MUBAYA’O’IN AƘABA
Mubaya’ar Aƙaba ta farko
A shekara ta goma sha ɗaya ta bi’isa, a watan Zulhijja, As’ad ɗan Zurara da abokansa goma sha ɗaya suka sake zuwa Makka a lokacin aikin hajji. Cif shekara guda ta wuce tun ganawarsu ta baya da Shugaban Talikai. A waccan shekara mushrikai suna cutar da Musulmi, suna azabtar da su fiye da kowace shekara da ta gabata. Suna bibiyar Shugabanmu Manzon Allah ba fasawa, suna azabtar da duk wanda ya yi magana da shi. Da mutanen Madina suka sami labarin haka, suka ɗauki alkawari da Annabinmu cewa za su gana da shi a Aƙaba cikin dare. Da dare ya yi, suka haɗu. Suka bayyana masa biyayyarsu, suka yi alkawarin za su miƙa wuya ga dukkan umarnansa da abubuwan da yake so, suka yi masa mubaya’a (bai’a). A wannan yarjejeniya suka ɗauki alkawari “ba za su yi shirka da Allahu Ta’ala ba, ba za su yi zina ba, ba za su yi sata ba, za su nisanci ƙage, ba za su kashe ƴaƴansu ba saboda tsoron kunya ko tsoron rashin arziki”.1
Ƙaunataccen Annabinmu ya sanya waɗannan mutum 12 – biyu daga cikinsu na ƙabilar Aus ne, sauran kuwa na ƙabilar Khazraj – wakilai ga ƙabilunsu. Su ne za su bayyana wa ƙabilunsu Musulunci, su zama masu lamuni a gaban Shugabanmu Manzon Allah a madadinsu. As’ad ɗan Zurara kuwa aka naɗa shi wakili a madadin dukkansu. Mutum biyar da suka halarci ganawar Aƙaba ta bara da kuma bakwai da suka karɓi Musulunci sababbi su ne: daga ƴaƴan Malik ɗan Najjar, As’ad ɗan Zurara, Auf ɗan Haris da Mu’az ɗan Haris; daga ƴaƴan Zuraiƙ ɗan Amir, Rafi’ ɗan Malik da Zakwan ɗan Abdu Ƙais; daga ƴaƴan Ghanm ɗan Auf, Ubada ɗan Samit; daga ƴaƴan Ghusaina, Yazid ɗan Sa’alaba; daga ƴaƴan Ajlan ɗan Zaid, Abbas ɗan Ubada; daga ƴaƴan Haram ɗan Ka’ab, Uƙba ɗan Amir; daga ƴaƴan Sawad ɗan Ghanm, Ƙuɗba ɗan Amir; daga ƴaƴan Abdulashhal ɗan Jusham, Abul-Haisam Malik ɗan Tayyihan; daga ƴaƴan Amr ɗan Auf kuma, Uwaim ɗan Sa’ida.
Ranar da ta fito a Madina
Bayan mubaya’ar (yarjejeniyar) Aƙaba ta farko, Sayyidina As’ad ɗan Zurara da abokansa, da suka koma Madina, suka riƙa bayyana wa ƙabilunsu Musulunci dare da rana, suna kiransu zuwa ga addinin gaskiya. Sakamakon wannan kira, Musulunci ya fara yaɗuwa a Madina da sauri. Har ƙabilun Aus da Khazraj, waɗanda a da suke maƙiyan juna, suka haɗu wuri ɗaya, suka nemi malami daga wurin Shugabanmu Manzon Allah domin su ƙara koyon Musulunci yadda ya kamata. Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) kuwa ya aiki Sayyidina Mus’ab ɗan Umair, ɗaya daga cikin Sahabbansa na Makka, zuwa Madina a matsayin malami, domin ya koyar da Alƙur’ani mai girma da Musulunci. Sayyidina Mus’ab ya sauka a gidan Sayyidina As’ad. Tare suka riƙa zagaya gida-gida, suna sanar da kowa Musulunci. Suka nemi mutane su ƙaunaci Manzon Allah, su yi alkawarin za su yi ƙoƙari da rai da dukiya domin su kare shi daga dukkan maƙiyansa. Ta haka suka shirya su don mubaya’ar da za a yi wa Manzon Allah. Shugaban ƙabilar Sayyidina As’ad ɗan Zurara kuwa Sa’ad ɗan Mu’az ne, kuma su dangin juna ne. Da yake a wancan lokaci al’ada ce a wurin Larabawa a guji wulaƙanta dangi, Sa’ad ɗan Mu’az, wanda bai riga ya yi imani ba, bai je gidan Sayyidina As’ad ɗan Zurara don ya hana wannan al’amari ba. Shi a matsayinsa na shugaban ƙabila, ba ya son ya sa hannu a ciki da kansa. Saboda haka ya ce wa Usaid ɗan Hudair, ɗaya daga cikin manyan ƙabilarsa: “Je ka unguwarmu, ka ga wannan mutumin da ya zo, ka yi abin da za ka yi. Da ba don As’ad ɗan ƴar’uwar uwata ne ba, da ban danƙa maka wannan al’amari ba.”
Sai Usaid ɗan Hudair ya ɗauki mashinsa, ya tafi gidan da Sayyidina Mus’ab ɗan Umair yake. Da ya isa can, ya fara magana cikin fushi: “Don me kuka zo mana? Kuna ruɗin mutane! Idan ba kwa son ku rasa rayukanku, ku bar nan yanzu-yanzu!” Da Mus’ab ɗan Umair ya ga yadda yake cikin fushi, ya ba shi amsa cikin tausasawa da ladabi ƙwarai, ya ce: “Da farko ka ɗan zauna, ka saurari maganarmu! Ka fahimci manufarmu; idan ka so, ka karɓa. In ba haka ba kuwa, ka hana…” Usaid ya huce, ya ce: “Gaskiyarka”, ya kafa mashinsa a ƙasa ya zauna. Ya saurari daɗin maganar Sayyidina Mus’ab, kalmominsa da suke shiga zuciyar mutum da ayoyin Alƙur’ani mai girma da yake karantawa da kyakkyawar murya. Ya shagala, har ya ce: “Wannan abu ne mai kyau ƙwarai!” Sannan ya tambaya: “Me ya kamata a yi don shiga wannan addini?” Suka bayyana masa, sai Usaid ɗan Hudair ya faɗi kalmar shahada ya musulunta. Sayyidina Usaid, wanda farin ciki bai bar shi ya zauna a wurinsa ba, ya ce: “Bari in tafi in aiko muku da wani mutum. Idan shi ya musulunta, ba wanda zai rage daga mutanensa a Madina da bai yi imani ba…”, sai ya tashi da sauri ya tafi. Ya nufi wurin Sa’ad ɗan Mu’az kai tsaye. Da Sa’ad ɗan Mu’az ya gan shi, ya ce: “Na rantse, Usaid bai dawo da fuskar da ya tafi da ita ba.” Sannan ya tambaya: “Me ka yi, ya Usaid?” Da yake Sayyidina Usaid ɗan Hudair yana matuƙar son Sa’ad ɗan Mu’az ya musulunta, ya ce: “Na yi magana da mutumin nan (Mus’ab ɗan Umair), ban ga wani mugun abu a gare su ba. Sai dai mun ji cewa Banu Harisa, da suka yi zargin yadda As’ad, ɗan ƴar’uwar uwarka, yake ɓoye irin wannan mutum a gidansa, sun tashi don su kashe shi.” Waɗannan kalmomi suka taɓa Sa’ad ɗan Mu’az ƙwarai. Domin shekaru kaɗan da suka wuce, a wani yaƙi, sun ci Banu Harisa da yaƙi, suka tilasta musu su gudu zuwa Khaibar. Bayan shekara guda kuma suka yafe musu, suka ba su izinin komawa ƙasarsu. Duk da haka, tunanin cewa sun ɗauki irin wannan mataki ya husata Sa’ad ɗan Mu’az ƙwarai. Alhali kuwa a haƙiƙa babu irin wannan abu. Usaid ɗan Hudair ya yi wannan dabara ne domin ya hana Sa’ad ɗan Mu’az cutar da ƴar’uwar uwarsa da ɗanta As’ad ɗan Zurara, ta haka kuma Mus’ab ɗan Umair. Ta haka ya shirya masa hanyar da zai koma ɓangarensu, a ƙarshe kuma ya musulunta. Da jin waɗannan kalmomi na Usaid ɗan Hudair, Sa’ad ɗan Mu’az ya tashi wuf daga wurinsa, ya tafi wurin Sayyidina As’ad ɗan Zurara. Da ya isa can, ya ga As’ad da Mus’ab ɗan Umair zaune suna hira cikin matuƙar nutsuwa da kwanciyar hankali. Ya kusance su, ya ce: “Ya As’ad! Da ba don dangantakar da ke tsakaninmu ba, da ba za ka iya yin waɗannan abubuwa ba…” Sayyidina Mus’ab ɗan Umair ya ba da amsa ga waɗannan kalmomi, ya ce: “Ya Sa’ad! Ka ɗan dakata, ka zauna, ka saurare mu, ka fahimta… Idan maganarmu ta yi maka daɗi, to madalla; in kuwa ba ka so ba, ba za mu ƙara gabatar maka da ita ba, kai ma ka tashi ka tafi!” A gaban waɗannan kalmomi masu laushi da daɗi, Sa’ad ɗan Mu’az ya huce, ya zauna a gefe guda, ya fara sauraronsu. Da farko Sayyidina Mus’ab ɗan Umair ya bayyana wa Sa’ad ɗan Mu’az Musulunci. Ya bayyana masa tushen Musulunci. Sannan ya karanta ɗan abu daga Alƙur’ani mai girma da muryarsa mai daɗi kuma kyakkyawa. Yayin da yake karantawa, halin Sa’ad ɗan Mu’az yana canzawa, yana shagala. A gaban fasahar Alƙur’ani mai girma mara misali zuciyarsa ta yi laushi, abin ya shiga ransa ƙwarai. Ya kasa riƙe kansa, ya ce: “Me kuke yi don shiga wannan addini?” Mus’ab ɗan Umair nan take ya koya masa kalmar shahada. Shi ma ya ce “Ash-hadu an la ilaha illallah wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu”, ya musulunta. Saboda nutsuwa da farin cikin da Sa’ad ɗan Mu’az ya ji na musulunta, ya kasa zama a wurinsa. Nan take ya tafi gidansa, ya yi wankan janaba kamar yadda aka koya masa. Sannan ya nemi a tara mutanensa. Ya ɗauki Usaid ɗan Hudair tare da shi, ya zo wurin da mutane suke. Ya fuskanci ƴaƴan Abdulashhal, ya ce: “Ya ƴaƴan Abdulashhal! Wane irin mutum kuka san ni?” Suka amsa da baki ɗaya: “Kai ne shugabanmu kuma babbanmu, mu masu bin ka ne!” Da jin waɗannan kalmominsu, Sa’ad ɗan Mu’az ya ce: “To, ina sanar da ku duka: na sami darajar zama Musulmi. Ina son ku ma ku yi imani da Allahu Ta’ala da ManzonSa. Idan ba ku yi imani ba, ba zan yi magana da ɗayanku ba, ba zan gana da shi ba!..”
“To, ina sanar da ku duka: na sami darajar zama Musulmi. Ina son ku ma ku yi imani da Allahu Ta’ala da ManzonSa” Sa’ad ɗan Mu’az (radiyallahu anhu)
Sanatus-Surur (Shekarar farin ciki)
Da ƴaƴan Abdulashhal suka ji cewa shugabansu Sa’ad ɗan Mu’az ya musulunta, kuma yana kiransu zuwa ga Musulunci, nan take dukkansu suka musulunta gaba ɗaya. A ranar, har zuwa magariba, sammai na Madina suka yi ta ƙara da kalmar shahada da sautukan kabbara.2 Ba a daɗe ba bayan musuluntar ƴaƴan Abdulashhal gaba ɗaya, sai dukkan mutanen Madina da ƙabilun Aus da Khazraj suka karɓi Musulunci. Kowane gida ya haskaka da nurin Musulunci. Sa’ad ɗan Mu’az da Usaid ɗan Hudair suka farfasa dukkan gumakan ƙabilunsu. Da aka sanar da ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) wannan al’amari, ya yi farin ciki ƙwarai. Musulmin Makka suna cikin farin ciki. Saboda haka aka kira wannan shekara (621 Miladiyya) “Sanatus-Surur” (shekarar farin ciki).
As-salatu was-salamu alaika ya Rasulallah!
As-salatu was-salamu alaika ya Habiballah!
As-salatu was-salamu alaika ya Sayyidal-awwalina wal-akhirin!
Mubaya’ar Aƙaba ta biyu
A shekara ta goma sha biyu ta bi’isa, zaluncin mushrikan Makka ga Musulmi ya kai ƙololuwarsa, ya zama abin da ba a iya jurewa. A Madina kuwa, saboda hidimar As’ad ɗan Zurara da Mus’ab ɗan Umair, mutanen Aus da Khazraj suna cikin ƙauna da kwaɗayin da za su karɓi Musulmi da hannu biyu-biyu, su rungume su, su yi kowace irin sadaukarwa saboda su. Suna kwaɗayin Shugabanmu Manzon Allah ya albarkaci Madina da zuwansa da wuri-wuri; suna alkawarin ba za su yi wa dukiyoyinsu da rayukansu rowa ba a tafarkinsa. Lokacin aikin hajji ya yi. A watan Zulhijja, tare da Mus’ab ɗan Umair, Musulmi maza 73 da mata 2 daga Madina suka zo Makka. Bayan hajji, dukkansu suka sake haɗuwa da Annabinmu a Aƙaba. Wakilai 12, har da As’ad ɗan Zurara, a madadin ƙabilunsu suka roƙi Annabinmu, suka gabatar masa cewa ya yi hijira zuwa Madina. Shugabanmu Manzon Allah, bayan ya karanta musu wasu ayoyi masu girma daga Alƙur’ani mai girma, ya nemi tabbataccen alkawari daga gare su cewa za su kare shi kamar yadda suke kare rayukansu da iyalansu da ƴaƴansu, suke kula da su. Sayyidina Abbas, baffan Shugabanmu Manzon Allah, wanda bai riga ya musulunta ba, shi ma yana nan. Ya yi wa wannan jama’a da ta zo don mubaya’a jawabi kamar haka: “Ya mutanen Madina! Wannan ɗan ɗan’uwana ne. A cikin mutane shi ne wanda na fi ƙauna. Idan kuna gaskata shi, kuna imani da abin da ya zo da shi daga wurin Allah, kuma kuna son ku tafi da shi tare da ku, to dole ne ku ba ni ƙwaƙƙwaran alkawari da zai gamsar da ni. Kamar yadda kuka sani, Muhammadu alaihis-salam namu ne. Mu mun kare shi daga mutanen da ba su yi imani da shi ba. Yana rayuwa a tsakaninmu cikin kariya, da izza da daraja. Duk da haka, ya juya wa kowa baya, ya yanke shawarar ya haɗu da ku, ya tafi tare da ku. Idan kuna da ƙarfin yaƙin da zai iya tunkarar dukkan ƙabilun Larabawa in sun haɗu suka kawo muku hari, to ku shiga wannan al’amari. Wannan al’amari kuma ku tattauna shi sosai a tsakaninku, ku shawarta, kada ku rabu a kansa daga baya. Shin za ku iya cika alkawarinku, ku kare shi daga maƙiyansa? Idan za ku iya yin hakan yadda ya kamata, to madalla. Idan kuwa za ku bar shi shi kaɗai bayan ya fita daga Makka, to ku fasa tun yanzu, don ya zauna a ƙasarsa cikin kariya da darajarsa.” Wannan jawabi na Sayyidina Abbas ya ɓata wa Musulmin Madina rai. Kamar an gaya musu cewa idan sun tafi da Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) zuwa ƙasarsu, ba za su iya kare shi daga mushrikai ba, idan matsi ya kama su kuma za su yashe shi. Sayyidina As’ad ɗan Zurara, ɗaya daga cikin Sahabban Madina, ya juya ga Shugabanmu Annabi, ya ce: “Ya Manzon Allah! Idan ka yi mini izini, ina da ƴan kalmomi. Bari in gabatar maka da su.” Da Abin Alfaharin Halittu ya yi izini, Sayyidina As’ad ya ce: “Uwata da ubana fansarka, ya Manzon Allah! Kowane kira yana da hanyarsa, salonsa, mai laushi ko mai tsauri. Yanzu kana kiranmu zuwa ga wani abu da yake da wuya ƙwarai mutane su karɓe shi. Domin yana da wuya ƙwarai mutane su bar gumakan da suka daɗe suna bauta wa, su karɓi Musulunci. Duk da haka mun karɓi Musulunci da dukkan zuciyarmu. Haka kuma ka umarce mu da mu yanke alaƙa da danginmu mushrikai, mun karɓi wannan ma da ikhlasi. Ka sani cewa karɓar wannan ma yana da wuya ƙwarai. Mun karɓi maɗaukakin mutuncinka – wanda har baffanninka suka zama maƙiyansa, ba su kare shi ba – da hannu biyu-biyu, mun ɗauki wannan aiki mai daraja a matsayin wajibi kuma dole a kanmu. Dukkanmu mun yarda a kan waɗannan kalmominmu. Abin da muke faɗa da harshenmu, da zuciyarmu muke gaskata shi. Muna rantsuwa cewa za mu kare jikinka mai albarka har zuwa ɗigon jininmu na ƙarshe, kamar yadda muke kare iyalanmu da ƴaƴanmu. Idan muka warware wannan alkawarinmu, to mu shiga cikin jerin ashararai, waɗanda ba su cika alkawarin da suka yi wa Allahu Ta’ala ba. Ya Manzon Allah! Mu masu gaskiya ne a kan wannan maganarmu. Allahu Ta’ala Ya ba da nasara!” Sannan ya ci gaba da cewa: “Ya Manzon Allah! Ka karɓi tabbacin da kake so daga gare mu saboda kanka, ka sanya sharaɗin da kake so.”
Shugabanmu Annabi ya ƙarfafa musu gwiwa a kan Musulunci, ya karanta Alƙur’ani mai girma. Sannan ya ce: “Sharaɗina a kanku saboda Ubangijina shi ne ku bauta wa Allahu Ta’ala, kada ku haɗa Shi da kowane abu; sharaɗina kuma saboda kaina da Sahabbaina shi ne ku ba mu mafaka, ku taimake ni da Sahabbaina, ku kare mu daga abubuwan da kuke kare kanku, kuke tsare kanku daga gare su.”
Bara’u ɗan Ma’rur ya ce: “Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda Ya aiko ka annabi da addinin gaskiya da littafi, za mu kare ka kamar yadda muke kare iyalanmu da ƴaƴanmu, muke tsare su! Ka karɓi mubaya’armu, ya Manzon Allah!” Abbas ɗan Ubada, ɗaya daga cikin Musulmin Madina, domin ya ƙarfafa yarjejeniyar da aka yi da Shugabanmu Annabi, ya ce wa abokansa: “Ya mutanen Khazraj! Kun san dalilin da ya sa kuka karɓi Muhammadu alaihis-salam?” Suka amsa: “I.” Sai ya ce: “Kuna karɓarsa ne domin ku bi shi a lokacin zaman lafiya da na yaƙi duka. Idan za ku bar Annabinmu shi kaɗai ba tare da taimako ba a lokacin da wata ɓarna ta sami dukiyoyinku, danginku da na kusa da ku suka halaka, to ku yi haka tun yanzu. Wallahi, idan kuka yi irin wannan abu, za ku halaka a duniya da Lahira! Idan kuwa hankalinku ya tabbatar muku cewa za ku cika alkawari gare shi a kan abin da yake kira zuwa gare shi, duk da tafiyar dukiyoyinku da kashe danginku na kusa, to ku riƙe shi. Wallahi wannan shi ne alheri ga duniyarku da Lahirarku.” Sai abokansa suka ce: “Ba za mu yashe Annabinmu ba, ko da dukiyoyinmu sun lalace, ko da an kashe na kusa da mu. Ba za mu taɓa rabuwa da shi ba. Mutuwa akwai, komawa baya babu!”
“Idan muka warware wannan alkawarinmu, to mu shiga cikin jerin ashararai, waɗanda ba su cika alkawarin da suka yi wa Allahu Ta’ala ba. Ya Manzon Allah! Mu masu gaskiya ne a kan wannan maganarmu. Allahu Ta’ala Ya ba da nasara!” As’ad ɗan Zurara (radiyallahu anhu)
Sannan suka juya ga Shugabanmu Annabi, suka tambaya: “Ya Manzon Allah! Idan muka cika wannan alkawarinmu, me za mu samu?” A lokacin ƙaunataccen Annabinmu ya ce: “Yardar Allahu Ta’ala da Aljanna!” Kowannensu ya ba da alkawari a matsayin wakilin mutanensa, amintaccensu. Da farko Sayyidina As’ad ɗan Zurara ya yi musafaha, yana cewa: “Ina yin mubaya’a don in cika alkawarin da na yi wa Allahu Ta’ala da ManzonSa, in tabbatar da alkawarina na taimakonsa da raina da dukiyata.” Bayansa kowannensu ya cika mubaya’a ta haka, ya bayyana farin cikinsa da miƙa wuyansa, yana cewa: “Mun karɓi kiran Allahu Ta’ala da ManzonSa, mun ji, mun yi biyayya.” Ta haka suka sadaukar da rayukansu da dukiyoyinsu a tafarkin Manzon Allah ba tare da jinkiri ba. Mubaya’a da mata kuwa, da magana kawai aka yi ta. Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya karɓi alkawari daga gare su a kan “kada su haɗa Allahu Ta’ala da kowane abu, kada su yi sata, kada su yi ƙage, kada su yi zina, kada su kashe ƴaƴansu, kada su yi ƙarya, kada su saɓa wa ayyukan alheri…” A lokacin da mutanen Madina suke yi wa Shugabanmu Annabi mubaya’a, wata murya ta yi ihu daga tudun Aƙaba: “Ya ku da kuka sauka a Mina! Annabi da Musulmin Madina sun yi yarjejeniyar su yaƙe ku!” Annabinmu ya ce game da wannan murya: “Wannan shaiɗanin Aƙaba ne”, ga mai ihun kuma ya ce: “Ya maƙiyin Allahu Ta’ala! Kai ma zan kawo ƙarshenka!” Ga mutanen Madina da suka yi mubaya’a kuwa ya ce: “Ku koma wuraren saukarku nan take.” Abbas ɗan Ubada ya ce: “Ya Manzon Allah! Na rantse, idan ka so, gobe da safe mu tunkari kafiran da suke Mina, mu karkashe su duka da takobi.” Shugabanmu Annabi ya ji daɗi, amma ya ce: “Har yanzu ba a umarce mu da mu yi aiki irin wannan ba. A yanzu ku koma wuraren saukarku.” Bisa riwayar Imam Nasa’i daga Abdullahi ɗan Abbas, Ansar waɗanda suka halarci mubaya’ar Aƙaba, da zuwansu wurin Manzon Allah, sun zama daga Muhajirun ma.3
Itacen sarwi yana taƙama, ba ya jin roƙon kurciya,
sai dai in ruwa ya faɗi ƙafarsa ya roƙe shi.
Fure yana son ya sha jinin ɗan tsuntsun bulbul da dabara,
sai dai in ruwa ya shiga jikin reshen fure ya cece shi.
Ruwa ya nuna wa mutanen duniya tsarkakar asalinsa,
ya bi tafarkin Ahmad Mukhtar, wancan ruwa.
Shugaban ƴaƴan Adamu, tekun lu’ulu’u zaɓaɓɓu –
mu’ujizozinsa suka zama ruwa ga wutar mugaye.
Domin ya sabunta kyan lambun annabta,
da mu’ujizarsa ya fitar da ruwa daga dutse mai tauri.
Mu’ujizarsa teku ce mara iyaka a duniya,
daga gare ta ruwa ya isa har gidajen wutar kafirai.
Wanda ya ji wannan, da mamaki sai ya ciji yatsa:
a ranar tsanani, daga yatsunsa ya ba Ansar ruwa.
