Ƙaunataccen Annabina

BUƊEWAR KHAIBAR

A Madina mai haske akwai Yahudawa waɗanda a zahiri Musulmi ne, amma a haƙiƙa munafukai ne. Kafin Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi hijira zuwa Madina, mutanen Madina sun riƙi Abdullahi ɗan Ubayy ɗan Salul shugaba a kansu. Sun kuma ba shi kambi da aka ƙawata da duwatsu masu daraja. Da Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya albarkaci Madina da zuwansa, mutanen Madina gaba ɗaya suka fara girmama ƙaunataccen Shugabanmu Annabi, suna kula da shi, suka bi shi. Ibn Salul ya tsaya a wani lungu cikin halin rashin daraja. Suka daina kula da Ibn Salul. Saboda haka Ibn Salul ya shiga aiki domin ya kashe Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ko ya jawo masa wata wahala. Wata rana Yahudawa suka taru a wurinsa. Suka ƙulla wasu shirye-shirye a kan wannan. Suka nemi taimakon Labid ɗan Asim. Labid ya ce: “A unguwa kaza akwai wata tsohuwa mai suna Khaira. Ta ƙware ƙwarai a yin sihiri. Ku nemo ta.” Suka nemo wannan la’ananniyar mace, suka ba ta zinariya dirhami dubu da kunshin yadi goma. Suka ce: “Idan kika halaka Muhammadu, za mu ƙara ba ki abubuwa da yawa!” Tsohuwar ta soka allurai a jikin wani ɗan tattabara, ta ƙulla zare ƙulli-ƙulli, ta naɗe shi a jikin ɗan tattabaran. Ta sa shi cikin wata rijiya da ta lalace a wajen Madina, ta rufe bakinta. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi rashin lafiya. Gaɓoɓinsa suka kasa motsi. Ko da yake an ba shi magunguna iri-iri, ba su yi amfani ba. Wannan hali ya ɗauki kwana tara.

Sannan Jibrilu alaihis-salam ya zo, ya sanar da al’amarin. Aka kai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) can. Ya buɗe rijiyar, ya fitar da tattabaran. Amma ba a iya kwance ƙullin da suke a zaren ba. Jibrilu alaihis-salam ya kawo surorin Mu’awwizatain (Suratul Falaƙ da Suratun Nas). Ya ce: “Ya Muhammadu alaihis-salam! Ka karanta waɗannan surori a kan waɗannan ƙulli.” Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya fara karanta waɗannan surori. Duk sa’ad da ya karanta aya, ɗaya daga cikin ƙullin yakan kwance, ɗaya daga cikin allurai kuma ta fito. Da ya gama karanta surorin gaba ɗaya (ayoyi 11 na surori biyun), dukkan ƙullin suka kwance. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya warke daga rashin lafiyar gaba ɗaya, ya sami lafiya. Sannan ya sa aka kira waɗannan la’anannun mutane, ya tsawata musu. Mutanen Madina suka yi musu hukunci mai tsanani, har suka halaka. Aka kama Bayahuden nan Labid ma, aka kawo shi gaban Shugabanmu Manzon Allah. Da Shugabanmu Annabi ya ce masa: “Don me ka sa aka yi wannan?”, ya amsa: “Saboda sona ga zinariya.” Da wasu daga cikin Sahabbai masu girma suka ce: “Ya Manzon Allah! Idan ka ba da izini, mu sare wuyan wannan Bayahude!”, ƙaunataccen Annabinmu, wanda bai taɓa hukunta kowa saboda kansa ba, ya ce: “Azabar Allah da zai gani a ƙarshe ta fi tsanani”, bai ba da izinin kashe shi ba.1 Lokacin da aka kori Yahudawa daga Madina, sun tafi ɓangarorin arewacin Ƙasar Larabawa. Wasu daga cikinsu suka zauna a Khaibar. Wasu kuma suka tafi Sham da yake arewa. An fitar da su daga ƙasarsu ne saboda shirya maƙarƙashiyar kisa a kan Shugabanmu Manzon Allah. Amma ƙiyayya, kwaɗayi da ƙudurin ɗaukar fansa da suke cikin zukatansu a kan Musulmi ba su taɓa mutuwa ba. Har ma suna ƙaruwa kullum: suna son su kawo ƙarshen rayuwar Sarkin Halittu, Habibin Allahu Ta’ala, da wuri, su kuma kawar da addinin Musulunci.

Wasu daga cikin manyansu suka ce: “Mu tafi wurin Ghaɗafan mu nemi taimako, mu yi yaƙi da Musulmi tare da su!” Wasu kuma suka ce: “Mu kira Yahudawan Fadak, Taima da Wadil-Ƙura ma zuwa ga taimako, kafin Musulmi su far mana, mu far wa garinsu, mu ɗauki dukkan fansarmu!…” Yahudawan Khaibar suka karɓi wannan magana, suka kira ƙabilun Yahudawa na kewaye da Ghaɗafan zuwa ga taimako. Daga Ghaɗafan kaɗai ma zaɓaɓɓun mayaƙa da yawa suka zo, aka fara shirye-shirye a Khaibar. Yayin da suke waɗannan shirye-shirye, Shugaban Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) ya sami labarin halin Yahudawa. Ya haɗa Sahabbai uku tare da Sayyidina Abdullahi ɗan Rawaha, ya aika shi nan take domin ya gano abin da yake faruwa a Khaibar. Abdullahi ɗan Rawaha da abokansa uku suka isa Khaibar da sauri. Wannan gari mai arziki ne, mai kagarai takwas masu ƙarfi, da waɗansu ƙananan kagarai, da gonaki masu albarka, da gonakin inabi da lambunan ƴaƴan itatuwa masu yawa. Sayyidina Abdullahi ya aika ɗaya daga cikin abokansa zuwa kagarar Shiƙƙ, ɗaya zuwa kagarar Katiba, ɗayan kuma zuwa kagarar Naɗat. Shi kuma ya shiga wata kagara dabam. Kwana uku suka yi nazarin halin Yahudawa da shirye-shiryensu na yaƙi a kurkusa. Bayan kwana uku suka haɗu a wurin haɗuwa, suka isa Madina da sauri, suka ba Shugabanmu Annabi labarin shirye-shiryen Yahudawa ɗaya bayan ɗaya.

Ƙaunataccen Annabinmu ya umarci Sahabbansa da yin shiri cikin gaggawa. Domin ya hana Yahudawa far wa Madina al-Munawwara, ya yanke shawarar tafiya a kan Khaibar. Da Yahudawan da suke Madina suka ji wannan shawara, tsoro ya kama su. Domin su karya gwiwar Musulmi, suna cewa: “Muna rantsuwa, da kun ga kagaran da suke Khaibar da jarumawan mayaƙan da suka taru a can, da ba za ku taɓa taka ƙafa a can ba!… Jarumawa masu sulke ne suke tsaron kagaran masu dogayen hasumiyoyi da suke kan ƙwanƙolin duwatsu. Dubban sojoji sun zo musu taimako daga kewaye!… Shin kuna iya buɗe Khaibar ne?!…” Dangane da haka, jarumawan Sahabbai suna cewa: “Allahu Ta’ala Ya yi wa HabibinSa alkawarin cewa Zai buɗe Khaibar”, suna bayyana cewa ba za su taɓa jin tsoron Yahudawa ba. Wannan ƙudurin Sahabbai ya ƙara ɓata wa Yahudawa rai, ya sa su cikin damuwa. Shugaban munafukai, Abdullahi ɗan Ubayy, ya aika labari zuwa Khaibar cikin gaggawa yana cewa: “Muhammadu yana zuwa kanku da ƙarfi kaɗan. Babu abin tsoro, amma ku yi hattara, ku cika kagaranku da dukiyoyinku. Ku fito daga kagara ku tare su!” Sahabbai masu girma suka kammala shirye-shiryensu, suka yi bankwana da iyalansu, suka nemi yafiya a tsakaninsu, suka taru a kewayen Shugabanmu Annabi. Sun kai mahaya ɗari biyu da masu tafiya a ƙasa dubu ɗaya da ɗari huɗu. Suka shirya bisa umarnin ƙaunataccen Annabinsu domin yaɗa addinin Allahu Ta’ala, yin jihadi da kuma samun matsayin shahada. A wannan lokaci aka ga wasu mata suna neman aiki daga Shugabanmu Annabi, domin su shirya wa Sahabbai masu girma abinci a yaƙin, su kula da waɗanda suka ji rauni da marasa lafiya, su ɗaure raunuka, su shirya magani, su kuma yi sauran ayyukan da za su iya. Shugabanmu Manzon Allah ya ji ƙansu, bai hana su wannan lada ba. Ta haka mata mujahidai ashirin ma suka shiga cikin mujahidai, a gabansu Nana Ummu Salama, matar ƙaunataccen Annabinmu mai albarka.2

Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya bar Sayyidina Siba’, daga ƙabilar Ghifar, a matsayin wakilinsa a Madina, ya ba da umarnin tashi zuwa Khaibar. (An kuma ruwaito cewa Numaila ɗan Abdullahi ne aka bari.) Tafiyar ta fara da kabbara. Sahabban da ba su iya shiga yaƙin ba saboda uzuri, da waɗanda ba a ba su izini ba saboda ƙuruciyarsu, suna kallon Shugabanmu Annabi da jarumawan ubanninsu, kakanninsu, baffanninsu, kawunansu da yayyensu da idon begen kwatanta, suna rakiyarsu da kabbara da addu’o’i.

“Kagarar Khaibar za a buɗe ta ta hannun Aliyu ɗan Abu Ɗalib” Hadisi mai daraja

Kalanda tana nuna watan Muharram na shekara ta bakwai bayan Hijira. Sayyidina Aliyu ne yake ɗauke da tuta mai tsarki ta Shugabanmu Annabi, Sayyidina Umar kuma yake jagorantar reshen dama.3 A reshen hagu kuma ya naɗa wani Sahabi dabam. Tafiya tana gudana cikin farin ciki. Mawaƙa suna gode wa Allahu Ta’ala da waƙoƙinsu saboda ni’imomin da Ya ba su, suna yi wa ƙaunataccen Annabinmu salati, suna yabon Sahabbai masu daraja. Sahabbai kuma, kamar masu zuwa idi, suna sa ko’ina ya yi ta amsa kuwwa da cewa: “Allahu akbar! Allahu akbar! La ilaha illallahu wallahu akbar!”

A kowane masauki Sarkin Halittu yana addu’a yana cewa: “Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga damuwa a kan gaba, da baƙin ciki a kan abin da ya wuce, da rauni da sanyin jiki, da rowa, da tsoro, da bashin da yake karya baya, da kuma rinjayen azzalumai da marasa adalci!”

Lokacin da aka kusanci Khaibar, aka ga ƙaunataccen Annabinmu ya tsayar da Sahabbansa. Ya buɗe hannuwansa, ya fara roƙo yana cewa: “Ya Allah, Ubangijin sammai da abin da suke inuwantarwa! Ya Allah, Ubangijin ƙasashe da abin da yake kansu! Ya Allah, Ubangijin shaiɗanu da waɗanda suke ɓatarwa! Ya Allah, Ubangijin iskoki da abin da suke watsarwa! Muna roƙonKa alherin wannan gari da nagartarsa, alherin mutanen da suke zaune a wannan gari da nagartarsu, da kuma alherin kowane abu da yake wannan gari da nagartarsa. Muna neman tsarinKa daga sharrin wannan gari, da sharrin mutanensa, da sharrin kowane abu da yake cikinsa!”

Daga leɓunan Sahabbai muryoyin “Amin, amin” suke fitowa. Bayan haka ya ce wa Sahabbansa: “Ku ci gaba da tafiya kuna cewa ‘Bismillahir-rahmanir-rahim’.”

Sahabbai masu girma suka sake kama tafiya a kewayen Manzo Mafi Daraja. Suka zo kusa da kagarar Naɗat, ɗaya daga cikin kagarai mafiya ƙarfi na Khaibar.

A can suka kafa sansaninsu. Lokaci magariba ne. Bisa al’ada mai daraja ta Shugabanmu Manzon Allah, ba ya kai hari sai gari ya waye, kuma da farko yakan yi kira zuwa ga Musulunci. Idan ba su karɓi shawararsa ba, sai a fara yaƙi. Saboda haka Sahabbai masu girma suka jira safiya. Babu ɗaya daga cikin Yahudawa da ya gane cewa rundunar Musulunci ta zo. Shugaban Halittu, bayan ya jagoranci sallar asuba, ya kammala shirye-shiryensa, ya tayar da mujahidai. Mahaya ɗari biyu da masu tafiya a ƙasa dubu ɗaya da ɗari huɗu suka kusanci gaban kagarar Naɗat da tafiya mai tsari. A wannan lokaci Yahudawan da suka fito daga kagarar domin aikin gonakin inabi, lambuna da gonaki, da suka haɗu da sojojin Musulunci ba zato ba tsammani, suka ruɗe.

Suka fara gudu suna komawa baya suna cewa: “Muna rantsuwa, waɗannan Muhammadu ne da rundunarsa mai tsari!…” Da ƙaunataccen Annabinmu ya ga wannan halinsu, ya ce: “Allahu akbar! Allahu akbar! Khaibar ta lalace”, ya maimaita wannan magana tasa mai albarka sau uku. Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya sanar wa Yahudawa cewa ko dai su musulunta, ko kuma su miƙa wuya su biya haraji da jizya, in ba haka ba za a yi yaƙi, a zubar da jini. Yahudawa suka tafi wurin Sallam ɗan Mishkam, ɗaya daga cikin manyansu, suka isar masa da al’amarin. Sallam ya ƙarfafa su ga yaƙi yana cewa: “Tun da farko na ce muku ku tafi a kan Muhammadu, ba ku karɓa ba. Aƙalla yanzu kada ku yi sanyin jiki wajen yaƙi da shi. Mutuwarku kuna yaƙi da Musulmi ta fi zamanku a duniya ba ku da kowa!…” Yahudawa suka tara yara da matansu a kagarar Katiba, abincinsu a Na’im, sojojinsu kuma a kagarar Naɗat da sauri.

Yahudawa suka amsa shawarar musulunta ta rundunar Musulunci da harbin kibiyoyi. Mujahidai suka tare kibiyoyin da garkuwoyinsu. Bisa umarnin ƙaunataccen Annabinmu aka ja bakuna, kuma a cikin sautin “Allahu akbar!…” kibiyoyi suka tashi a kan Yahudawan da suke hasumiyoyin kagarar. Yanzu yaƙi ya fara. A gefe ɗaya Sarkin Halittu da jarumawan Sahabbansa suna yaƙi domin yaɗa Musulunci, su zama sanadin musuluntar Yahudawa, su tsira daga Wuta. A ɗaya gefen kuwa akwai Yahudawa, waɗanda ba su fahimtar nasiha, suke son su buga wa Musulmi daga baya a kowace dama, suka taurare a kan ƙin ganin gaskiya. Da suka ga Cikamakin Annabawa (Khatamul-Anbiya) bai fito daga cikin mutanensu ba, saboda hassada ba su karɓe shi ba. Sun yi amfani da kowace irin makirci da ta zo musu a rai domin su kawar da Shugabanmu Annabi tun daga ƙuruciyarsa, amma da kiyayewar Allahu Ta’ala ba su iya yin kome ba.

Sojojin Yahudawa fiye da dubu goma suna harbin kibiya a kan mujahidai masu daraja dubu ɗaya da ɗari shida. Sahabbai masu girma suna kare kansu da garkuwoyinsu daga waɗannan kibiyoyi da suke zuwa a jere, kuma duk sa’ad da suka sami dama, sukan mayar da kibiyoyin da suka faɗi ƙasa a kan Yahudawa. Amma wasu Sahabbai suka ji rauni.

A wani lokaci aka ga Sayyidina Hubab ɗan Munzir ya kusanci gaban Habibullah da ladabi ƙwarai, ya tambaya: “Raina fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Ko ba za mu kafa sansaninmu a wani wuri dabam ba?” Shugabanmu Annabi ya ce: “In sha Allahu ta’ala, idan magariba ta yi za mu canza!” Mujahidai sun shiga cikin nisan harbin kibiya. Kibiyoyin da Yahudawa suke harbawa daga kagarar suna kaiwa har bayan sansanin Musulunci.4 A wannan rana yaƙi ya ci gaba da kibiyoyi har magariba. Sahabbai kusan hamsin suka ji rauni daga kibiyoyin da aka harba. Da magariba ta yi, aka ɗora wa Sayyidina Muhammadu ɗan Maslama aikin neman sabon wurin sansani. Da ya bayyana cewa wurin da ake kira Raji’ ya dace, aka mayar da sansanin Musulunci can.

“Mu annabawa ba ma barin gado. Abin da muka bari sadaka ne ga talakawa” Hadisi mai daraja

Buɗewar Khaibar

Aka fara jinyar waɗanda suka ji rauni.5 Washegari jarumawan Sahabbai suka zo gaban Naɗat, suka yi yaƙi har magariba. A rana ta uku, ta huɗu da ta biyar ma kewayen ya ci gaba. Yahudawa kullum kare kansu kawai suke yi. A waɗannan kwanaki ƙaunataccen Annabinmu ya kamu da ciwon kai mai tsanani, saboda haka kwana biyu bai iya kasancewa a cikin mujahidai ba. A rana ta farko ya ba Sayyidina Abubakar tutar, a rana ta biyu kuma Sayyidina Umar. Dukkansu biyu, a gaban Sahabbai masu girma, sun yi yaƙi mai tsanani ƙwarai da Yahudawa, amma ba a iya buɗe kagarar ba. A wannan lokaci aka ga Yahudawa, waɗanda ƙarfin halinsu ya ƙaru, sun buɗe ƙofofin kagara, suka fara kai hari. Yanzu an fara yaƙi ƙirji da ƙirji. Yaƙi ya yi zafi ƙwarai. Duk sa’ad da Shugabanmu Annabi ya ce wa Sahabbansa: “Ku yi kabbara kuna cewa: Allahu akbar! Allahu akbar!…”, sukan sari abokan gaba da takobi cikin sautin kabbara, da ƙauna da shauƙi. A wani lokaci Mahmud, ɗan’uwan Muhammadu ɗan Maslama, ya yi shahada. Faɗa mai tsanani ya ci gaba har magariba.

Washegari Marhab, ɗaya daga cikin shahararrun kwamandojin Khaibar, ya fito daga kagarar a lulluɓe da sulke. Mutum ne mai ƙarfi da ƙwari, kamar dodo. Har zuwa lokacin babu wani jarumi da ya taɓa fito masa ya kayar da shi. Ya juya ga mujahidai, ya fara alfahari yana cewa: “Ni ne Marhab, wanda aka sani da ƙarfin hali da jaruntaka!” Yayin da yake alfahari haka, aka ga wani mujahidi ya fito gaba daga cikin Sahabbai. Ya yi wa Marhab ihu: “Ni kuma Amir ne, wanda ba ya tsoron jefa kansa cikin tsakiyar yaƙe-yaƙe masu ban tsoro da tsanani!”, nan take ya tsaya a gabansa. Dodon nan Marhab ya sari Sayyidina Amir da dukkan ƙarfinsa da takobinsa, wanda aka rubuta a kansa: “Duk wanda ya taɓa, ya halaka shi!…” Jarumi Amir nan take ya ɗaga garkuwarsa. Da faffaɗan takobin ya bugi garkuwar, wata ƙara mai tsanani ta girgiza kewaye, takobin ya kafe a garkuwar.

Sayyidina Amir ya nemi tsarin Mahalicci, ya ce: “Ya Allah!”, ya sari ƙafafun Marhab masu sulke da takobinsa. Da takobin ya taɓa sulken ƙarfe, sai ya dawo baya, ba zato ba tsammani ya taɓa ƙafar Sahabin da kansa. Dawowar takobin baya da ƙarfi ta sa aka yanke babbar jijiyar jini da take ƙafar Sayyidina Amir. Sahabbai masu girma suka zo da gudu, suka ɗauki Amir, suka kai shi sansani domin jinya. Amma Amir (radiyallahu anhu) a can ya yi shahada, ya tashi zuwa mafi ɗaukakar darajojin Aljanna.6

Yaƙi yana ci gaba da dukkan ƙarfinsa. Zuwa magariba ƙaunataccen Annabinmu ya ba mushrikan Ghaɗafan, waɗanda suka zo wa Yahudawa taimako da sojoji dubu huɗu suka shiga yaƙin, shawarar su rabu, su koma ƙasarsu. Ya kuma yi musu alkawarin cewa idan suka yi haka, zai ba su amfanin dabino na Khaibar na shekara ɗaya. Amma mutanen Ghaɗafan suka ƙi wannan shawara. Sai Shugaban Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) ya umarci Sahabbansa da su wayi gari a kewayen kagarar da mutanen Ghaɗafan suke. Mutanen Ghaɗafan suka ji tsoro ƙwarai kada mujahidai su far musu da dare, ba su iya barci ko kaɗan ba. A daren nan wata murya, da ba a san inda take fitowa ba, tana sanar da cewa an far wa ƙasar Ghaɗafan, an kama iyalansu da dukiyoyinsu. Wannan murya ta maimaita sau uku, dukkan mutanen Ghaɗafan kuwa suka saurare ta cikin tsoro mai girma. Kwamandansu Uyaina ma ya ji wannan murya sau uku, kuma lokacin da gari yake gab da wayewa, ya ɗauki sojojinsa, ya nisanta daga Khaibar da gaggawa, ya kama hanyar ƙasarsu. Da safe Yahudawa suka yi mamakin barin Khaibar da mutanen Ghaɗafan suka yi ba tare da dalili ba, suka yanke ƙauna. Suka kuma yi nadama ƙwarai da kiransu zuwa ga taimako.

“A ranar da muka ci kagarar Khaibar, Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya haramta cin naman jakin gida da auren mata ta hanyar auren mut’a” Sayyidina Aliyu (radiyallahu anhu)

Jaruntakar Sayyidina Aliyu

A ranar ma an yi faɗa mai tsanani a gaban Khaibar, amma ba a buɗe kagarar ba. Da magariba Sarkin Halittu ya yi bushara yana cewa: “Gobe zan ba da tuta ga wani jarumi da yake son Allahu Ta’ala da ManzonSa, Allahu Ta’ala da ManzonSa kuma suna son sa. Allahu Ta’ala Zai tabbatar da buɗewa ta hannunsa!”

A daren nan Sahabbai masu girma suka jira safiya cikin tsananin marmari. Kowannensu yana fatan a ba shi tutar, yana addu’a ga Allahu Ta’ala a kan haka. Sayyidina Bilalu Habashi ya yi kiran sallar asuba da muryarsa mai taɓa zuciya kuma kyakkyawa. Yayin da ake kiran salla, kowa yakan ji wani irin marmari na dabam, wani irin daɗi na dabam, ba a ƙoshi da wannan daɗi mai tsarki. Bayan ƙaunataccen Annabinmu ya jagoranci Sahabbansa a sallar asuba, ya miƙe tsaye. Ya ba da umarnin a kawo tutar Musulunci mai albarka. Yayin da ake kawo tuta mai tsarki, Sahabbai masu girma suna jira a tsaye, suna kasa kunne da zuciya ɗaya domin su ji kalmomin da za su fito daga leɓuna masu albarka na Manzo Mafi Daraja.

A ƙarshe Shugaban Talikai ya ce: “Ina rantsuwa da Allahu Ta’ala, wanda Ya ɗaukaka Muhammadu da annabta, zan ba da wannan tuta ga wani jarumi da bai san mene ne gudu ba”, sannan ya zagaya idanunsa masu albarka a cikin Sahabbansa, ya tambaya: “Ina Aliyu?” Sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah! Idanunsa suna ciwo.” Shugabanmu ya ce: “Ku kira mini shi.” A waɗannan kwanaki Sayyidina Aliyu ya kamu da ciwon ido, bai iya buɗe idanunsa ba. Suka je wurinsa, suka sanar da shi al’amarin, suka kama hannunsa mai albarka, suka kawo shi gaban Shugabanmu Manzon Allah. Sarkin Halittu ya yi addu’a ga Allahu Ta’ala domin Ya ba Sayyidina Aliyu waraka, ya jiƙa yatsunsa masu albarka a bakinsa, ya shafa a idanunsa. A wannan lokaci babu wani ciwo da ya rage a idanun Sayyidina Aliyu. Annabinmu ya sake yi masa addu’a yana cewa: “Ya Ubangijina! Ka kawar masa da wahalar zafi da sanyi!” Sannan ya sa wa Sayyidina Aliyu sulke da hannuwansa masu albarka, ya ɗaura masa takobinsa a kugu, ya ba shi farar tutar Musulunci a hannu, ya ce: “Ka yi yaƙi har Allahu Ta’ala Ya ba ka nasara. Kada ka juya baya!” Sayyidina Aliyu ya ce: “Raina fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Zan yi yaƙi da su har lokacin da suka shiga addinin Musulunci.” Ƙaunataccen Annabinmu ya ce: “Wallahi, idan Allahu Ta’ala Ya shiryar da ko mutum ɗaya ne daga cikinsu ta sanadinka, wannan ya fi maka alheri a kan ka mallaki jajayen raƙuma da yawa, ka ba da su sadaka a tafarkin Allahu Ta’ala.”7

Lokacin da Sayyidina Aliyu yake tafiya zuwa kagarar Yahudawa da tuta a hannunsa, Sahabbai masu daraja ma suka bi bayansa. Da suka kusanci kagarar sosai, lokacin da ake kafa tutar a gindin wani dutse, aka ga ƙofar kagarar Naɗat ta buɗe.

Rundunonin kai hari na Yahudawa suka fito waje. Waɗannan su ne zaɓaɓɓun jarumawan Khaibar. Kowannensu ya sa sulke biyu-biyu, a lulluɓe da kayan kariya na ƙarfe. Aka ga ɗaya daga cikinsu ya nufi Sayyidina Aliyu, ya tsaya a gabansa domin faɗa. Wannan Haris ne, ɗan’uwan Marhab, wanda ba shi da kama a ƙarfin hali. Ya far masa da sauri… Yayin da ƙarar ƙarafa biyu take cika fili, aka ga Zulfiƙar ya sauka kamar walƙiya, ya raba kan Haris da jikinsa. A wannan lokaci muryoyin “Allahu akbar! Allahu akbar!” suka tashi zuwa sammai. Marhab, da ya ji an kashe ɗan’uwansa, ya zo fili a guje tare da sojojin da suke ƙarƙashinsa. Ya tsaya a gaban Sayyidina Aliyu. Shi ma yana da sulke biyu a jikinsa. Ya ɗaura takobi biyu, kuma da girman jikinsa kamar wani dodo yake. Da dukkan fushinsa ya fara yabon kansa yana cewa: “Ni ne Marhab, wanda yake fitowa fili a lokacin da yaƙe-yaƙe suka fi tsanani, yana yaƙi da jaruntaka! Ni, ko zakoki masu ruri ma nakan huhhuda su da mashina ko takobina!…”

Sayyidina Aliyu (karramallahu wajhahu wa radiyallahu anhu) ya amsa masa yana cewa: “Ni ne wanda uwata ta sa masa suna Haidar (Zaki). Ni kamar zaki mai girman gaske nake! Ni jarumi ne da zan kayar da kai ƙasa da buga ɗaya!…”

Da Marhab ya ji kalmar “Haidar” daga Sayyidina Aliyu, tsoro ya faɗa zuciyarsa. Domin da dare, a mafarkinsa, wani zaki ya yayyaga shi. Shin zakin da ya gani a mafarki wannan ne? A wannan lokaci dodon nan Marhab ya kai hari, Sayyidina Aliyu ya tare shi da garkuwarsa. Sannan ya nemi tsarin Allahu Ta’ala, ya ce: “Ya Allah!…”, ya sauko da Zulfiƙar a kan kafirin da irin ƙarfin da ya tsaga garkuwar ƙarfe mai kauri, wadda babban Marhab ya riƙe a gaban Zulfiƙar, da kwalkwalinsa da aka yi da ƙarfe gida biyu, ya raba kansa gida biyu daga samansa har zuwa ƙeyarsa. Jini ya ɓuɓɓugo daga wuyansa kamar maɓuɓɓuga, jikinsa irin na dodo ya faɗi ƙasa. Ƙarar Zulfiƙar mai ban tsoro an ji ta a kowane lungu na Khaibar. Shugabanmu Annabi ya ce: “Ku yi farin ciki! Buɗewar Khaibar yanzu ta sauƙaƙa.” Sahabbai masu girma suka yi mamakin wannan jaruntaka ta Sayyidina Aliyu, suka girgiza sama da muryoyin “Allahu akbar! Allahu akbar!…”

Faɗa yana ci gaba da dukkan ƙarfinsa. A wani lokaci da Sahabbai masu girma suka iso kusa da ƙofar kagarar suna yaƙi, wani Bayahude ya bugi garkuwar Sayyidina Aliyu da takobinsa. Garkuwar ta faɗi ƙasa, amma babu lokacin sunkuyawa a ɗauke ta. Bayahuden, wanda bai so ya rasa damar ba, ya ƙwace garkuwar, ya gudu baya. Zakin Allahu Ta’ala, wanda wannan ya ɓata masa rai ƙwarai, bayan ya watsar da abokan gaba da suke kewaye da shi da Zulfiƙar, ya yi niyyar mayar da ƙofar kagarar garkuwa. Ya ce: “Bismillahir-rahmanir-rahim”, ya kama zoben babbar ƙofar ƙarfe. Ya girgiza ƙugiyoyinta daga bango, ya cire su… Lokacin da Sayyidina Aliyu yake cire ƙofar, kagarar ta girgiza daga wurinta. Ya mayar da wannan ƙofa, wadda jarumawa takwas ko goma ba za su iya motsa ta daga wurinta ba, garkuwa da hannu ɗaya, ya fara yaƙi. Wannan al’amari mai wuyar gaskatawa mu’ujizar ƙaunataccen Annabinmu ce da kuma karamar Sayyidina Aliyu.8

A gabansa kuma wasu jarumawa shida daga cikin mafiya jarumtar Yahudawa suka fito ɗaya bayan ɗaya. Sayyidina Aliyu, wanda ya kayar da su ma da izinin Allahu Ta’ala, ya shiga kagarar tare da jarumawan abokansa. Yanzu ana yaƙi a cikin kagarar. A cikin ɗan lokaci babu wanda ya rage da zai fito musu. Suka kafa tutar Musulunci a kagarar. Ta haka aka buɗe Naɗat, kagararsu mafi ƙarfi. Ƙaunataccen Annabinmu ya sumbaci idanun Sayyidina Aliyu, ya ce: “Saboda jaruntakar da ka nuna, Allahu Ta’ala da ManzonSa sun yarda da kai.” Da Aliyu ya ji wannan magana mai albarka, ya yi kuka saboda farin ciki. Da Shugabanmu Annabi ya tambaya: “Don me kake kuka?”, ya ce: “Raina fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Ina kuka ne saboda farin ciki. Domin Allahu Ta’ala da ManzonSa sun yarda da ni.” Sai ƙaunataccen Annabinmu ya ce: “Ba ni kaɗai ba, Jibrilu, Mika’ilu da dukkan mala’iku sun yarda da kai.” A wannan lokaci Musulmi ɗari huɗu daga ƙabilar Daus suka zo wa Shugabanmu Annabi taimako.9 Bayan haka faɗa ya ci gaba da tsanani domin buɗe sauran kagarai. Da sauran kagarai bakwai masu ƙarfi na Khaibar ma suka faɗi ɗaya bayan ɗaya, Yahudawa, waɗanda suka rasa mafita, suka aika wakilai, suka nemi sulhu. Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya karɓi wannan shawara, suka yi yarjejeniya a kan sharuɗɗan nan: 1. Ba za a zubar da jinin Yahudawan da suka yi yaƙi da Musulmi a wannan yaƙi ba. 2. Yahudawan da suka bar Khaibar za su iya tafiya da ƴaƴansu kawai da kuma kayan gida masu muhimmanci, kaya ɗaya na raƙumi. 3. Sauran dukiyoyi duka, masu motsi da marasa motsi; dukkan makamai irin su sulke, takobi, garkuwa, baka, kibiya; dukkan tufafi ban da waɗanda suke jikinsu; yadudduka, zinariya da kuma taskoki, dukkan dabbobi irin su dawakai, raƙuma, tumaki… duk abin da yake akwai zai zama na Musulmi. 4. Ba za a ɓoye kowane abu da ya kamata a bar wa Musulmi ba ta kowace hanya. Waɗanda suka ɓoye za su fita daga amincin Allahu Ta’ala da ManzonSa da kariyarsu…

“Ni ne wanda uwata ta sa masa suna Haidar (Zaki). Ni kamar zaki mai girman gaske nake!” Sayyidina Aliyu (radiyallahu anhu)

Kinana ɗan Rabi’, wanda bai kiyaye waɗannan sharuɗɗa ba, ya binne taskokinsa a ƙasa cikin salkuna, aka hukunta shi. Ganimar da aka samu ba ta da iyaka. Waɗannan gonaki masu albarka na Khaibar da gonakin dabinonsa duka suka koma hannun rundunar Musulunci.10 A wannan lokaci mutanen Ghaɗafan, waɗanda suka koma ƙasarsu, sun sake dawowa Khaibar domin su taimaki Yahudawa. Da suka ga Shugabanmu Annabi ya buɗe Khaibar, ya sa Yahudawa sun miƙa wuya, suka ce: “Ya Muhammadu! Ka yi mana alkawarin cewa idan muka bar Khaibar, za ka ba mu dabinon Khaibar na shekara ɗaya. Mun cika maganarmu. Yanzu ka ba mu shi!” Shugabanmu ya ce musu: “Dutse kaza ya zama naku.” Mutanen Ghaɗafan suka yi ƙoƙarin yin barazana suna cewa: “To, idan haka ne, za mu yi yaƙi da ku.” Manzo Mafi Daraja ya ce: “Wurin yaƙinmu ya zama Janafa.” Janafa sunan wani yanki na mutanen Ghaɗafan ne. Da mutanen Ghaɗafan suka ji haka, suka ja da baya suka tafi saboda tsoro.

Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) da jarumawan Sahabbansa sun gaji ƙwarai a lokacin buɗewar Khaibar. A gefe ɗaya ana jinyar waɗanda suka ji rauni, a ɗaya gefen kuma suna hutawa.

Zainab, matar Sallam ɗan Mishkam, ɗaya daga cikin manyan Yahudawa, ta so ta kashe Shugabanmu Annabi da guba. Saboda haka ta yanka tunkiya ta dafa, ta zuba guba mai yawa a naman. Sannan ta zo gaban Shugabanmu Manzon Allah, ta ce ta kawo kyauta. Manzo Mafi Daraja ya karɓa, ya kira Sahabbansa, duk suka zauna tare domin cin abinci. Shugaban Talikai ya yanko wani guntu daga gasasshen naman tunkiyar, ya ce: “Bismillahir-rahmanir-rahim”, ya sa a bakinsa mai albarka. Bayan ya tauna sau kaɗan, nan take ya fitar da shi daga bakinsa mai albarka, ya ce: “Ya ku Sahabbaina! Ku janye hannuwanku daga wannan abinci! Domin wannan naman kafaɗa ya sanar mini da cewa an sa masa guba.” Sahabbai nan take suka janye hannuwansu daga abincin. Amma Sayyidina Bishr ɗan Bara’u, wanda ya ci loma ɗaya daga naman, jikinsa ya yi shuɗi nan take, ya yi shahada. Jibrilu alaihis-salam ya zo wa ƙaunataccen Annabinmu, ya ce masa ya sa a yi masa kaho (hijama) a tsakanin kafaɗunsa masu albarka domin ya kuɓuta daga tasirin gubar da ta haɗu da yawunsa mai albarka. Aka yi haka. Sannan aka binne gasasshen naman mai guba a ƙasa. Aka kama Zainab, wadda ta yi wannan aiki, aka kawo ta gaban Annabi.

Shugabanmu ya ce mata: “Ke kika sa wa wannan gasasshen naman tunkiya guba?” Ta amince da abin da ta yi, ta ce: “E! Ni na sa masa guba!” Da Shugabanmu Annabi ya tambaya: “Don me kika so ki yi wannan?”, ta ce: “Ka kashe mijina, ubana da baffana. Na ce wa kaina: ‘Idan da gaske shi annabi ne, Allah Zai sanar da shi. In ba haka ba, wannan guba za ta yi masa tasiri, ya mutu. Ta haka za mu kuɓuta daga gare shi.’” Sahabbai masu girma suka yi baƙin ciki ƙwarai da wannan al’amari. Da suka tambaya: “Rayukanmu fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Mu kashe wannan?”, Shugaban Talikai, wanda yake yafe kowane cin mutunci da aka yi masa, ya yafe wannan ma. Da Zainab ta ga wannan rahama mai girma, ta faɗi kalmar shahada, ta musulunta.11 A cikin ganimomi da fursunonin da aka kama a Khaibar akwai Safiyya, ƴar Huyayy ɗan Akhɗab. Ta faɗa rabon Shugabanmu Annabi a matsayin hakkin babban kwamanda. Shugaban Talikai ya ƴanta fursunarsa. Ita kuwa wannan ya taɓa zuciyarta ƙwarai, ta faɗi kalmar shahada daga zuciyarta, ta musulunta. Ƙaunataccen Annabinmu, wanda ya yi farin ciki ƙwarai da wannan, ya ɗaukaka uwarmu Nana Safiyya da aurenta, ya faranta mata rai. Ta haka Nana Safiyya ta zama uwar muminai. An yi bikin aurenta a wurin da ake kira Sahba, aka yi walima, wato liyafar aure, da guna da dabino.12

A idanun uwarmu Safiyya masu albarka ana ganin wata alamar shuɗi.

Da ƙaunataccen Annabinmu ya tambaya: “Mene ne wannan alama?”, ta ce: “Wani dare na ga a mafarki wata ya sauko daga sama, ya shiga kirjina. Da na faɗa wa mijina Kinana, ya ce: ‘Kin sa ido ne a kan zama matar wancan sarkin Larabawa da yake zuwa kanmu!’, ya mare ni a ido, kuma kamar yadda kake gani, ya yi shuɗi.” Bayan an buɗe Khaibar, Yahudawa suka zo wa Shugabanmu Annabi da wannan shawara: “Ya Muhammadu! Mu za mu bar Khaibar mu tafi. Amma mu mun ƙware a noma da kula da gonaki, gonakin inabi da lambuna. Idan kana so, ka ba mu waɗannan gonaki masu albarka haya. Mu yi aikin waɗannan dukiyoyi, mu ba ka rabin amfanin da ya fito!” Ƙaunataccen Annabinmu da Sahabbai ba su da lokacin shagaltuwa da aikin gona. Suna ƙoƙari ne domin yaɗa addinin Musulunci, suna aiki ba tare da tsayawa ba, suna haɗa dare da rana, domin jihadi a tafarkin Allah (jihadi fi sabilillah).13 Shugabanmu Annabi ya yarda da wannan shawara, ya ce: “Da sharaɗin mu fitar da ku duk lokacin da muka so.” Yahudawa suka karɓi wannan, suka fara aikin gonakin Khaibar.14 Shugabanmu Annabi ya koma Madina tare da Sahabbansa a matsayin masu nasara. A waɗannan kwanaki Sahabban da suka rage na ƙarshe daga cikin masu hijira zuwa Habasha, waɗanda a cikinsu akwai Ummu Habiba (radiyallahu anha), ƙarƙashin jagorancin Ja’afar ɗan Abu Ɗalib, suka shiga jiragen ruwa biyu da Najashi ya ba su, suka sauka a tashar jiragen ruwa ta Jar. Daga can suka hau raƙuma, suka zo Madina. Da Annabinmu ya ga Sahabbansa, waɗanda suka yi hijira zuwa Habasha shekara goma sha biyu da suka wuce, sun dawo ƙarƙashin jagorancin Ja’afar ɗan Abu Ɗalib, ya yi farin ciki ƙwarai. Ya sumbaci goshin Sayyidina Ja’afar, ya rungume shi a ƙirjinsa, ya ce:

“Ya ku Sahabbaina! Ku janye hannuwanku daga wannan abinci! Domin wannan naman kafaɗa ya sanar mini da cewa an sa masa guba” Hadisi mai daraja

“Ban san ko da buɗewar Khaibar zan yi farin ciki, ko da dawowar Ja’afar ba. Hijirarku ta ninka biyu: kun yi hijira zuwa ƙasar Habasha, kun kuma yi hijira zuwa ƙasata.” Suka miƙa wa Manzon Allah kyaututtuka da wasiƙar da Najashi Ashama ya aika. An yi bikin auren uwarmu Ummu Habiba ma a wannan shekara. A lokacin uwarmu Ummu Habiba tana da shekara talatin da shida. Ganimar da aka samu a Khaibar aka raba ta ga dukkan Sahabbai masu girma da suka halarci yarjejeniyar Hudaibiyya, da waɗanda suka halarci Khaibar, da Sahabban da suka yi hijira daga Habasha, da kuma ƙabilar Daus da ta shiga buɗewar.15

Da buɗewar Khaibar, dukkan Yahudawan Ƙasar Larabawa suka shiga ƙarƙashin umarnin Shugabanmu Annabi. Yanzu ba su da sauran damar taimakon mushrikai. Ƙabilu da daulolin da suke kewaye ma suka fahimci cewa Musulmi, waɗanda suka ci kagarar Khaibar, wadda ta fuskar makamai da sojoji ta yi kamar ba za a iya buɗe ta ba, suna da ƙarfi mai girma, suka fara jin tsoron wannan Daular Musulunci. Mushrikan Makka suka faɗa cikin babban baƙin ciki da yanke ƙauna saboda buɗewar Khaibar. Bayan wannan buɗewa, ƙabilu da dama, ƙanana da manya, suka zo Madina al-Munawwara domin su musulunta, suka sami darajar kasancewa daga cikin Sahabbai masu girma, har ma mutanen Ghaɗafan… Wasu ƙabilun da ba su shiga hanya ba kuwa aka aika musu da runduna, aka sa su yin ɗa’a.