kada ki ƙara wa Manzon Allah baƙin ciki!”, sai ƙaunataccen Annabinmu ya ce: “Kada ka ɓata mata rai, ya Aliyu! Bari idanunta su zubar da hawaye saboda ubanta!…” Sannan ya rufe idanunsa masu albarka, ya zama kamar wanda ya suma. Daga nan Sayyidina Hasan ya zo gaban kakansa mai albarka, ya ce yana kuka: “Ya kakana mai albarka! Wa zai iya jure wa rabuwa da kai? Ga wa za mu kai ƙorafin ɓacin zukatanmu? Bayanka, wa zai tausaya wa mahaifiyata, mahaifina da ɗan’uwana? Matanka da Sahabbanka, a ina za su sami waɗannan kyawawan ɗabi’unka?..” Sai matan Shugabanmu Annabi masu albarka suka kasa jurewa, dukkansu tare suka fara kuka a hankali, ba tare da ɗaga murya ba. Sahabbai masu girma, waɗanda suke jira a waje cikin tsananin damuwa, da suka ji cewa rashin lafiyar Shugabanmu Annabi ta ƙaru ƙwarai, zukatansu suka ƙone. Suka fara kuka. Domin su ga fuskar ƙaunataccen Annabinsu mai albarka, ko da sau ɗaya ne na ƙarshe, suka riƙa roƙo a bakin ƙofa: “Don Allah, ku buɗe ƙofa! Mu sake ganin fuskar Manzo alaihis-salam mai albarka sau ɗaya kuma!..” Habibin Allahu Ta’ala, masoyinSa, wanda aka aiko rahama ga talikai, da ya ji waɗannan roƙe-roƙen Sahabbansa, ya ji tausayinsu, ya ce: “Ku buɗe ƙofa!” Manyan Sahabbai suka shiga ciki. Ƙaunataccen Annabinmu, bayan ya yi musu wasiyya da haƙuri, ya ce: “Ya Sahabbaina! Ku ne mafi ɗaukakar mutane, mafi darajarsu. Duk wanda ya zo bayanku, ku ne za ku riga su duka shiga Aljanna. Ku tsaya tsayin daka wajen riƙe addini, ku riƙi Alƙur’ani mai girma a matsayin limami (jagora).
“Ya Sahabbaina! Kuna cikin kiyayewar Allahu Ta’ala, kuma na danƙa ku amana ga Allahu Ta’ala! Ku kasance a kan taƙawa” Hadisi mai daraja
Kada ku yi gafala daga hukunce-hukuncen addini.” Sannan ya ce: “Ya Ubangijina! Shin na isar da saƙo?”, ya rufe idanunsa masu albarka. Fuskarsa mai albarka ta yi zufa. Sayyidina Aliyu ya yi wa Sahabbai alama su fita. Bayan sun tafi, uwarmu Nana A’isha ta zo wurinsa, ta nemi nasiha. Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya A’isha! Ki zauna a kusurwar gidanki, ki kiyaye kanki!” Bayan haka hawaye suka fara zuba daga idanunsa masu albarka. Sarkin Halittu yana kuka… Zukatan waɗanda suke wurin suka ji rauni, hanjinsu suka yayyage. Da uwarmu Nana Ummu Salama ta tambaya: “Raina ya zama fansarka, ya Manzon Allah! Don me kake kuka?”, ya ce: “Ina kuka ne domin a yi wa al’ummata rahama.”
Rana tana hawa zuwa tsakiyar sama. Lokaci ya kusa… Kan ƙaunataccen Annabinmu mai albarka yana jingine a ƙirjin uwarmu Nana A’isha. Shugaban Talikai yanzu yana cikin lokutansa na ƙarshe, kuma waɗannan kalmomi suna zuba daga leɓunansa masu albarka: “Ku kiyaye! Ku kiyaye! Ku kyautata wa bayin da suke a hannuwanku! Ku yi musu sutura, ku ƙosar da cikinsu. Ku yi musu magana a hankali. Salla, salla – ku dawwama a kanta. Ku ji tsoron Allahu Ta’ala game da matanku da bayinku!.. Ya Allah! Ka gafarta mini! Ka ba ni rahamarKa!… Ka haɗa ni da jama’ar Rafiƙ-i A’la!…” Hawayen uwarmu Nana Fatima suna zuba kamar rigyawa, nishinta kuma yana ƙona hanji. Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya zaunar da ita kusa da shi, ya ce: “Ƴata, ki ɗan yi haƙuri, kada ki yi kuka. Domin Hamalatul-Arsh (mala’iku) suna kuka saboda kukanki.” Ya share hawayen uwarmu Nana Fatima. Ya sanyaya mata zuciya, ya roƙi Allahu Ta’ala Ya ba ta haƙuri, ya ce: “Ya ƴata, za a karɓi raina. Ki ce: ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un’. Ya Fatima! Kowace masifa da ta zo, akwai sakamakonta.” Bayan ya rufe idanunsa masu albarka na ɗan lokaci, ya ce: “Daga yanzu babu sauran baƙin ciki da damuwa ga babanki. Domin yana kuɓuta ne daga duniya mai ƙarewa da wurin wahala.” Sannan ya ce wa Sayyidina Aliyu: “Ya Aliyu! Akwai dukiyar wane Bayahude kaza da kaza a kaina. Na karɓa ne domin shirya runduna. Kada ka manta da biyansa. Lalle za ka ƙwato ni daga wannan bashi, kuma kai ne na farkon waɗanda za su haɗu da ni a bakin tafkin Kausar. Bayana, cutarwa mai yawa za ta same ka; ka yi haƙuri. Lokacin da mutane suka nemi duniya, kai ka zaɓi Lahira.”
Usama ya sake zuwa. Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Allahu Ta’ala Ya zama mataimakinka! Yi gaba, ka tafi yaƙi!” Shi ma ya fita, ya tafi wurin rundunarsa, ya ba da umarnin tashi nan take.10
Shugaban Talikai yanzu yana numfashinsa na ƙarshe… Lokaci ya matso ƙwarai… Allahu Ta’ala Ya yi wahayi ga Azra’ilu alaihis-salam: “Ka je wurin HabibiNa a mafi kyawun sura! Idan ya ba da izini, ka karɓi ransa a hankali ƙwarai, cikin sauƙi. Idan bai ba da izini ba, ka koma!” Azra’ilu alaihis-salam, a mafi kyawun sura, a kamannin mutum, ya zo bakin ƙofar gidan ƙaunataccen Annabinmu mai albarka, ya ce: “Assalamu alaikum, ya mai gidan annabta! Za ka ba ni izinin shiga? Allahu Ta’ala Ya yi maka rahama!”
Uwarmu Nana A’isha ta ce wa Nana Fatima, wadda take zaune kusa da ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam): “Ke ki ba wa wannan mai zuwa amsa.” Nana Fatima ta je bakin ƙofa, ta ce da murya mai cike da baƙin ciki: “Ya bawan Allahu Ta’ala! Manzon Allah a yanzu yana shagaltuwa da halin da yake ciki.” Azra’ilu alaihis-salam ya sake neman izini. Aka ba shi irin wannan amsa. Da ya maimaita sallamarsa a karo na uku, ya faɗa da babbar murya cewa dole ne ya shiga, sai Shugabanmu Annabi ya ji, ya ce: “Ya Fatima! Wane ne a bakin ƙofa?”
Nana Fatima ta ce: “Ya Manzon Allah! Wani a bakin ƙofa yana neman izinin shiga. Na ba shi amsa sau da yawa. Amma da ya yi kira a karo na uku, jikina ya yi tsima.” Sai Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ya Fatima! Kin san wane ne a bakin ƙofa? Shi ne mai rusa daɗaɗa, mai watsa taruka, mai barin mata zawarawa, yara marayu, mai lalata gidaje, mai cika kaburbura: mala’ikan mutuwa, Azra’ilu. Ya Azra’ilu, shigo!” A lokacin uwarmu Nana Fatima ta faɗa cikin wani baƙin ciki da ba a iya siffantawa, kuma waɗannan kalmomi suka fito daga bakinta mai albarka: “Kaico, Madina, kin lalace!” Annabinmu ya kama hannun Nana Fatima, ya sanya shi a ƙirjinsa mai albarka, ya rufe idanunsa masu albarka. Waɗanda suke wurin suka yi tsammanin an karɓi ransa mai albarka. Uwarmu Nana Fatima ba ta iya jurewa ba, ta sunkuya zuwa kunnen ubanta mai albarka, ta yi kira da murya mai raunata zukata: “Ya babana!…” Da ba a sami amsa ba, a wannan karo ta ce: “Raina ya zama fansarka, ya Manzon Allah! Don Allah ka buɗe idanunka masu albarka sau ɗaya, ka faɗa mini wani abu…” Shugaban Talikai ya buɗe idanunsa masu albarka, ya share hawayen ƴarsa, ya faɗa mata a kunne cewa zai yi wafati. Sai Nana Fatima ta fara kuka. A wannan karo ya faɗa mata a kunne: “Daga cikin Ahlul-Baitina, ke ce za ki fara zuwa wurina.” Ita kuma ta yi farin ciki da wannan bushara, ta sami sanyin zuciya.
“Ya Allah! Ka gafarta mini! Ka ba ni rahamarKa!… Ka haɗa ni da jama’ar Rafiƙ-i A’la!…” Hadisi mai daraja
Uwarmu Nana Fatima ta tambaya: “Ya babana! Yau ranar rabuwa ce! Yaushe zan sake haɗuwa da kai?” Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ya ƴata! Za ki same ni a Ranar Ƙiyama a gefen tafki (haudi). Zan shayar da waɗanda suka zo tafkin daga cikin al’ummata.” Da Nana Fatima ta tambaya: “Idan ban same ka a can ba, me zan yi?”, Shugabanmu Annabi ya ce: “Za ki same ni a wurin Mizani. A can zan yi wa al’ummata ceto.”
Da uwarmu Nana Fatima ta ce: “Idan a can ma ban same ka ba, ya Manzon Allah?”, Shugabanmu Annabi ya ce: “Za ki same ni a wurin Siraɗi. A can zan roƙi Ubangijina: ‘Ya Ubangijina! Ka kiyaye al’ummata daga wuta!’”
Bayan haka Sayyidina Aliyu ya tambaya da murya mai baƙin ciki: “Ya Manzon Allah! Bayan ka miƙa ranka, wa zai yi maka wanka, da me za mu yi maka likkafani, wa zai jagoranci sallar jana’izarka, wa zai sa ka a kabari?” Shugabanmu Annabi ya ce:
“Ya Aliyu, kai ka yi mini wanka, Fadl ɗan Abbas ya riƙa zuba maka ruwa. Jibrilu zai zama na ukunku. Idan kuka gama wanka (ghusl), ku yi mini likkafani. Jibrilu zai kawo turare mai ƙanshi daga Aljanna. Sannan ku kai ni masallaci, ku fita. Domin da farko Jibrilu, sannan Mika’ilu, sannan Isra’filu, sannan mala’iku rukuni-rukuni za su yi mini salla. Bayan haka ku shigo, ku yi sahu-sahu. Kada kowa ya shige gabana.”11 Sannan ya tambayi Azra’ilu alaihis-salam, wanda yake jira: “Ya Azra’ilu! Ziyara ka zo yi ne, ko kuwa karɓar raina?..”, sai Azra’ilu alaihis-salam ya ce: “Na zo a matsayin baƙo, kuma a matsayin mai aiki. Allahu Ta’ala Ya umarce ni da kada in shiga gabanka sai da izini. Ba zan karɓi ranka mai albarka ba sai da izininka. Ya Manzon Allah! Idan ka ba da izini, zan bi umarninka, in karɓi ranka. In ba haka ba, zan koma, in tafi wurin Ubangijina.” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya Azra’ilu! A ina ka bar Jibrilu?..” Azra’ilu ya ce: “Na bar Jibrilu a saman duniya. Mala’iku suna yi masa ta’aziyya saboda wafatinka.” Suna cikin wannan magana, sai Jibrilu alaihis-salam ya zo. Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ya ɗan’uwana Jibrilu! Lokacin ƙaura daga duniya ya yi. Me nake da shi a wurin Allahu Ta’ala? Ka yi mini busharar hakan, domin in miƙa amana ga mai ita da kwanciyar hankali.” Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya masoyin Allahu Ta’ala! Na bar ƙofar sama a buɗe. Mala’iku sun yi sahu-sahu, suna jiran ranka da ƙauna.” Shugabanmu Annabi ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allahu Ta’ala. Kai ka yi mini bushara! Me nake da shi a wurin Ubangijina?..” Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Manzon Allah! Saboda zuwanka, ƙofofin Aljanna sun buɗe, kogunan Aljanna sun gudana, itatuwan Aljanna sun sunkuya, huruliyai sun yi ado.”
Shugabanmu Annabi ya sake cewa: “Godiya ta tabbata ga Allahu Ta’ala. Ka yi mini wata bushara, ya Jibrilu!..” Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Manzon Allah! A Ranar Ƙiyama kai ne mai ceto na farko, kuma na farkon wanda za a karɓi cetonsa.” Da ƙaunataccen Annabinmu ya sake cewa: “Godiya ta tabbata ga Allahu Ta’ala. Ya Jibrilu! Ka yi mini wata bushara”, Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Manzon Allah! Game da me kake tambaya?..” Sai Shugabanmu Annabi ya ce: “Dukkan damuwata, baƙin cikina da ɓacin raina, game da al’ummata ce da zan bari a bayana.” Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Habibin Allahu Ta’ala! A Ranar Ƙiyama Allahu Ta’ala Zai gafarta wa al’ummarka har sai ka yarda. Zai shigar da kai Aljanna kafin dukkan annabawa, al’ummarka kuma kafin dukkan al’ummomi.” Ƙaunataccen Annabinmu ya ce wa Jibrilu alaihis-salam: “Ina da buƙatu uku a wurin Allahu Ta’ala: na farko, Ya sanya ni mai ceto ga masu zunubi na al’ummata. Na biyu, kada Ya azabtar da su saboda zunuban da suka aikata a duniya. Na uku, a riƙa nuna mini ayyukan al’ummata a ranakun Alhamis da Litinin. (Idan ayyukansu nagari ne, zan yi addu’a, Allahu Ta’ala Ya karɓa. Idan munana ne, zan yi ceto, in roƙi a goge su daga littafin ayyuka.)” Jibrilu alaihis-salam ya kawo labari daga Allahu Ta’ala cewa an karɓi waɗannan buƙatunsa ukun duka. Sai ƙaunataccen Annabinmu ya huta.
Allahu Ta’ala Ya yi wahayi: “Ya HabibiNa! Wane ne ya sanya wannan ƙauna da tausayi ga al’ummarka a cikin zuciyarka mai albarka?..” Shugabanmu Annabi ya amsa: “Ubangijina Maɗaukaki, wanda Ya halicce ni, Ya tarbiyyantar da ni.” Allah Maɗaukakin Sarki kuma Ya ce: “RahamaTa da jin ƙaiNa ga al’ummarka sun fi naka sau dubu. Ka bar su gare Ni.” Sai ƙaunataccen Annabinmu ya ce: “Yanzu na huta. Ya Azra’ilu! Ka cika aikin da aka umarce ka da shi!” Azra’ilu alaihis-salam, domin ya cika aikinsa, ya kusanci gaban Sarkin Halittu, wanda saboda darajarsa aka halicce shi kansa. Ƙaunataccen Annabinmu ya tsoma hannuwansa biyu masu albarka a cikin kwaryar ruwa da take kusa da shi, ya shafa fuskarsa mai albarka da hannuwansa jiƙaƙƙu, ya ce: “La ilaha illallah! Ya Allah! Rafiƙ-i A’la!…” Azra’ilu alaihis-salam ya fara karɓar ran Shugaban Talikai mai albarka. Fuskar Shugabanmu Manzon Allah mai albarka wani lokaci tana yin ja, wani lokaci kuma tana yin fari. Da ya ce wa Azra’ilu alaihis-salam: “Ran al’ummata ma haka za ka karɓa, da tsanani da ƙarfi?..”, sai Azra’ilu ya amsa: “Ya Manzon Allah! Ban taɓa karɓar ran kowa cikin sauƙi irin haka ba.” Ƙaunataccen Annabinmu, wanda ko a lokacinsa na ƙarshe bai manta da al’ummarsa ba, ya ce: “Ya Azra’ilu! Tsananin da za ka yi wa al’ummata, ka yi mini shi! Domin su raunana ne, ba za su iya jurewa ba…” Sannan ya ce: “La ilaha illallah! Rafiƙ-i A’la!..”, aka karɓi ransa mai albarka, aka isar da shi zuwa A’la-yi Illiyyin…
Shafa’a, ya Rasulallah!
Dakhilak, ya Rasulallah!
As-salatu was-salamu alaika ya Rasulallah!
As-salatu was-salamu alaika ya Habiballah!
As-salatu was-salamu alaika ya Sayyidal-awwalina wal-akhirin!
Jibrilu alaihis-salam ya yi wa Shugabanmu Annabi bankwana da cewa: “Assalamu alaikum, ya Manzon Allahu Ta’ala! Kai ne nufina, kai ne abin nemana. Daga yanzu ba zan ƙara zuwa doron ƙasa ba!..”
Da ran Manzo Mafi Daraja mai albarka ya tafi zuwa ga duniya maɗaukakiya, uwarmu Nana Fatima da matansa tsarkaka (azwaj-i ɗahirat) (radiyallahu anhunna) suka fara kuka a hankali, ba tare da ɗaga murya ba.12 A wannan lokaci wata murya, da ba a ga mai ita ba, ta ce:
“Ya Fatima! Kin san wane ne a bakin ƙofa? Shi ne mai rusa daɗaɗa, mai watsa taruka, mai barin mata zawarawa, yara marayu, mai lalata gidaje, mai cika kaburbura: mala’ikan mutuwa, Azra’ilu” Hadisi mai daraja
“Assalamu alaikum, ya Ahlal-Baiti! Wa rahmatullahi wa barakatuhu”, kuma ta karanta aya mai girma ta ɗari da tamanin da biyar ta Suratu Ali Imrana, wadda ma’anarta: “Ku sani, kowane mai rai zai ɗanɗani mutuwa. Kuma a Ranar Ƙiyama za a cika muku sakamakonku.” Sannan ta sanyaya musu zuciya, ta yi ta’aziyya da cewa: “Ku dogara ga falalar Allahu Ta’ala da karamcinSa. Ku riƙe Shi, ku yi fata a gare Shi. Kada ku yi kururuwa! Wanda masifa ta same shi da gaske, shi ne wanda ya rasa lada!”
Dukkan waɗanda suke wurin suka ji waɗannan kalmomi, suka amsa sallamarsa. Mai faɗar su kuwa Khidir alaihis-salam ne.13 Da aka ga alamomin mutuwa a jikin Manzo Mafi Daraja, Ummu Aiman ta aika labari ga ɗanta Usama. Usama, Sayyidina Umar da Abu Ubaida, da suka sami wannan labari mai ɗaci, suka bar runduna, suka zo Masallacin Annabi. Da A’isha as-Siddiƙa da sauran mata suka yi kuka, Sahabbai masu girma da suke cikin Masallaci mai daraja suka ruɗe. Ba su fahimci abin da ya faru ba. Suka zama kamar waɗanda aka bugi kawunansu. Sayyidina Aliyu ya tsaya cik kamar matacce. Sayyidina Usman harshensa ya kame. Sayyidina Abubakar a lokacin yana gidansa. Ya zo a guje. Ya shiga Hujra-i Sa’adat nan take. Ya buɗe fuskar Abin Alfaharin Talikai, ya ga cewa ya yi wafati. Fuskarsa mai albarka da dukkan jikinsa, cikin laushi da tsarki, suna haskakawa kamar nuri. Ya sumbace shi, yana cewa: “Mutuwarka ma, kamar rayuwarka, ina kyanta, ya Manzon Allah!” Ya yi kuka mai yawa. Ya rufe fuskarsa mai albarka. Ya sanyaya wa mutanen gida zuciya. Sannan ya zo Masallaci mai daraja. Ya hau mimbari, ya yi wa Sahabbai masu girma huɗuba. Ya yi godiya da yabo ga Allahu Ta’ala, bayan ya yi salati ga Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam), ya ce: “Duk wanda ya yi imani da Muhammadu alaihis-salam, ya sani cewa Muhammadu alaihis-salam ya yi wafati. Duk wanda yake bauta wa Allahu Ta’ala kuwa, ya sani cewa Shi Hayyu ne (Rayayye) kuma Baƙi ne (ba Ya mutuwa, Madawwami ne).” Sannan ya karanta aya mai girma ta ɗari da arba’in da huɗu ta Suratu Ali Imrana, wadda ma’anarta: “Muhammadu (alaihis-salam) manzo ne. Kafin shi ma manzanni sun zo. Shi ma zai mutu. Idan ya yi wafati ko aka kashe shi, za ku juya baya daga addininku ne? Wanda ya fita daga addininsa, ba zai cutar da Allahu Ta’ala ba. Kansa yake cutarwa. Waɗanda ba su juya baya daga addininsu ba kuwa, Allahu Ta’ala Zai ba su lada.” Ya yi wa Sahabbai masu girma nasiha, ya daidaita al’amura.14 Ta haka dukkansu suka tabbata cewa Manzon Allah ya yi wafati. Baƙin ciki da ɓacin rai suka soki zukatan Sahabbai masu girma kamar wuƙa mai guba. Idanu suna kuka, hawaye suna gudana kamar kogi, wutar kewa tana ƙona hanjin kowa. Sahabbai masu girma (alaihimur-ridwan), a matsayin aiki na farko, suka zaɓi Sayyidina Abubakar halifa, domin ya gudanar da dukkan al’amura. Suka yi masa mubaya’a (bai’a), suka bi shi, suka fara gudanar da al’amura bisa umarninsa.15 Manzo Mafi Daraja ya koma Lahira a shekara ta goma sha ɗaya bayan Hijira (632 Miladiyya), a ranar 12 ga watan Rabi’ul-Awwal, ranar Litinin, kafin azahar. A lokacin yana da shekara 63 bisa kalandar wata (61 bisa kalandar rana).16
Sayyidina Aliyu, Sayyidina Abbas, Sayyidina Fadl ɗan Abbas da Sayyidina Usama ɗan Zaid suka yi wa Shugabanmu Annabi wanka.17
“Ku dogara ga falalar Allahu Ta’ala da karamcinSa. Ku riƙe Shi, ku yi fata a gare Shi. Kada ku yi kururuwa! Wanda masifa ta same shi da gaske, shi ne wanda ya rasa lada!” Khidir alaihis-salam
Mihrab-i Sharif – Rauda-i Mutahhara / Masallacin Annabi
Sashen Masallaci mai daraja na Shugabanmu Annabi (alaihis-salatu was-salam) da ake kira “Rauda-i Mutahhara / Lambun Aljanna”. Ana ganin mihirabin da ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya jagoranci salla a cikinsa a matsayin limami. Ko da yake ba a ganinsa a wannan hoto, a gefen hagu kabarinsa mai albarka (Hujra-i Sa’adat) yake.
Mimbar-i Sharif – Rauda-i Mutahhara / Masallacin Annabi
Ana ganin mimbarin da ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi huɗubar Juma’a a kansa. Mimbari mai daraja na wancan lokaci yana da mataki uku, tsawonsa mita ɗaya. Ya ƙone gaba ɗaya a gobarar shekara ta 654 (1256 Miladiyya). A shekaru daban-daban an yi mimbarai daban-daban; mimbarin marmara na yau, mai mataki goma sha biyu da tsawon mita bakwai, Sultan Murad Khan na Uku ne ya aiko da shi daga Istanbul a shekara ta 998 bayan Hijira (1590 Miladiyya).
A lokacin wanka, wani ƙanshi irin na miski ya bazu daga jikinsa mai albarka, wanda babu wanda ya taɓa jin irinsa har zuwa wannan lokaci. Sannan, ba tare da an cire masa rigarsa mai albarka ba, aka yi masa wanka sau uku, aka naɗe shi a cikin sabon likkafani fari mai kashi uku. Aka ɗauke shi a kan wani gado, aka kawo shi masallaci. Kamar yadda ƙaunataccen Annabinmu ya sanar a baya, kowa ya fita daga masallaci. Mala’iku suka riƙa zuwa rukuni-rukuni, suka yi masa sallar jana’iza. Da mala’iku suka gama salla, sai wata murya, da ba a ga mai ita ba, ta ce: “Ku shigo! Ku yi wa Annabinku sallar jana’iza!” Sai Sahabbai masu girma suka shiga ciki. Su ma suka riƙa zuwa rukuni-rukuni, suka yi wa ƙaunataccen Annabinmu sallar jana’iza ba tare da limami ba. Sai da yammacin ranar Laraba suka iya kammalawa. Game da haƙa kabarin ƙaunataccen Annabinmu mai albarka, Sahabbai masu girma suka bi wannan hadisi mai daraja da Sayyidina Abubakar ya tunatar da su: “Annabawa, a wurin da suka miƙa rayukansu ake binne su.” An binne Shugabanmu Annabi a kabari mai albarka da Sayyidina Abu Ɗalha al-Ansari ya haƙa a siffar lahadi, wajen tsakiyar daren da ya haɗa Talata da Laraba (daren Laraba). Ƙusam, ɗan Sayyidina Abbas, shi ne ya kammala aiki a cikin kabari, ya fito na ƙarshe. Ya ce: “Ni ne na ƙarshe da ya ga fuskar Manzon Allah mai albarka. Leɓunansa masu albarka suna motsi. Na sunkuya a kansa, na kasa kunne. Yana roƙo: ‘Ya Ubangijina! Al’ummata!… Ya Ubangijina! Al’ummata!..’”18 A ranar da ƙaunataccen Annabinmu ya koma Lahira, Sayyidina Abdullahi ɗan Zaid ya yi addu’a: “Ya Ubangijina! Ni ina son wannan ido ne domin in kalli fuskar HabibinKa mai albarka, mai nuri. Da ya zama ba a ganinsa, to me zan yi da shi! Ya Ubangijina, Ka karɓi idona!”, sai ya makance…
A wafatin Shugabanmu Manzon Allah, gwaggonsa mai daraja Safiyya ƴar Abdulmuɗɗalib (radiyallahu anha) ta faɗi wannan waƙar makoki:
Ya Manzon Allah! Kai ne fatanmu,
Kai ne wanda kullum yake kyautata mana.
Ba ka taɓa kasancewa daga masu zalunci ba,
Kai, daga masu tausayi ne da masu shiryarwa.
Kai kuma tekun ilimi ne da ba a iya siffantawa.
Yau kukan masu kuka, saboda kai ne.
Dukkan kakannina su zama fansa a tafarkinka!
Dukiyata, raina, dukkan abin da nake da shi, fansa su zama.
Kaico! Da a ce a yau kana nan a raye a tsakaninmu,
Da ka zauna, da mun yi farin ciki ƙwarai.
Hukuncin Allah Maɗaukaki ke nan, muna cewa “Haƙuri!”,
Ban san me za mu yi ba, kullum kuka muke yi.
Amincin Allah ya tabbata a gare ka, ya Manzon Allah!
Ka shiga Aljannar Adnin, ka zauna a ciki, ya Manzon Allah!
