HUƊUBAR BANKWANA
Godiya ta tabbata ga Allahu Ta’ala. Muna gode maSa, muna neman gafara daga gare Shi, muna tuba gare Shi. Muna neman tsari ga Allahu Ta’ala daga sharrin zukatanmu da zunuban ayyukanmu. Wanda Allahu Ta’ala Ya shiryar zuwa tafarki madaidaici, babu mai ɓatar da shi; wanda kuma Ya ɓatar, babu mai shiryar da shi zuwa tafarki madaidaici. Ina shaida cewa babu abin bautawa sai Allahu Ta’ala. Shi Ɗaya ne. Ba Shi da kini, ba Shi da abokin tarayya. Ina kuma shaida cewa Muhammadu (alaihis-salam) bawanSa ne kuma manzonSa.
Ya bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ku ji tsoron Allahu Ta’ala, ku yi maSa ɗa’a.
Ya ku mutane! Ku saurari maganata da kyau! Ban sani ba, watakila bayan wannan shekara ba zan ƙara haɗuwa da ku a nan ba har abada. Ya ku mutane! Kamar yadda waɗannan kwanakinku kwanaki ne masu tsarki, kamar yadda wannan watanku wata ne mai tsarki, kamar yadda wannan birninku (Makka) birni ne mai albarka, haka nan rayukanku, dukiyoyinku da mutuncinku masu tsarki ne. An kiyaye su daga kowane irin keta.
Sahabbaina! Gobe za ku haɗu da Ubangijinku, lalle kuma za a tambaye ku a kan kowane hali da aikinku na yau. Kada fa, bayana, ku koma ga ɓatar baya, ku riƙa sare wa juna wuya!
Waɗanda suke nan su isar da wannan wasiyya tawa ga waɗanda ba sa nan!
Mai yiwuwa ne wanda aka isar wa ya fi wanda ya ji a nan fahimtarta da kiyaye ta. Sahabbaina! Wanda yake da wata amana a wurinsa, ya mayar da ita ga mai ita!
An soke kowane irin riba. Tana ƙarƙashin ƙafata. Amma dole ne ku mayar da asalin bashinku. Kada ku yi zalunci, kada kuma a zalunce ku. Da umarnin Allahu Ta’ala, cin riba yanzu haram ne. Kowace irin wannan mummunar al’ada da ta rage daga Jahiliyya tana ƙarƙashin ƙafata. Ribar farko da na soke ita ce ribar Abbas, ɗan Abdulmuɗɗalib (baffana). Sahabbaina! Ramuwar jini da ake yi a zamanin Jahiliyya ma an soke ta gaba ɗaya. Ramuwar jini ta farko da na soke ita ce ramuwar jinin Rabi’a, jikan Abdulmuɗɗalib (ɗan baffana).
Ya ku mutane! Canza wuraren watanni masu alfarma domin a iya yin yaƙi, babu shakka, zurfafa ƙwarai ne a cikin kafirci. Abu ne da kafirai suke ɓacewa da shi. A wata shekara sukan ɗauki (wani wata) halal, a shekara ta gaba kuma su ayyana shi haram. Suna yin haka ne domin su daidaita da adadin watannin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya halatta da Ya haramta. Suna halatta abin da Allahu Ta’ala Ya haramta, suna haramta abin da Ya halatta.
Ya Sahabbaina! Muna yin hajji daidai a lokacinsa. Tsarin watanni kamar yadda yake a lokacin da Allahu Ta’ala Ya halicce su. Babu shakka ko kaɗan, zamani ya koma ga sura da tsarin da yake da su a ranar da Allahu Ta’ala Ya halicce shi.
“Ya Allah! Ka ƙara wa wannan Ɗaki daraja, ɗaukaka, kwarjini da martaba. Waɗanda suke girmama shi da hajji da umra ma, Ka ƙara musu daraja, kwarjini, girmamawa da alheri” Hadisi mai daraja
Ya ku mutane! A yau shaiɗan ya rasa ikon sake kafa tasirinsa da mulkinsa a wannan ƙasa taku har abada. Amma idan kuka bi shi, a wajen waɗannan abubuwa da na soke, a ayyukan da kuke ganinsu ƙanana, wannan zai faranta masa rai. Domin ku kiyaye addininku, ku kiyayi waɗannan ma!
Ya ku mutane! Ina yi muku wasiyya da ku kiyaye haƙƙoƙin mata, a wannan al’amari kuma ku ji tsoron Allahu Ta’ala. Kun ɗauki mata a matsayin amanar Allahu Ta’ala; kun halatta wa kanku mutuncinsu da kamun kansu da ba da alkawari da sunan Allahu Ta’ala. Kuna da haƙƙi a kan mata; su ma suna da haƙƙoƙi a kanku. Haƙƙinku a kan mata shi ne kada su bar wanda ba ku so ya keta sirrin iyalanku. Idan suka shigar da wani da ba ku yarda da shi ba a gidan iyalanku, kuna iya dukansu a hankali domin ku gargaɗe su. Haƙƙoƙin mata a kanku kuma su ne ku samar musu da kowane irin abinci da tufafi ta hanyar halal. Ya ku muminai! Ina bar muku wata amana, wadda matuƙar kun riƙe ta ƙam, ba za ku taɓa ɓata hanyarku ba. Wannan amana ita ce Littafin Allahu Ta’ala, Alƙur’ani mai girma. (A wasu riwayoyi an kuma sanar da: “Sunnata” da “Ahlul-Baitina”.)
Ya ku muminai! Ku saurari maganata da kyau, ku kiyaye ta da kyau! Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, ta haka kuma dukkan Musulmi ƴan’uwa ne. Keta wani haƙƙi da yake na ɗan’uwanku na addini ba halal ba ne ga wani, sai dai idan shi da kansa ya ba da shi da yardar rai. Sahabbaina! Kada ku zalunci kanku (rayukanku). Ku kanku ma kuna da haƙƙi a kanku. Ya ku mutane! Allahu Ta’ala Ya ba kowane mai haƙƙi haƙƙinsa (a cikin Alƙur’ani mai girma). Babu buƙatar wasiyya ga magaji. Yaro na wanda aka haife shi a shimfiɗarsa ne. Ga mai zina akwai hanawa. Marar asali wanda ya yi da’awar nasaba ga wanin ubansa, ko kuma butulu wanda ya yi ƙoƙarin danganta kansa ga wanin ubangidansa, fushin Allahu Ta’ala da la’anar mala’iku da ta dukkan Musulmi su sauka a kansa! Allah Maɗaukakin Sarki ba Ya karɓar tubar irin waɗannan mutane, ba Ya kuma karɓar shaidarsu. Ya ku mutane! Ubangijinku Ɗaya ne. Ubanku ma ɗaya ne; dukkanku ƴaƴan Adamu ne. Adamu kuwa daga ƙasa yake. Mafi darajarku a wurin Allah shi ne wanda ya fi taƙawa a cikinku. Balarabe ba shi da wani fifiko a kan wanda ba Balarabe ba. Fifiko sai da taƙawa kaɗai. Idan aka naɗa muku wani baƙin bawa gurgu shugaba a kanku, ya kuma mulke ku da Littafin Allah, ku saurare shi, ku yi masa ɗa’a. Ba a zargin mai laifi da wani laifi in ba nasa ba. Ba a zargin uba a kan laifin ɗansa, ba a kuma zargin ɗa a kan laifin ubansa.
Ya ku mutane! Ku saurara! Waɗannan abubuwa huɗu kada ku aikata su ko kaɗan:
1. Kada ku haɗa Allah da kowane abu.
2. Kada ku kashe ran da Allah Ya haramta ba da haƙƙi ba.
3. Kada ku yi zina.
4. Kada ku yi sata.
An umarce ni da in yi jihadi da mutane har su ce “La ilaha illallah, Muhammadun Rasulullah” (wato har su zama Musulmi). Idan sun faɗi haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu. Hisabinsu kuma na Allahu Ta’ala ne. Ya ku mutane! Gobe za a tambaye ku game da ni, me za ku ce?… Sahabbai masu girma suka ce: “Muna shaida cewa ka isar da addinin Allahu Ta’ala. Ka cika aikinka. Ka yi mana wasiyya da nasiha.” A kan haka Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya ɗaga ɗan yatsansa na shaida mai albarka, ya sauko da shi zuwa ga jama’a, ya ce: “Ka shaida, ya Ubangiji! Ka shaida, ya Ubangiji! Ka shaida, ya Ubangiji!”
A ranar da ƙaunataccen Annabinmu ya yi Huɗubar Bankwana, aya ta 3 mai girma ta Suratul Ma’ida ta sauka, wadda ma’anarta: “A yau Na kammala muku addininku. Na cika ni’imaTa a kanku, Na kuma yarda da ba ku Musulunci ya zama addini…” Da Shugabanmu Annabi ya karanta wa Sahabbai masu girma wannan aya mai girma, Sayyidina Abubakar ya fara kuka. Da Sahabbai masu girma suka tambayi dalilin kukansa, ya ce: “Wannan aya mai girma tana nuna cewa wafatin Manzon Allah ya kusa. Saboda haka nake kuka.”1
Bayan huɗubar, suka yi tsayuwa (wuƙufi) a Jabalur-Rahma. Shugabanmu bai yi sallar magariba a Arafa ba; ya yi limancinta a Muzdalifa tare da sallar isha’i. A wannan dare suka kwana a Muzdalifa. Washegari da safe suka yi tsayuwa a Mash’arul-Haram. A ranar farko ta Babbar Sallah suka tashi daga Muzdalifa zuwa Mina. A hanya, a kwarin da ake kira Muhassir, wurin da Rundunar Giwa (Ashabul-Fil)2 ta tsaya, ba su tsaya ba, suka wuce. Suka iso Mina; a nan Shugabanmu da kansa ya yanka 63 daga cikin raƙuman yanka, ya ba Sayyidina Aliyu wuƙar. Sauran Sayyidina Aliyu ya yanka. A rana ta biyu, ta uku da ta huɗu ta Babbar Sallah suka yi jifan jamarori, a rana ta goma sha huɗu ga watan Zulhijja kuma, kafin sallar asuba, suka zo Ɗakin Allah, suka yi ɗawafin bankwana. Shugabanmu Manzon Allah ya zauna a Makka kwana 10, ya yi Hajjin Bankwana da ɗawafin bankwana, ya koma Madina. Ya yi salla raka’a biyu a Masallacin Annabi, ya albarkaci gidansa mai albarka da zuwansa. Bayan Hajjin Bankwana Sahabbai masu girma suka tafi wuraren da suka zo daga gare su, a can kuma suka ba da labarin abubuwan da Manzon Allah ya sanar, ya kuma umarta.
Sauran al’amura da suka faru a shekara ta goma bayan Hijira
Wani al’amari da ya faru a shekara ta goma bayan Hijira shi ne bayyanar maƙaryata masu da’awar annabta. Ɗaya daga cikinsu shi ne Aswad al-Ansi, wanda ya bayyana a Yaman. Bisa umarnin ƙaunataccen Annabinmu, Musulmin Yaman suka kashe Aswad al-Ansi a gidansa. (Ɗayan kuma Musailima Maƙaryaci (al-Kazzab) ne. Bayan wafatin Shugabanmu Annabi, Sayyidina Abubakar ya aika runduna a kan Musailima ƙarƙashin jagorancin Khalid ɗan Walid. Wahshi (radiyallahu anhu) ne ya kashe Musailima.)3
“A yau Na kammala muku addininku. Na cika ni’imaTa a kanku, Na kuma yarda da ba ku Musulunci ya zama addini” Ma’ida: 3
Ya Sarkin duniya, ya Sarkin teku da tudu!
Ya Annabi na ƙarshe, mara misali, wanda ya fi mala’iku!
“Li ma’allahi waƙtun” yana ba da labarin halinka,
Kai ne rai ga jiki, daɗi ga harshe, sarki ga zuciya.
Ahmad, Muhammadu, Mahmud – Allah koyaushe Yana yabonka;
Da sunanka ne “La ilaha illallah” take cika.
Ɓatacce ba ya fahimta, ba ya sanin wannan sirri mai zurfi!
Da sunanSa ne Rahman Ya rubuta sunanka.
Bayin da suke ƙaunarka suna zama sarakuna, ya sarkina!
Zauna a kan gadon sarautar zuciyata, ya sarkina mara misali!
Ina ƙaunarka ƙwarai, ko da zunubaina suna da yawa!
Na yi imani cewa masu ƙaunarka suna samun rabo daga karamcinka.
Yaya ba zan ƙaunace ka ba, kai ne raina a jikina,
Saboda darajarka na samu, kai ne dalilin rayuwata.
Kai ne jinina a jijiyoyina, ka fi ni kusanci da ni,
Kai ne masoyin masoya, kuma masoyin dukkan rayuka.
Kai ne maganin kowane ciwo, kai ne waraka ga kowane rai,
Kwalli ga ido, rawani ga kai, haske ga zukata kai ne.
Kai ne Habibullah, kai ne wanda ya fi Majalisar Maɗaukakiya,
Wanda ya ɗan san ka ba ya ƙwanƙwasa wata ƙofa.
Jagoran waliyyai, mai shiryar da malamai;
Zuwansa ya faranta wa sammai bakwai da ƙasa rai.
Annabin ƙarshe na Gaskiya ga mutane da aljanu!
Wanda ba bawa ba ne a ƙofarka, ya kasance ƙarƙashin ƙasa!
