Ƙaunataccen Annabina

HAJJIN BANKWANA

A shekara ta goma bayan Hijira, Shugabanmu Annabi ya yi shirin hajji, ya kuma umarci Musulmin Madina su yi shirin hajji. Ya aika da saƙo ga waɗanda suke wajen Madina ma. A kan haka dubban Musulmi suka taru a Madina. Shugabanmu Manzon Allah ya sayi raƙuma ɗari domin yanka. Kafin ya tashi tafiya ya yi wankan janaba. Ya taje gashinsa mai albarka, ya shafa turare, ya sa izar da ridarsa. Da shiri ya kammala, ƙaunataccen Annabinmu ya tashi daga Madina a rana ta 25 ga watan Zulƙa’ada, bayan sallar azahar, tare da ayari na mutum fiye da dubu talatin. Ta hanyar Shajara suka iso Zulhulaifa. A nan adadin Sahabbai ya wuce dubu arba’in. Suka kwana a can. Ƙaunataccen Annabinmu ya sa aka kawo ɗaya daga cikin raƙuma ɗari da ya tafi da su. Ya yi masa zane a gefen dama na tozonsa har jini ya fito, domin ya zama alamar dabbar yanka, ya rataya masa takalma biyu a wuya, ya kuma umarci Sahabbai su yi haka. Ya yi sallar harama raka’a biyu. Bayan ya yi godiya da yabo ga Allahu Ta’ala, Jagoran Halittu ya yi addu’a: “Ya Allah! Ka sanya wannan ya zama mini hajji mabrur kuma karɓaɓɓe, wanda babu riya, nuna wa ido ko neman suna a cikinsa!” Ya shiga harama, da sanarwar Jibrilu alaihis-salam kuma ya fara yin talbiya da babbar murya. Da Sahabbai masu girma ma suka shiga tare da shi, ƙasa da sama suka fara amsawa da sautukan talbiya: “Labbaika, Allahumma labbaik! Labbaika, la sharika laka labbaik! Innal-hamda wan-ni’mata laka wal-mulk, la sharika lak!…”

Suka bi hanyar Baida, suka nufi Malal. A bayansa Sahabbai suka kwararo kamar rigyawa. A hanya kuma mutane suna ta ƙara shiga cikinsu. Da suka iso kwarin Rauha, inda annabawa kusan saba’in, har da Musa alaihis-salam, suka yi salla, Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Wannan kwari yana daga kwaruruka na Aljanna.” Suka yi salla a nan. Daga nan suka tashi zuwa Munsaraf, suka yi sallar asuba a Asasa. Da suka iso Lahyu Jamal, Shugabanmu ya ji rashin lafiya, ya sa aka yi masa kaho (hijama), suka sauka a Suƙya. Da suka iso Abwa, inda uwarsa mai girma Amina ta rasu, ya ziyarci kabarinta, ya yi kuka. Ya sa waɗanda suke tare da shi ma suka yi kuka. Bayan haka suka isa Tal’atul-Yaman, Juhfa, Ghadir Khum, Ƙudaid da kwarin Usfan. A nan Shugabanmu Annabi ya ce wa Sayyidina Abubakar: “Hudu da Salihu alaihimas-salam sun wuce ta nan suna yin talbiya domin hajji, da zannuwan ulu a ɗaure a kugunansu, sanye da yadi mai zane-zane, kowannensu a kan raƙumi matashi mai jan launi, wanda linzaminsa aka saƙa da zaren dabino.”1 Suka ci gaba ta Ghanim, Marruz-Zahran da Sharif, suka iso Zi Ɗuwa. Suka kwana a nan; bayan sallar asuba kuma suka wuce Hajun, suka shiga Makka ta gangaren Kada. Bayan tafiya ta kwana 10, suka isa Makka a rana ta 4 ga watan Zulhijja. Da shigowar waɗanda suka zo daga Yaman da sauran ƙasashe domin yin hajji, adadin Musulmi ya wuce dubu 90. (A wata riwaya dubu ɗari da goma sha huɗu ne, a wata riwaya kuma kusan dubu ɗari da ashirin.)

“Ya Allah! Ka sanya wannan ya zama mini hajji mabrur kuma karɓaɓɓe, wanda babu riya, nuna wa ido ko neman suna a cikinsa!” Hadisi mai daraja

Da Shugabanmu Manzon Allah ya ga Ɗakin Allah, ya yi addu’a:

“Ya Allah! Ka ƙara wa wannan Ɗaki daraja, ɗaukaka, kwarjini da martaba. Waɗanda suke girmama shi da hajji da umra ma, Ka ƙara musu daraja, kwarjini, girmamawa da alheri.”

Sannan ya fara ayyukan hajji (manasik). A tsawon lokacin hajji ya zauna a tanti da aka kafa a Abɗah, tsakanin Makka da Mina. Ƙaunataccen Annabinmu ya tafi Mina a rana ta 8 ga watan Zulhijja (ranar Tarwiya), ya tafi Arafa a rana ta 9 (ranar Arafa). Ya zo kwarin Urana, a tsakiyar kwarin Arafa, ya tsaya a nan. Bayan azahar, a kan raƙumarsa mai suna Ƙaswa, ya yi Huɗubar Bankwana, ya yi bankwana da Sahabbai masu girma radiyallahu anhum.2

NA ZO GARE KA!
Ya mafakar masu zunubi, na zo in nemi mafaka a gare ka!
Na aikata laifuka da yawa, na zo in roƙe ka!
Na karkata zuwa wurare masu duhu, na nutse cikin fadama,
Na zo ga maɓuɓɓugar haske da take haskaka tafarki madaidaici.
Rai ɗaya ya rage mini da zai fita, ya ran dukkan rayuka!
Shin ya dace in ce: na zo in sadaukar da raina?
Kai likitan masu ciwo ne, ni kuwa mai ciwon zuciya.
Domin maganin raunin zuciyata, na zo in ƙwanƙwasa ƙofarka.
Kai wa ƙofar masu karamci wani abu kuskure ne,
Na zo in sumbaci ƙasar da ka ba ta daraja da takawarka.
Zunubaina suna da yawa kamar dutse, fuskata baƙa ce kamar ƙwalta!
Na zo in kuɓuta gaba ɗaya daga wannan kaya da wannan baƙi.
Ɗigo ɗaya daga tekun karamcinka lalle yana tsarkake dukkansu,
Ko da yake baƙi ne kamar fuskata, na zo da littafin ayyukana.
Da zan iya shafa fuskata a ƙofarka, ya masoyi mafi daraja daga raina!
Ayyukan da ruwa ba ya iya yi, suna samuwa daga wannan ƙasa!