TARBIYYAR SAHABBAI MASU GIRMA
Masallacin Annabi
Da Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya albarkaci Madina da zuwansa, aiki na farko da yake so a yi shi ne a gina masallacin da zai tarbiyyantar da Sahabbansa a cikinsa, a yi sallar jam’i. A wannan lokaci Jibrilu alaihis-salam ya zo, ya ce: “Ya Manzon Allah! Allahu Ta’ala Yana umartarka da ka gina Masa gida (masallaci) da dutse da tubali.” Habibi Mafi Daraja nan take ya so ya sayi, daga hannun masu shi, wurin da raƙumarsa Ƙaswa ta durƙusa a lokacin da suka zo Madina. Masu wurin suka yi matuƙar son su ba da shi kyauta, suna cewa: “Ya Manzon Allah! Mu, kuɗinsa daga wurin Allah Maɗaukakin Sarki kaɗai muke sa rai. Wannan wuri muna ba ka shi kyauta saboda yardar Allah.” Duk da haka Shugabanmu bai karɓa ba, ya biya kuɗinsa fiye da yadda ya kamata.1
A gefe guda ana daidaita filin ana gyara shi, a ɗaya gefen kuma ana yanka tubali, ana jan duwatsu. A ƙarshe, bayan an kammala kowane shiri, aka taru don kafa harsashi. Dutse na farko na harsashin, Muhammadu Mustafa sallallahu ta’ala alaihi wa sallam ne ya sanya shi da hannuwansa masu albarka. Sannan ya ce bi da bi: “Abubakar ya sanya dutsensa kusa da dutsena! Umar ya sanya dutsensa kusa da dutsen Abubakar! Usman ya sanya dutsensa kusa da dutsen Umar! Aliyu ya sanya dutsensa kusa da dutsen Usman!” Bayan an aiwatar da umarninsa, ya ce wa Sahabbai masu girma da suke wurin: “Ku ma ku sanya duwatsunku.” Su ma suka fara sanyawa.
A gina masallacin, tun daga ƙaunataccen Annabinmu har zuwa dukkan Sahabbai masu girma, suka yi aiki ba fasawa, ba hutawa. Suka ɗauki dutse da tubali a bayansu masu albarka. Suka ɗaga harsashin da dutse har tsawon mita ɗaya da rabi, a kansa kuma suka gina da tubali. Wata rana Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yana ɗauke da tubali yana tafiya. Ɗaya daga cikin Sahabbansa ya zo gabansa mai daraja, ya ce da ladabi na musamman: “Ya Manzon Allah! Za ka yarda ni in ɗauki tubalin?” Cikamakin Annabawa ya sanar da shi, da ladabi mafi girma, cewa shi da kansa ya fi buƙatar samun lada, bai ba shi tubalin ba. Ya shawarce shi shi ma ya je ya kawo dutse.
A gina Masallacin Annabi, ɗaya daga cikin waɗanda suka fi kowa yin aiki Shugabanmu Manzon Allah ne. Yakan ɗauki duwatsu mafi nauyi, ya kai su wurin masu gini, ƙirjinsa mai albarka yana matsewa. Yayin da yake ɗaukar waɗannan duwatsu da tubula, yakan ƙarfafa gwiwar Sahabbansa da bayyana darajar aikin da ake yi, da bushara da ni’imomin da za a samu.
Musulmi, da suka ga wannan ƙoƙari na Shugabanmu, suna aiki da matuƙar ƙauna. Har ma, yayin da kowa yake ɗaukar tubali ɗaya-ɗaya, Ammaru ɗan Yasir yakan ɗauki tubali biyu – ɗaya saboda Shugabanmu Annabi, ɗaya kuma saboda kansa. Da Shugabanmu Manzon Allah ya ga wannan hali, ya zo wurinsa. Ya shafa bayan Sayyidina Ammaru da hannuwansa masu albarka, ya ce: “Ya ɗan Sumayya! Kai kana da lada biyu, sauran kuwa ɗaya!”
Aka kammala bangwayen masallacin cikin ɗan lokaci kaɗan, aka rufe samansa. Ɗakunan, bisa al’adar Larabawa, na rassan dabino ne, samansu kuma an rufe su da lulluɓin da aka yi da gashi. A ƙofofinsu labule kawai aka rataya. Ɗakunan suna gefen kudu maso gabas da gefen arewa na masallacin. Ƙofofin mafi yawansu suna buɗewa zuwa masallacin. Tsayin rufinsu ya fi tsayin mutum matsakaici da taƙi ɗaya. Tsakanin ɗakin Nana Fatima da na Nana A’isha akwai ƙofa. Bugu da ƙari, manne da masallacin, aka gina ɗakuna biyu na tubali saboda Shugabanmu Manzon Allah. Samansu ma an rufe su da kututturen dabino da rassansa. Da shigewar lokaci aka ƙara waɗannan ɗakuna har zuwa tara. Bayan an gama gina masallacin, Shugabanmu Annabi ya ƙaura daga gidan Sayyidina Khalid ɗan Zaid zuwa gidan da aka gina masa.2
“Muminai ƴan’uwan juna ne kawai” Hujurat: 10
YA MANZON ALLAH!
Abin da yake sa masoya haukar kewa koyaushe
– fuskarka ce, ya Manzon Allah.
Abin da yake sa su nishi da ciwo safe da yamma
– kewarka ce, ya Manzon Allah!
Abin da ya mayar da aikina kuka dare da rana,
ya ƙona zuciyata da wutar kewa,
yake sa idanuna kuka ba fasawa
– rabuwa da kai ce, ya Manzon Allah!
Falalar Allah da asfiya suka gani,3
daɗi da walwala da waliyyai suka ɗanɗana,4
ɗaukakar da annabawa suka samu, ya sarki,
– dukiyarka ce, girmanka ne, ya Manzon Allah!
Ka ji ƙaina, baƙo mai yawo ba gida,
mai laifi ne ni, ka ji tausayin baƙar fuska,
jin ƙan maraya da marar mafita
– al’adarka ce, ya Manzon Allah!
Ya mai ceton masu zunubi, nurin Allah Makaɗaici,
Nasuhi bawanka ne, kada ka kore shi.
Ka yi karamci, kada ka mayar da shi daga ƙofar falalarka,
daga al’ummarka yake, ya Manzon Allah!
Nasûhî Üsküdârî
Nishin kututturen dabino
A Masallacin Annabi akwai wani kututturen dabino kafe. Shugabanmu Annabi a ranakun Juma’a yakan yi huɗuba yana jingina da wannan ginshiƙi na masallacin, mai suna Hannana.
Daga baya ya sa aka yi masa mimbari mai mataki uku. Wata ranar Juma’a Shugabanmu Manzon Allah da Sahabbai masu girma suka taru a Masallacin Annabi. Da Shugabanmu ya hau sabon mimbarin don huɗuba, busasshen kututturen dabinon da yake jingina da shi a da ya fara kuka da nishi da muryar da ta yi kama da kukar raƙuma masu ciki, har kowa yana ji. Dukkan Sahabbai masu girma suka saurari wannan murya cikin mamaki. Amma muryar ba ta yanke ko kaɗan ba. Sai Shugaban Talikai ya sauka daga mimbarin, ya shafi kututturen da hannuwansa masu albarka. Nan take kukan da nishin suka yanke. Sahabban da suka ga wannan ƙauna da shauƙi na busasshen kututturen dabino ga Annabinmu, ba su iya riƙe hawayensu ba.
Game da wannan al’amari Sayyidina Anas ɗan Malik ya ce: “Har masallacin ma ya girgiza da muryarsa”, Ibn Abi Wada’a kuma ya ce: “Kututturen dabinon ya tsage, ya motsa daga wurinsa. Sai da Shugabanmu Manzon Allah ya zo ya ɗora hannunsa mai albarka a kansa, sannan ya yi shiru.”
Shugabanmu Annabi ya ce: “Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda raina yake a hannun ikonSa, da ban shafe shi ba, da ya ci gaba da kuka haka har zuwa Ranar Ƙiyama saboda kewarsa gare ni da baƙin cikinsa.” A wata riwaya an sanar da haka: Manzo alaihis-salam ya juya ga busasshen kututturen dabinon, ya ce: “Idan ka so, in mayar da kai lambun da kake a da. Ka sake fitar da rassa da ganye, ka koma halinka na da. Idan ka so, in dasa ka a Aljanna, masoyan Allahu Ta’ala su ci daga ƴaƴanka.” Shugabanmu Manzon Allah ya kasa masa kunne, ya ji yana cewa: “Ka dasa ni a Aljanna, masoyan Allahu Ta’ala su ci daga gare ni, in kasance a wurin da ba zan tsufa ba, ba zan ruɓe ba.” Wannan magana ta itacen, waɗanda suke wurin Shugabanmu Annabi ma sun ji ta. Sai Shugabanmu Manzon Allah ya amsa masa: “Zan yi abin da kake so.” Sannan ya juya ga Sahabbansa, ya ce: “Ya fifita gidan dawwama (darul-baƙa) a kan gidan ƙarewa (darul-fana, wannan duniya).”5 Sannan bisa umarnin Manzon Allah aka binne kututturen dabinon.
Zuwan iyalai Madina
Lokacin da Jagoran Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) da Sayyidina Abubakar suka yi hijira, sun bar ƴaƴansu a Makka. A cikin hadisi mai daraja da Imam Bukhari ya riwaito, Nana A’isha ta ce: Shugabanmu Manzon Allah ya ce mini: “Ya A’isha! An nuna mini ke a mafarki sau biyu. Sai na ga hotonki a cikin wani yankin tufafin alharini kore, aka ce mini: ‘Mai wannan hoto ita ce matarka ta gaba.’” Bayan wannan mafarki (shekara guda bayan rasuwar uwarmu Nana Khadija), an ɗaura alkawarin aure tsakanin Shugabanmu Annabi da uwarmu Nana A’isha tun suna Makka. Amma ba a riga an yi biki ba. Uwarmu Nana A’isha ta ba da labarin haka kamar haka: “Lokacin da Manzon Allah ya yi hijira zuwa Madina, ya bar mu da ƴaƴansa mata a Makka. Da ya albarkaci Madina da zuwansa, ya aiko mana da bawansa da ya ƴanta, Zaid ɗan Harisa, da Abu Rafi’, da raƙuma biyu da kuɗin guzuri dirhami 500 don su sayi abubuwan da za su buƙata.
Babana ma ya rubuta wa ɗan’uwana Abdullahi wasiƙa, ya umarce shi ya haɗa Abdullahi ɗan Uraiƙiɗ tare da su da raƙuma biyu-uku, ya hau da uwata, ni da ƴar’uwata Asma’u a kan raƙuma ya aiko da mu. Ni, uwata Ummu Ruman, daga cikin ƴaƴan Manzon Allah Nana Fatima az-Zahra da Ummu Kulsum, matarsa Sauda, da Ummu Aiman da Usama, dukkanmu muka fita tafiya tare. Da muka isa wurin Ƙudaid, Zaid ya ƙara sayen raƙuma uku da dirhami 500. Ɗalha ɗan Ubaidullahi ma ya haɗu da ayarin. Lokacin da muka isa wurin da ake kira Baid daga Mina, raƙumata ta gudu. Ni ina cikin shimfiɗar hawa ne. Uwata ma tana kusa da ni. Uwata tana kaɗuwa, tana cewa: ‘Kaitona, ƴar ƙaramar ƴata, kaitona, ƙaramar amaryata!’ Allahu Ta’ala Ya kwantar da raƙumarmu, Ya cece mu. A ƙarshe muka iso Madina. Ni na sauka tare da iyalan babana. Iyalan Shugabanmu Manzon Allah kuwa suka sauka a gaban ɗakunansa.”
“Da ban rungume shi (Hannana) ba, da ya yi kuka har zuwa Ranar Ƙiyama saboda rabuwa da ni” Hadisi mai daraja
Uwarmu Nana A’isha ma ta zauna na ɗan lokaci a gidan babanta Sayyidina Abubakar. Bikinsu bayan Yaƙin Badar aka yi shi.
Yaya rabon wancan mutum,
wanda karatunsa Alƙur’ani ne!
Da ya ji kiran salla da iƙama,
zuciyarsa ta cika da imani!
Azan-i Muhammadi
Bayan an gina Masallacin Annabi, a lokutan salla babu wata hanya da za ta sanar da shigowar lokaci, ta kira Musulmi zuwa masallaci. Kawai ana cewa: “As-salatu jami’a (Ku zo salla).”
Wata rana Shugabanmu Manzon Allah ya yi shawara da Sahabbansa, ya tambaya yadda ya kamata a kira muminai zuwa masallaci a lokutan salla. Wasu suka ce, domin sanar da lokutan salla, mu buga naƙus, wato ƙararrawa, kamar Nasara; wasu suka ce a busa ƙaho kamar Yahudawa. Wasu kuma suka faɗi ra’ayinsu da cewa: “A lokacin salla mu hura wuta mu ɗaga ta sama.” Shugabanmu Manzon Allah bai karɓi ko ɗaya ba.6
Abdullahi ɗan Zaid ɗan Sa’alaba da Sayyidina Umar suka ga ana kiran salla (azan) a mafarki. Sayyidina Abdullahi ya zo wurin ƙaunataccen Annabinmu, ya ba da labarin mafarkinsa kamar haka: “Na ga wani mutum sanye da koren mayafi, ya ɗaura zani, yana riƙe da ƙararrawa a hannunsa. Na tambaye shi: ‘Za ka sayar da ƙararrawar da ke hannunka?’ Ya ce mini: ‘Me za ka yi da ita?’ Da na ce: ‘Zan buga ta don sanar da lokutan salla’, mutumin nan ya ce: ‘Bari in koya maka abin da ya fi wannan alheri’, ya fuskanci alƙibla, ya fara karantawa da babbar murya: ‘Allahu akbar, Allahu akbar…’ Bayan ya gama kuma, ya ce: ‘A lokacin da za ka tashi salla kuma’, ya sake maimaita azan, kuma a ƙarshenta ya ƙara jumlar ‘Ƙad ƙamatis-salatu’.”
Sai Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Mafarkin gaskiya ne. Ka koya wa Bilalu waɗannan kalmomi, ya karanta!” Aka ba wannan suna azan.7
Sayyidina Bilalu kuma ya hau wani rufin gida mai tsayi da yake kusa da Masallaci mai daraja, ya karanta azan ta farko da kalmomin da aka koya masa.
Da Sayyidina Umar ya ji muryar azan, ya zo wurin Shugabanmu Manzon Allah a guje. Ya bayyana cewa ya ga kalmomin da Sayyidina Bilalu ya faɗa daidai haka a mafarkinsa. A wannan dare wasu daga cikin Sahabbai masu girma ma sun yi irin wannan mafarki. A daidai wannan lokaci ne aya ta 9 mai girma ta Suratul Juma’a ta sauka, aka kuma sanar da haka ta wahayi.
Wata rana a lokacin sallar asuba Bilalu Habashi ya yi kira sau biyu a gaban ƙofar ƙaunataccen Annabinmu: “As-salatu khairun minan-naum.”8 Shugabanmu Annabi ya so wannan. Ya ce: “Bilalu, wannan kalma mai kyau ce ƙwarai! Idan kana azanin asuba, ka faɗi wannan ma.” Ta haka aka fara faɗar wannan kalma ma a azanin asuba.
Bilalu Habashi, wanda ya yi ladanci har zuwa wafatin Annabinmu, muryarsa ƙaƙƙarfa ce, mai kyau ƙwarai kuma mai matuƙar tasiri. Idan ya fara azan, kowa yakan saurara cikin babbar ƙauna da shauƙi, ya shagala. Idan yana azan yakan sa kowa kuka.
Yadda Sahabbai masu girma suke kiran juna zuwa masallaci a lokutan salla da Azan-i Muhammadi ya yi wa mushrikan Madina da Yahudawa baƙon abu ƙwarai. Idan ana azan sukan yi ba’a, su mai da ita abin wasa. Game da wannan wulaƙanci nasu, Allahu Ta’ala Ya ce a cikin Alƙur’ani mai girma, a ma’ana: “Idan kun yi kira zuwa ga salla da azan, sukan riƙe ta abin wasa da ba’a. Wannan kuwa saboda su mutane ne da ba su hankalta.”9
Ladan ya yi kira, ya tsaya, ya tayar da iƙama,
Ya fuskanci Ka’aba da fuskarsa, ya kuma yi niyya.
Da ma’abuta imani suka ji, suka saurara da girmamawa,
Sannan suka tsaya salla, suka bauta wa Ubangiji.
Ashabus-Suffa
Shugabanmu Annabi ya sa aka yi wata rumfa da rassan dabino a bangon arewa na Masallacin Annabi. Ya umarci Sahabbai marasa aure da suka yi hijira daga Makka, waɗanda ba su da dukiya ko mallaka, su kwana su tashi a nan.10 Waɗannan Sahabbai marasa aure da talakawan Ansar da Muhajirun suna rayuwa a ƙarƙashin babbar rumfar nan da ake kira Suffa kusa da Masallacin Annabi, suna shagaltuwa da koyon ilimi da koyarwa. Adadinsu yakan canza tsakanin goma da ɗari huɗu. Mafi yawan lokaci sukan kasance mutum saba’in. Waɗannan Sahabbai ba sa rabuwa da Shugabanmu Manzon Allah ko kaɗan, ba sa rasa majalisinsa ko kaɗan. Dare da rana suna karatun Alƙur’ani mai girma, suna koyon ilimi, suna haddace hadisai masu daraja. Mafi yawan kwanakinsu suna azumi; ba sa rabuwa da ibada da ɗa’a ko na ɗan lokaci. Waɗanda suka sami tarbiyya a nan ana aika su zuwa ƙabilun da suka musulunta sababbi, su koya musu Alƙur’ani mai girma da sunna mai daraja, wato addinin Musulunci. Waɗannan Sahabbai masu albarka, ma’abuta falaloli masu yawa ƙwarai, babbar rundunar ma’arifa ce. Shugabanmu Annabi yana ƙaunarsu ƙwarai, yakan zauna da su ya yi majalisi, ya ci abinci tare da su. Waɗanda suke zama a nan ana kiransu Ashabus-Suffa. Wata rana Shugabanmu Manzon Allah ya dubi Ashabus-Suffa, ya yi tunanin yadda suke cikin matuƙar talauci. Duk da suna cikin wannan hali, suna ibada cikin kwanciyar zuciya da haske. Shugabanmu Annabi ya ji ƙansu, ya ce musu: “Ya Ashabus-Suffa! Bushara gare ku! Idan daga al’ummata wani ya rage da ya yarda da wannan hali mai tsanani da kuke ciki, to lalle shi daga abokaina yake.”
“Idan kun yi kira zuwa ga salla da azan, sukan riƙe ta abin wasa da ba’a. Wannan kuwa saboda su mutane ne da ba su hankalta” Ma’ida: 58
Habibi Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam), kafin kowane abu yakan biya buƙatun waɗannan zaɓaɓɓun Sahabbansa, sannan ya yi ƙoƙarin biyan na Ahlul-Baitinsa. Abu Huraira ya ba da labari kamar haka: “Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda babu abin bauta sai Shi, wani lokaci nakan jingina cikina da ƙasa saboda yunwa, wani lokaci kuma in ɗauki dutse daga ƙasa in danne shi a cikina. Wata rana kuma ina cikin irin wannan hali. A ranar na zauna a kan hanyar da Manzon Allah yake bi zuwa masallaci. A lokacin adon duniya da Lahira, wanda aka aiko rahama ga talikai, ya zo wurina yana watsa nuri. Ya fahimci halina, ya yi murmushi, ya ce: ‘Ya Abu Huraira!’ Da na ce: ‘Raina fansarka, na’am, ya Manzon Allah!’, ya ce: ‘Zo tare da ni.’ Nan take na bi bayansa. Ya shiga gidansa na ni’ima. A gidan akwai ƙoƙon madara guda. Ya ce: ‘Je ka wurin Ahlus-Suffa. Ka kira su zuwa wurina.’ Yayin da nake tafiya don in kira su, ina cewa a raina: ‘Yaya ƙoƙon madara guda zai ishi dukkan Ahlus-Suffa? Ko wani kurɓi zai kai gare ni?..’ Na kira su, muka zo gidan ni’ima, muka nemi izini muka shiga ciki, bayan mun zauna a wuraren da suka dace, Shugabanmu Manzon Allah ya ce: ‘Ya Abu Huraira! Ɗauki wannan ƙoƙon madara ka ba su!’ Na ɗauki ƙoƙon, na fara ba abokaina bi da bi. Kowannensu yakan karɓi ƙoƙon, ya sha har ya ƙoshi, ya mayar mini. Duk lokacin da na karɓa daga wurin kowannensu, nakan ga ƙoƙon bai ragu ko kaɗan ba, yana nan cike da madara kamar da. Ta haka na ba dukkan abokaina da suka zo. Dukkansu suka sha suka ƙoshi. Sannan Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ɗauki ƙoƙon, ya yi mini murmushi, ya ce: ‘Ya Abu Huraira! Waɗanda ba su sha madara ba sun rage ni da kai kawai. Zo kai ma ka zauna, ka sha!’ Na zauna na sha. Ya ce: ‘Ka sake sha!’, na sha. Shugabanmu ya ce sau da yawa: ‘Sha!’ Ni ma kowane lokaci na sha. A ƙarshe na ce: ‘Uwata da ubana fansarka, ya Manzon Allah! Yanzu ba zan iya sha ba. Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda Ya aiko ka da addinin gaskiya, na ƙoshi sosai.’ Ya ce: ‘To, ba ni ƙoƙon.’ Na ba shi. Bayan ya yi wa Allahu Ta’ala godiya da yabo, ya yi basmala, ya sha madarar.”
Sahabban Madina suna ƙaunar waɗannan fitattun Sahabbai, waɗanda suke koyon ilimi a masallaci ba tare da sun rasa ko majalisi ɗaya na Shugabanmu Manzon Allah ba, ƙauna irin wadda ba a taɓa ganin irinta ba. Wata yamma, wani Sahabi daga Suffa, wanda ya rasa ƙarfi saboda yunwa, ya zo gaban Shugabanmu Manzon Allah mai daraja, ya bayyana halinsa. Shugabanmu Annabi ya tambaya a gidansa na ni’ima ko akwai wani abin ci. Da ya sami amsar: “A yanzu babu wani abin ci a gida sai ruwa”, ya ce wa Sahabbansa da suke wurin: “Wa zai ɗauki wannan mayunwaci baƙo?” Wani mutumin Madina daga Sahabbai masu girma ya riga kowa, ya ce: “Uwata da ubana fansarka, ya Manzon Allah! Ni zan ɗauke shi baƙo.” Ya tafi gidansa da baƙonsa, ya ce wa matarsa: “Ki shirya wani abu da za a karɓi baƙon Shugabanmu Manzon Allah da shi.” Matarsa ta amsa: “A yanzu babu komai a gidanmu sai abincin yara.” Sahabin ya ce: “Ki fara sa yaran barci. Sannan ki kawo abincin nan”, ya ɗauki abincin da zai ishi mutum ɗaya kawai, ya shiga ɗakin da baƙon yake. Ya ajiye abincin, ya gayyace shi ya ci. Bayan sun fara cin abinci tare, ya tashi, ya yi kamar yana gyara fitilar, ya kashe ta. Ya sake zama a kan abincin cikin duhu. Yana motsi kamar yana ci, ya jira baƙon ya ƙoshi. Bayan baƙon ya ƙoshi, ya ɗauke abincin. A wannan dare shi da ƴaƴansa suka kwana da yunwa har safe. Da safe, da suka je gaban Shugabanmu Annabi mai daraja, ya ce: “Allahu Ta’ala Ya yarda da aikinku na wannan dare.” Sai Allahu Ta’ala Ya aiko aya ta 9 mai girma ta Suratul Hashr, Ya ce, a ma’ana: “Su (Ansar) suna fifita (Muhajirun) a kan kansu, ko da suna cikin talauci da buƙata.”
Layin waƙa:
Komai ya faru, maganar Masoyi ta fi komai daɗi!
Majalisin Sarkin Zukata
Abin Alfaharin Halittu (sallallahu alaihi wa sallam), domin ya tarbiyyantar da Sahabbansa masu girma, ya kammala su, yakan yi majalisai marasa misali a Masallacin Annabi, yana gudanar da faidi da albarkokin da Allahu Ta’ala Ya ba shi zuwa zukatansu. Waɗanda suka sami darajar halartar majalisin Shugabanmu Annabi sukan ji babban canji a zukatansu tun a majalisi na farko, su sami ma’arifa ta Allah maɗaukakiya ƙwarai. Da albarkar waɗannan majalisai Sahabbai masu girma sukan kai ga ƙaunar ƙaunataccen Annabinmu, da farko, sannan dukkan ƴan’uwansu Sahabbai fiye da rayukansu. Allahu Ta’ala Ya yabe su a cikin ayoyi masu girma. Su, a gaban Shugabanmu Manzon Allah mai daraja, sukan zauna da ladabi ƙwarai da kulawa sosai, kamar tsuntsu ya sauka a kawunansu, idan sun motsa zai tashi. Ta haka Sahabbai masu girma suka zama mafifita kuma mafi falalar halittu bayan annabawa da manyan mala’iku. Shugabanmu Manzon Allah yana bayyana wa Sahabbansa umarnan addininmu da hane-hanensa dalla-dalla, yana koya musu: sharuɗɗan imani da na Musulunci; dukkan hukunce-hukuncen salla, azumi, hajji da zakka; tafsirin ayoyi masu girma; abinci da tufafi na haram da na halal; rantsuwa, bakance11 da kaffarori; ilimin ciniki; ladubban ci da sha, sa tufafi, ganawa da magana, gaisuwa; alaƙar maƙwabtaka, dangantaka da abota; hukunce-hukuncen aure, ciyarwa (nafaƙa), gado da wasiyya; ƙararraki, ukubobi, yarjejeniyoyi da haɗin gwiwa; ilimin lafiya da kiwon lafiya; yaƙi da maƙiyi, dokokin yaƙi… a taƙaice, dukkan ilimin da ya shafi addinin Musulunci na Lahira da na duniya, tun daga farko har ƙarshe, ta yadda kowa zai fahimta, al’amarin da ya ɗauka muhimmi kuma yakan maimaita shi sau uku.12 Ilimin da ya shafi mata kuwa yakan koyar da shi ta hannun matansa masu albarka.
Hadisin Jibrilu mai daraja
Jarumin limamin Musulmi, ɗaya daga cikin manyan Sahabbai masu girma, wanda ya shahara da faɗar gaskiya koyaushe, ƙaunataccen babbanmu Umar ɗan Khaɗɗab radiyallahu anhu yana cewa:
– Wata rana ce irin haka: wasu daga cikinmu Sahabbai masu girma muna gaban Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), muna hidimarsa. Wannan rana, wannan sa’a, rana ce mai daraja, mai ƙima ƙwarai, wadda ba a samunta ko kaɗan. A ranar ya rabu gare mu mu sami darajar zama a majalisin Manzon Allah, kusa da shi, mu ga fuskarsa kyakkyawa, wadda take abincin ruhohi, take ba rayuka daɗi da walwala. (Domin ya bayyana darajar wannan rana da ƙimarta, ya ce: “Wata rana ce irin haka…” Shin za a iya samun lokaci mai daraja da ƙima kamar ranar da ya rabu a ga Jibrilu alaihis-salam a surar mutum, a ji muryarsa, a ji ilimin da bayi suke buƙata, mai kyau ƙwarai kuma a sarari, daga bakin Manzon Allah mai albarka?)
“Ya Ashabus-Suffa! Bushara gare ku! Idan daga al’ummata wani ya rage da ya yarda da wannan hali mai tsanani da kuke ciki, to lalle shi daga abokaina yake” Hadisi mai daraja
A lokacin wani mutum ya zo wurinmu kamar fitowar wata. Tufafinsa fari ƙwarai, gashinsa baƙi ƙwarai. A jikinsa ba a ganin alamomin tafiya irin su ƙura, ƙasa, gumi. Babu ɗaya daga cikinmu, Sahabban Manzon Allah, da ya san shi. Wato ba daga cikin mutanen da muka sani ba ne. Ya zauna a gaban Manzon Allah. Ya kusanta gwiwoyinsa da gwiwoyinsa masu albarka. (Wannan da ya zo Jibrilu ne. Ya shiga surar mutum. Zaman Jibrilu alaihis-salam haka, domin ya sanar da wani abu mai muhimmanci ne. Wato yana nuna cewa jin kunya don koyon ilimin addini ba daidai ba ne, kuma girman kai da taƙama ba su dace da malami ba. Da wannan hali nasa Jibrilu alaihis-salam yana bayyana wa Sahabbai masu girma cewa dole ne kowa ya tambayi malamai abin da yake son ya koya a addini a sake, ba tare da jin kunya ba. Domin jin kunya wajen koyon addini, da jin nauyi wajen biyan haƙƙin Allahu Ta’ala da koyarwa da koyo, ba daidai ba ne.)
Wannan mutum mai daraja ya ɗora hannuwansa a kan gwiwoyin Manzo Mafi Daraja masu albarka, ya ce: “Ya Manzon Allah! Ka bayyana mini Musulunci, zama Musulmi.”
Manzo Mafi Daraja ya ce: “Na farko daga sharuɗɗan Musulunci shi ne faɗar kalmar shahada. (Faɗar kalmar shahada shi ne a ce “Ash-hadu an la ilaha illallah wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu”. Wato mutum mai hankali, baligi kuma mai iya magana ya ce: “A ƙasa da a sama babu wani abu, babu wani mutum da ya cancanci a bauta masa, a yi masa ibada, in ba Shi ba.
Abin bauta na gaskiya Allahu Ta’ala ne kaɗai. Shi Wajibul-wujud ne (Wanda samuwarSa wajibi ce). Kowace ɗaukaka tana gare Shi. Babu wani aibi a gare Shi. SunanSa Allah ne”, kuma ya yi imani da wannan da zuciyarsa tabbatacce. Haka kuma ya ce: “Wancan maɗaukakin mutum mai suna Muhammadu ɗan Abdullahi, daga zuriyar Hashim, mai fuska mai launin fure, fari-ja, mai haske, mai kyan gani, mai baƙaƙen gira da baƙaƙen idanu, mai buɗaɗɗen goshi mai albarka, mai kyawawan ɗabi’u, wanda inuwarsa ba ta faɗuwa ƙasa, mai daɗin magana, wanda ake kira Balarabe saboda an haife shi a Makka a Ƙasar Larabawa – bawan Allahu Ta’ala ne kuma manzonSa, wato annabinSa.”)
Sannan yin salla idan lokacinta ya yi. Bayar da zakkar dukiya. Yin azumi kowace rana a watan Ramadan mai daraja. Wanda yake da iko ya yi hajji sau ɗaya a rayuwarsa.”
Da mutumin nan ya ji waɗannan amsoshi daga Manzon Allah, ya ce: “Gaskiya ka faɗa, ya Manzon Allah!” Mu masu saurare muka yi mamakin wannan maganarsa, muna cewa: “Shi yake tambaya, shi kuma yake tabbatarwa!”
Wannan mutum ya sake cewa: “Ya Manzon Allah! Ka sanar da ni mene ne imani ma.” (A wannan hadisi mai daraja bai kamata a yi tunanin ma’anar imani ta luga ba. Domin ma’anarsa ta luga tabbatarwa ce da gaskatawa, kuma a cikin jahilan Larabawa babu wanda bai san wannan ma’ana ba. Balle kuma Sahabbai masu girma (radiyallahu ta’ala anhum ajma’in) su kasance ba su sani ba. Jibrilu alaihis-salam yana son ya koya wa Sahabbai masu girma ma’anar imani. A nan ana tambayar mene ne ake kira imani a Musulunci.) Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) kuwa ya sanar cewa imani shi ne gaskata abubuwa shida sanannu, kamar haka: “Da farko, yin imani da Allahu Ta’ala, da mala’ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa, da Ranar Lahira, da ƙaddara, da cewa alheri da sharri daga Allahu Ta’ala suke.” Mutumin nan ya sake tabbatarwa, ya ce: “Gaskiya ka faɗa.”
Sannan ya sake cewa: “Ya Manzon Allah! Ka sanar da ni mene ne ihsani ma.” Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Shi ne ka bauta wa Allahu Ta’ala kamar kana ganinSa. Domin ko da yake kai ba ka ganinSa, Shi babu shakka Yana ganinka.” Mutumin nan ya sake cewa: “Ya Manzon Allah! Ka ba ni labarin Ƙiyama!” Manzo alaihis-salam ya ce: “A wannan al’amari wanda ake tambaya bai fi mai tambaya sani ba.” Mutumin nan ya sake cewa: “To, ka sanar da alamominta.” Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Baiwa ta haifi uwargijiyarta, da kuma ka ga makiyaya marasa takalma, tsirara, talakawa (sun wadata) suna gasa da juna wajen gina dogayen gine-gine.” Bayan haka ya juya ya tafi. Manzon Allah ya juya gare ni, ya tambaya: “Ya Umar! Ka san wane ne mai tambayar nan?” Na ce: “Allahu Ta’ala da ManzonSa ne suka fi sani.” Sai Manzon Allah ya ce: “Jibrilu ne. Ya zo ne don ya koya muku addininku.”13 Shugabanmu Annabi yakan yi wa Sahabbansa bayani gwargwadon darajarsu a addini, ta yadda za su fahimta.
Sayyidina Umar, ɗaya daga cikin mafi girman Sahabbai masu girma, wata rana yayin da yake tafiya masallaci, ya ga Shugabanmu Manzon Allah yana bayyana wa Abubakar as-Siddiƙ wani abu. Ya je wurinsu ya saurara. Wasu ma sun ga haka, amma suka ji nauyin zuwa su saurara. Washegari, da suka ga Sayyidina Umar, suka ce: “Ya Umar! Jiya Manzon Allah yana bayyana muku wani abu. Faɗa mana, mu ma mu koya.” Domin Shugabanmu Manzon Allah koyaushe yana cewa: “Abin da kuka ji daga gare ni, ku bayyana wa ƴan’uwanku na addini ma! Ku sanar da juna!” Sayyidina Umar ya ce: “Jiya Sayyidina Abubakar ya tambayi ma’anar wata aya mai girma daga Alƙur’ani mai girma da bai fahimta ba, Manzon Allah yana bayyana masa. Na saurara na tsawon sa’a guda, ban fahimci komai ba.” Domin yana bayyana masa ne gwargwadon maɗaukakiyar darajar Sayyidina Abubakar. Sayyidina Umar ya ɗaukaka ƙwarai, har Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ni ne na ƙarshen annabawa. Bayana ba wani annabi da zai zo. Da wani annabi zai zo bayana, da Umar ne zai zama annabi.” Duk da ya ɗaukaka haka, kuma ya san harshen Larabci, harshen uwarsa, sosai, bai fahimci tafsirin Alƙur’ani mai girma da aka bayyana wa Sayyidina Abubakar ba. Darajar Abubakar ta fi tasa ɗaukaka nesa ba kusa ba. Sayyidina Abubakar, har ma Jibrilu alaihis-salam, sukan tambayi Manzon Allah ma’anar Alƙur’ani mai girma da asirransa. Manzon Allah ya sanar da Sahabbansa tafsirin Alƙur’ani mai girma duka.
Ƙaunataccen Annabinmu, kamar yadda yake koya wa Sahabbansa addini, yana duba ƙararraki, yana sauraron shaidu, yana warware saɓani mafi wuya da yanke hukunci a kansu; yana matuƙar ƙoƙari domin ya gabatar da Musulunci ya yaɗa shi, ya ƙara ceto wani mutum ɗaya daga wutar Jahannama; yana zama abin koyi ga mutane da halinsa da ayyukansa; yana kuma sa a ɗauki matakan da suka dace domin a kare muminai daga sharrin mushrikai.
“Ya Umar! Ka san wane ne mai tambayar nan? Jibrilu ne. Ya zo ne don ya koya muku addininku” Hadisi mai daraja
Ya kyau wanda yake nurin idanun waliyyai,
taimako, ya ma’adanin nurin Allah!
Ƙurar ƙafarka kwalli ce ga idanun asfiya,
taimako, ya ma’adanin nurin Allah!
Ba tare da kai ba babu wanda zai kai ga Gaskiya,
da faidin falalarka mutum yakan zama karɓaɓɓe,
kai ne “rahama ga talikai”, ya Manzo,
taimako, ya ma’adanin nurin Allah!
Na yi laifuffuka da zunubai marasa iyaka,
na zama abokin mabiya son zuciya,
ka yi ceto a gafarta zunubaina, ya Mai karamci,
taimako, ya ma’adanin nurin Allah!
Ya ma’adanin karamci, Manzon Allah Mai girma,
wannan Selîmî cike da kurakurai, mafi ƙanƙantar bayinka,
yana neman mafaka a ƙofarka, yana roƙon kyauta,
taimako, ya ma’adanin nurin Allah!
Yavuz Sultan Selim (Selîmî)
