Ƙaunataccen Annabina

MI’IRAJI

Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya bayyana Musulunci ga kowane mutum da kowace ƙabila da ya gani, ko masu zuwa aikin hajji ne, ko masu zuwa Makka da kasuwanni domin ciniki. Ya nemi su kare shi, su taimake shi wajen isar da Musulunci ga mutane. Amma babu wanda ya musulunta, babu kuma wanda ya kusanci ɗaukar nauyin kare shi. Bugu da ƙari, suka wulaƙanta shi, suka zalunce shi, suka azabtar da shi, suka yi masa ba’a, suka ƙaryata shi. Shugaban Talikai ya gaji ƙwarai, yana jin yunwa da ƙishirwa, yana cikin damuwa da baƙin ciki mai tsanani. Kwanakinsa suna wucewa haka, wannan hali kuma yakan ci gaba har dare ya yi nisa. Mushrikan Makka suna ta bin sa a baya; baya ga hana mutanen da suke zuwa ziyarar Ka’aba musulunta, ba su daina zaluntar Habibi Mafi Daraja ba. Yanzu babu sauran wurin da Shugabanmu Manzon Allah zai je. Ko’ina maƙiya ne. Watanni kaɗan suka wuce a Makka cikin tsananin ƙunci.

A daren 27 ga watan Rajab mai daraja, ya zo kai tsaye gidan Ummu Hani, ƴar baffansa Abu Ɗalib, da yake a unguwar Abu Ɗalib. A lokacin Ummu Hani ba ta yi imani ba tukuna. Da ta ce: “Wane ne wannan?”, Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ni ne Muhammadu, ɗan baffanki. Idan kin karɓa, na zo baƙunci.”

Ummu Hani ta ce: “Raina fansa ga baƙo mai gaskiyar magana, amintacce, mai asali, mai daraja irinka. Sai dai, da ka sanar da zuwanka tun da wuri, da na shirya wani abu. Yanzu ba ni da abin da zan ciyar da kai.” Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ba na son abinci ko abin sha. Babu ɗayansu a idona. Wuri guda na yin ibada ga Ubangijina, na roƙonSa, ya ishe ni.”

Ummu Hani ta shigar da ƙaunataccen Annabinmu ciki, ta ba shi tabarma da ƙwarya da buta. Karɓar baƙo da kyautata masa da kare shi daga maƙiyi, aiki ne mafi daraja a wurin Larabawa. Idan baƙon da yake cikin gida ya sami cuta, babban abin kunya ne ga mai gidan. Ummu Hani ta yi tunani: “Wannan yana da maƙiya da yawa a Makka. Har ma akwai masu son kashe shi. Domin in kare darajata, bari in tsare shi har safiya.” Ta ɗauki takobin ubanta, ta fara kewaya gidan. A wannan rana an cutar da Manzon Allah ƙwarai. Ya yi alwala, ya fara roƙon Ubangijinsa, yana neman gafara, yana addu’a domin bayi su yi imani, su sami farin ciki. Ya gaji ƙwarai, yana jin yunwa, yana baƙin ciki. Da ya kwanta a kan tabarmar, nan take barci ya ɗauke shi.

A lokacin nan Allahu Ta’ala Ya ce wa Jibrilu alaihis-salam: “Na sa ƙaunataccen AnnabiNa cikin baƙin ciki ƙwarai. Na cutar da jikinsa mai albarka, zuciyarsa mai taushi, sosai. A wannan hali ma, har yanzu Ni yake roƙo. Ba ya tunanin kome sai Ni. Je ka, ka kawo MasoyiNa! Ka nuna masa AljannaTa da WutaTa. Ya ga ni’imomin da Na shirya masa da masu ƙaunarsa. Ya ga azabobin da Na shirya wa waɗanda ba su yi imani da shi ba, waɗanda suke cutar da shi da maganganunsu, rubuce-rubucensu da ayyukansu. Ni da kaiNa Zan ta’azantar da shi. Ni da kaiNa Zan ɗaure raunukan zuciyarsa mai taushi.”

Da Jibrilu alaihis-salam ya zo wurin Manzon Allah, ya same shi yana barci mai daɗi.

Bai yi ƙarfin halin da zai tashe shi ba. Yana cikin siffar mutum. Ya sumbaci tafin ƙafarsa mai albarka. Tun da Jibrilu ba shi da zuciya, ba shi da jini, leɓunansa masu sanyi suka tashe Manzon Allah. Annabinmu ya gane Jibrilu alaihis-salam nan take, kuma, saboda tsananin tsoron kada Ubangijinsa Ya yi fushi da shi, ya ce: “Ya ɗan’uwana Jibrilu! Don me ka zo a irin wannan lokaci da ba a saba ba? Ko na yi wani kuskure ne? Na ɓata wa Ubangijina rai ne? Ko kuwa labari mai raɗaɗi ka kawo mini?”

“Ba na son abinci ko abin sha. Babu ɗayansu a idona. Wuri guda na yin ibada ga Ubangijina, na roƙonSa, ya ishe ni” Hadisi mai daraja

Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya mafi ɗaukakar dukkan halittu! Ya masoyin Mahalicci, ya shugaban annabawa, Annabi mai daraja kuma mai girma, mabuɓɓugar alherai, ma’adanin ɗaukaka! Ubangijinka Yana yi maka sallama, Yana kiranka zuwa gare Shi. Don Allah, tashi mu tafi.” Ƙaunataccen Annabinmu ya yi alwala. Jibrilu alaihis-salam ya sa rawani na nuri a kan kai mai albarka na Shugabanmu Manzon Allah, ya sa masa tufafi na nuri, ya ɗaura masa ɗamara ta yaƙutu a kugunsa mai albarka. Ya sa a hannunsa mai albarka sandar zumurrudu da aka ƙawata da lu’ulu’u ɗari huɗu. Kowane lu’ulu’u yana haskakawa kamar tauraruwar Gamzaki. Ya sa masa takalma na koren zumurrudu a ƙafafunsa masu albarka.

Sannan suka kama hannun juna, suka zo Ka’aba. A nan Jibrilu alaihis-salam ya tsaga ƙirji mai albarka na ƙaunataccen Annabinmu. Ya fitar da zuciyarsa. Ya wanke ta da ruwan Zamzam. Sannan ya kawo wani kwano cike da hikima da imani, ya zuba a cikinta, ya rufe ƙirjinsa.

Alƙiblarmu ta farko, Masallacin Aƙsa / Ƙudus

Sannan Jibrilu alaihis-salam ya nuna wata fararriyar dabba mai suna Buraƙ, da ya kawo daga Aljanna, ya ce: “Ya Manzon Allah! Hau wannan! Dukkan mala’iku suna jiranka a hanya.” A lokacin nan wani baƙin ciki ya sauka wa Shugabanmu Annabi, ya nutse cikin tunani. A wannan lokaci Allahu Ta’ala Ya yi magana da Jibrilu alaihis-salam: “Ya Jibrilu! Ka tambaya! Don me MasoyiNa yake baƙin ciki?”, sai Shugabanmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya amsa: “Na ga irin wannan daraja da karimci masu yawa. Sai ya zo mini a rai: yaya halin al’ummata mai rauni zai kasance a Ranar Ƙiyama? Shekara dubu hamsin a tsaye a filin Arasat, yaya za su ɗauki nauyin zunubansu masu yawa haka, yaya kuma za su ƙetare Siraɗi, wanda tafiyarsa shekara dubu talatin ce?” Umarnin Allah ya zo: “Ya MasoyiNa! Ka kwantar da hankalinka. Ga al’ummarka Zan mayar da lokacin shekara dubu hamsin kamar ƙiftawar ido. Kada ka yi baƙin ciki.”

Shugabanmu Annabi ya hau Buraƙ. Buraƙ yana tafiya da sauri ƙwarai, da taki guda yakan isa bayan inda ido yake gani. A lokacin tafiyar, Jibrilu alaihis-salam ya ce wa ƙaunataccen Annabinmu ya sauka ya yi salla a wasu wuraren sauka. Shugaban Talikai, bisa haka, ya sauka sau uku cif, ya yi salla. Jibrilu alaihis-salam kuma ya tambaye shi ko ya san wuraren da ya yi salla. Ya ba da amsar da kansa: ya sanar cewa wurin da ya fara sauka Madina ne, kuma zai yi hijira zuwa wannan birni. Game da sauran wuraren kuma ya sanar, bi da bi, cewa na biyu Ɗur-i Sina ne, inda Musa alaihis-salam ya yi magana da Allahu Ta’ala ba tare da wata fuska ba, ta hanyar da ba a sani ba; na ƙarshe kuma Baitu Lahm ne, inda aka haifi Isa alaihis-salam, a nan ya yi salla. Sannan suka zo Masallacin Aƙsa da yake a Ƙudus.

A Masallacin Aƙsa, Jibrilu alaihis-salam ya huda wani dutse da yatsansa, ya ɗaure Buraƙ. Rayukan wasu annabawan da suka gabata sun taru a can a siffar mutane. Domin sallar jam’i, aka faɗa wa annabawa Adamu, Nuhu da Ibrahim (alaihimus-salam) bi da bi su yi limanci. Suka nemi gafara, ba su karɓa ba. Jibrilu ya ce: “Da kake nan, babu wanda zai iya zama limami”, ya gabatar da Habibullah.

Shugabanmu Annabi ya yi wa annabawa limanci, ya yi musu salla raka’a biyu. Al’amarin da ya faru bayan haka ya ba da labarinsa kamar haka: “Jibrilu (alaihis-salam) ya kawo mini kwano ɗaya na giyar Aljanna, kwano ɗaya kuma na madara. Na ɗauki madarar. Jibrilu (alaihis-salam) ya ce mini: ‘Ka zaɓi fiɗra (farin cikin duniya da Lahira).’ Daga baya kuma suka miƙa mini ƙoƙuna biyu. Ɗaya ruwa ne, ɗaya zuma, na sha daga dukkansu biyu. Jibrilu ya ce: ‘Zuma alama ce ta cewa al’ummarka za ta ci gaba har zuwa Ƙiyama, ruwa kuma alama ce ta cewa al’ummarka za ta tsarkaka daga zunubanta.’ Sannan muka hau sama tare. Jibrilu (alaihis-salam) ya ƙwanƙwasa ƙofa. Suka ce: ‘Wane ne kai?’ ‘Ni ne Jibrilu.’ ‘To wane ne wanda yake tare da kai?’ ‘Shi ne Muhammadu (alaihis-salam).’ ’An aiko masa (da wahayi da kiran Mi’iraji domin hawa sama)?’ ‘E, an aiko’, ya ce. ‘Maraba ga wanda ya zo! Wannan mai zuwa, mai kyawun matafiyi ne!’ suka ce, nan take ƙofar ta buɗe, na ga kaina a gaban Adamu (alaihis-salam). Ya ce mini ‘Maraba’, ya yi mini addu’a… A dama da hagun Adamu alaihis-salam rayukan wasu mutane suna tsaye kamar inuwowi. Duk lokacin da Adamu alaihis-salam ya dubi damansa yakan yi murmushi, duk lokacin da ya dubi hagunsa kuma yakan yi kuka. Jibrilu alaihis-salam ya ce: ‘Ya Manzon Allah, waɗannan inuwowi kuma rayukan ƴaƴan Adamu ne daga zuriyarsa. Waɗannan da suke dama ƴan Aljanna ne, waɗanda suke hagu kuma ƴan Wuta ne! Idan ya dubi ɓangaren dama yakan yi murmushi, idan ya dubi ɓangaren hagu kuma yakan yi kuka!’

“Ya mafi ɗaukakar dukkan halittu! Ya masoyin Mahalicci, ya shugaban annabawa, Annabi mai daraja kuma mai girma, mabuɓɓugar alherai, ma’adanin ɗaukaka! Ubangijinka Yana yi maka sallama, Yana kiranka zuwa gare Shi. Don Allah, tashi mu tafi” Jibrilu alaihis-salam

A nan na ga mala’iku masu yawa. Dukkansu suna tsaye a ƙiyam, cikin tawali’u da ƙasƙantar da kai, suna shagaltuwa da zikirin ‘Subbuhun ƙuddusun rabbul-mala’ikati war-ruh’. Na tambayi Jibrilu: ‘Ibadar waɗannan mala’iku wannan ce?’ ‘E. Waɗannan, tun da aka halicce su har zuwa Ƙiyama, suna tsaye a ƙiyam. Ka roƙi Allah Maɗaukaki Ya ba al’ummarka wannan ibada.’ Na roƙi Allah Maɗaukaki. Ya karɓi addu’ata. Ƙiyam da yake cikin salla shi ne.

(A can) na wuce ta wurin wata jama’a. Mala’iku suna murƙushe kawunan waɗannan mutane, sai su sake komawa yadda suke. Su sake dukansu, su sake zama kamar yadda suke. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Masu barin sallar Juma’a da sallar jam’i ne. Waɗanda ba sa cika ruku’u da sujada ne.’

Na ga wata jama’a. Suna jin yunwa, tsirara suke. Zabaniya suna kiwonsu a cikin Wuta kamar dabbobi. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Waɗanda ba sa jin ƙan talakawa, waɗanda ba sa bayar da zakka ne.’

Na wuce ta wurin wata jama’a. An sa musu abinci masu daɗi a gabansu. A gefe guda kuma akwai mushe. Sun bar waɗancan abinci masu daɗi, mushen suke ci. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Waɗannan maza da mata ne da suka bar halal, suka karkata zuwa ga haram. Mutane ne da suke da dukiyar halal, amma suna cin haram.’

Na ga (wasu) mutane da ba su da sauran ƙarfin motsi saboda yawan kayan da suke a bayansu. A wannan hali suna kiran mutane, suna neman a ƙara musu kaya a kai. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Waɗannan mutane masu cin amana ne. Duk da cewa sun ci haƙƙin mutane, har yanzu suna zalunci.’

Mun wuce ta wurin wasu mutane da suke yanka namansu suna ci. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Jibrilu (alaihis-salam) ya ce: ‘Waɗannan masu gulma da masu kai magana ne.’

Na ga wasu mutane fuskokinsu baƙaƙe, idanunsu shuɗaye, leɓunansu na sama sun kai goshinsu, leɓunansu na ƙasa sun lanƙwashe har ƙafafunsu, jini da mugunya suna zuba daga bakunansu. Ana shayar da su da ƙoƙunan wuta jini mai guba da mugunya da suke gudana daga Wuta; suna kuka kamar jakuna. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Waɗannan masu shan giya ne.’

Mun haɗu da wasu mutane: ana azabtar da su, an ja harsunansu daga bayan kawunansu, an canza siffofinsu zuwa siffar alade (khinzir). Jibrilu (alaihis-salam) ya ce: ‘Waɗannan masu shaidar zur ne.’

Mun haɗu da wasu mutane kuma. Cikunansu sun kumbura sun lanƙwashe ƙasa, launinsu ya koma shuɗi, hannuwansu da ƙafafunsu a ɗaure, ba sa iya tashi daga wurarensu. Na tambayi Jibrilu a kansu. Ya ce: ‘Waɗannan masu cin riba ne.’1

Mun haɗu da wasu mata. Fuskokinsu baƙaƙe, idanunsu shuɗaye. An sa musu tufafi na wuta. Mala’iku suna dukansu da kulaken wuta. Suna ihu kamar karnuka da aladu. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Jibrilu ya ce: ‘Waɗannan mata masu zina ne, da masu cutar da mazajensu.’

Na ga wata jama’a. Suna da yawa ƙwarai. An tsare su a cikin kwaruruka na Wuta. Wuta tana ƙone su, su sake rayuwa, ta sake ƙonawa. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Ya ce: ‘Waɗannan masu saɓa wa ubanninsu ne.’

Na wuce ta wurin wata jama’a. Suna shuka hatsi, nan take sai ya girma ya yi kai. Na ce: ‘Su wane ne waɗannan?’ Jibrilu ya ce: ‘Masu yin ibada saboda Allahu Ta’ala ne.’

Na isa wani teku. Ba zai yiwu a bayyana halin ban mamaki na wannan teku ba. Ya fi madara fari, yana da raƙuman ruwa kamar duwatsu. Na ce: ‘Mene ne wannan teku?’ Ya ce: ‘Sunan wannan teku Tekun Rai ne. Lokacin da Allah Maɗaukaki Zai raya matattu, Zai saukar da ruwan sama daga wannan teku. Jikunan da suka ruɓe, suka watse, za su rayu, su tashi daga kabari kamar yadda ciyawa take tsirowa…’

Sannan muka hau sama ta biyu. Jibrilu (alaihis-salam) ya sake ƙwanƙwasa ƙofa. Aka ce: ‘Wane ne kai?’ ‘Ni ne Jibrilu.’ ‘To wane ne wanda yake tare da kai?’ ‘Shi ne Muhammadu alaihis-salam.’ ‘An aiko masa da wahayi da kiran Mi’iraji?’ ‘E, ya zo’, ya ce. Aka ce: ‘Maraba ga wanda ya zo! Wannan mai zuwa, mai kyawun matafiyi ne!’, nan take ƙofar ta buɗe. Na ga kaina a wurin Isa da Yahaya ɗan Zakariyya (alaihimas-salam), waɗanda uwayensu ƴan’uwan juna ne. Suka ce mini ‘Maraba’, suka yi mini addu’a… (Isa alaihis-salam mai matsakaicin tsayi ne, launin fatarsa fari mai ɗan ja ne irin na alkama.)

Na haɗu da wata jama’ar mala’iku. Sun jera sahu suna tsaye, dukkansu a ruku’u suke. Suna da tasbihi na kansu. Kullum suna ruku’u, ba sa ɗaga kawunansu su dubi sama. Jibrilu (alaihis-salam) ya ce: ‘Ibadar waɗannan mala’iku haka take. Ka roƙi Allah Maɗaukaki, al’ummarka ta samu.’ Na yi addu’a. Ya karɓa, Ya ba da ruku’u a cikin salla.

Sannan muka hau sama ta uku. Bayan tambaya da amsa iri ɗaya, ƙofar ta buɗe, na ga kaina a wurin Yusufu (alaihis-salam). Na duba, an ba shi rabin kyau. Ya ce mini ‘Maraba’, ya yi mini addu’a…

Na ga mala’iku masu yawa. A sahu suke, dukkansu a sujada suke. Tun da aka halicce su suna sujada, suna tasbihi da tasbihi na kansu. Jibrilu (alaihis-salam) ya ce: ‘Ibadar waɗannan mala’iku haka take. Ka roƙi Allahu Ta’ala Ya sauƙaƙa wa al’ummarka wannan aiki.’ Na roƙi Allah Maɗaukaki. Ya karɓa, Ya ba ku ita a cikin salla.

Na isa sama ta huɗu. Tana da ƙofa ta nuri, da aka yi da azurfa tsantsa. An rataya mata maƙulli na nuri. A kan maƙullin an rubuta ‘La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah’. Bayan tambaya da amsa iri ɗaya na ga kaina a wurin Idrisu (alaihis-salam). Ya ce mini ‘Maraba’, ya yi mini addu’a. Allahu Ta’ala Ya ce a kansa (a ma’ana): ‘Mun ɗaukaka shi zuwa wani wuri maɗaukaki.’2

Na ga wani mala’ika. Yana zaune a kan wata kujera, cikin baƙin ciki da damuwa. A kewayensa akwai mala’iku masu yawa, waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki ne kaɗai Ya san yawansu. A damansa na ga mala’iku masu nuri (nurani). Suna sanye da kore, suna da ƙanshi mai daɗi ƙwarai. Saboda kyawun kowannensu ba a iya kallon fuskokinsu. A ɓangaren hagunsa akwai mala’iku da wuta take fitowa daga bakunansu. A gabansu akwai mashi da bulala na wuta. Suna da irin idanun da ba a iya jure kallonsu. Mala’ikan da yake zaune a kan kujerar yana da idanu tun daga kansa har ƙafafunsa. Kullum yana dubin littafin da yake gabansa, ba ya ɗauke idonsa daga gare shi ko na ɗan lokaci. A gabansa akwai wani itace. A kowane ganyensa an rubuta sunan mutum ɗaya. A gabansa akwai wani abu kamar ƙwarya. Wani lokaci yakan ɗauki wani abu daga ciki da hannun damansa ya miƙa wa mala’iku masu nuri da suke damansa, wani lokaci kuma ya ɗauki wani abu da hannun hagunsa ya ba mala’iku masu duhu (zulmani) da suke hagunsa. Da na kalli (wannan) mala’ika, tsoro ya shiga zuciyata. Na ce wa Jibrilu: ‘Wane ne wannan mala’ika?’ Ya ce: ‘Azra’ilu ne. Babu wanda yake da ƙarfin ganin fuskar wannan.’ Ya je wurinsa ya ce: ’Ya Azra’ilu!

“‘Maraba ga wanda ya zo! Wannan mai zuwa, mai kyawun matafiyi ne!’ suka ce, nan take ƙofar ta buɗe, na ga kaina a gaban Adamu (alaihis-salam)” Hadisi mai daraja

Wannan shi ne Annabin ƙarshen zamani, habibin Allahu Ta’ala, masoyinSa.’ Azra’ilu (alaihis-salam) ya ɗaga kansa, ya yi murmushi. Ya tashi, ya girmama ni, ya ce: ‘Maraba! Allah Maɗaukaki bai halicci wanda ya fi ka daraja ba. Al’ummarka ma ta fi dukkan al’ummomi ɗaukaka. Ni ina jin ƙan al’ummarka fiye da ubanninsu da uwayensu.’ Na ce: ‘Ina da roƙo guda a gare ka. Al’ummata mai rauni ce. Ka yi musu laushi. Ka karɓi rayukansu da tausasawa.’ Ya ce: ’Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda Ya aiko ka annabi na ƙarshe, Ya kuma mayar da kai habibinSa, Allahu Ta’ala Yakan umarce ni sau saba’in a dare da rana:

‘Ka karɓi rayukan al’ummar Muhammadu da laushi da sauƙi, ka gudanar da al’amuransu da tausasawa.’ Saboda haka ni ma ina tausaya wa al’ummarka fiye da uwayensu da ubanninsu.’ Sannan muka hau sama ta biyar, a can muka haɗu da Haruna3 (alaihis-salam). Ya ce mini ‘Maraba’, ya yi mini addu’ar alheri. Na ga ibadar mala’ikun sama ta biyar. Dukkansu suna tsaye a ƙafafunsu, suna kallon yatsun ƙafafunsu, ba sa taɓa kallon wani wuri, suna tasbihi da babbar murya. Na tambayi Jibrilu (alaihis-salam): ‘Ibadar waɗannan mala’iku haka take?’ Ya ce: ‘E, ka roƙi Allah Maɗaukaki Ya ba al’ummarka wannan ibada.’ Na yi addu’a. Allah Maɗaukakin Sarki Ya bayar. Sannan muka hau sama ta shida. A can muka haɗu da Musa (alaihis-salam). Ya ce mini ‘Maraba’, ya yi mini addu’ar alheri.

Sannan muka hau sama ta bakwai. Bayan tambaya da amsa iri ɗaya, na sami Ibrahim (alaihis-salam) ya jingina bayansa ga Baitul-Ma’mur. Wannan Baitul-Ma’mur ɗin, kowace rana mala’iku dubu saba’in suke shiga cikinsa (kuma ba su ƙara samun dama ba). Na yi wa Ibrahim (alaihis-salam) sallama. Ya amsa sallamata. Ya ce: ‘Maraba, annabi salihi, ɗa salihi.’ (Sannan:) ‘Ya Muhammadu! Wurin Aljanna mai taushi ne ƙwarai, ƙasarta kuma tsarkakiya ce. Ka faɗa wa al’ummarka, su dasa itatuwa da yawa a can’, ya ce. Na ce: ‘Yaya ake dasa itace a Aljanna?’ Ya ce: ‘Ta hanyar karanta tasbihin “La haula wa la ƙuwwata illa billah”’ (a wata ruwaya kuma): “Subhanallahi wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wallahu akbar”. Sannan (Jibrilu alaihis-salam) ya kai ni Sidratul-Muntaha. Sidratul-Muntaha itace ne da saiwarsa take a sama ta shida, kututturensa da rassansa a saman sama ta bakwai, ganyensa kamar kunnuwan giwa, ƴaƴansa kuma kamar manyan tuluna.4 Kamar itace ne da yake yi wa dukkan sammai da Aljanna inuwa da inuwarsa. Da bayyanar nurin girma da ɗaukakar Allahu Ta’ala, yakan ɗauki launuka iri-iri, ya ƙawatu da yaƙutu, zumurrudu ko jauhari irinsu, ya yi kyau yadda babu ɗaya daga cikin halittun da Allahu Ta’ala Ya halitta da zai iya bayyana kyawunsa.

Jibrilu (alaihis-salam) ya kai ni bayan Sidratul-Muntaha, ya yi mini bankwana. Na ce: ‘Ya Jibrilu! Za ka bar ni ni kaɗai?’ Jibrilu (alaihis-salam) ya shiga damuwa. Ya fara rawar jiki saboda girman Allah Maɗaukaki, ya ce: ’Ya Muhammadu! Idan na ɗauki taki guda (kuma), zan halaka saboda girman Allahu Ta’ala. Jikina duka zai ƙone, ya ɓace.’”

Shugaban Talikai ya zo tare da Jibrilu alaihis-salam har zuwa nan. A nan Jibrilu alaihis-salam ya nuna kansa ga Manzon Allah a siffar da aka halicce shi, ya buɗe fikafikansa dubu ɗari shida, a kowane fiffike lu’ulu’u da yaƙutu suna watsuwa.

Sannan wata koriyar shimfiɗar Aljanna mai suna Rafraf ta zo, haskenta ya fi na rana. Tana shagaltuwa da zikirin Allahu Ta’ala ba tare da tsayawa ba, sautin tasbihi yana cika duniyar da take ciki. Ta yi wa Shugabanmu Annabi sallama. Shugabanmu Manzon Allah ya zauna a kan Rafraf. Nan take suka haura zuwa sama ƙwarai, suka wuce ta labule dubu saba’in da ake kira hijabi. Tsakanin kowane hijabi nesa ƙwarai ne. A kowane labule akwai mala’iku masu aiki. Rafraf ta wuce da Shugabanmu Annabi ta waɗannan labulai ɗaya bayan ɗaya. Ta haka suka ƙetare Kursiyyu, Al’arshi da duniyoyin rayuka. Habibi Mafi Daraja, Annabi Mai Girma (sallallahu alaihi wa sallam), duk lokacin da ya wuce ta wani labule, yana jin ana umarni: “Kada ka ji tsoro, ya Muhammadu! Kusanto, kusanto!” Ya kusanta har ya isa maƙamin Ƙaba Ƙausaini. Ta hanyar da ba a sani ba, ba a fahimta ba, ba a iya bayyanawa ba, ya isa ga ɗaukakar da Allahu Ta’ala Ya so. Ba tare da wuri, lokaci, fuska ko siffa ba, ganin Allah (ru’ya) ya kasance, wato ya ga Allahu Ta’ala. Ya yi magana da Ubangijinsa ba tare da ido, kunne, wata hanya ko tsakani ba. Ya sami ni’imomin da babu wata halitta da za ta iya sani ko fahimta.

Imam Rabbani ya ce a cikin “Maktubat” ɗinsa: “Wancan Jagora alaihis-salatu was-salam, a daren Mi’iraji, bai ga Ubangijinsa a duniya ba. A Lahira ya gan Shi. Domin Manzo alaihis-salam a daren nan ya fita daga kewayen lokaci da wuri. Ya sami lokaci guda marar farko kuma marar ƙarshe. Ya ga farko da ƙarshe a matsayin ɗigo guda. Ya ga a daren nan shigar Aljanna ta waɗanda za su shiga Aljanna bayan shekaru dubbai, da kasancewarsu a Aljanna. To, gani a wannan maƙami, ba gani ba ne na duniya. Gani ne irin ganin Lahira.”

Da aka ce wa Shugabanmu Annabi: “Ka yabi Ubangijinka!”, nan take ya ce: “At-tahiyyatu lillahi was-salawatu waɗ-ɗayyibat” (wato: dukkan yabo, kirari da godiya da ake yi da harsuna, hidimomi da ɗa’a da ake yi da jiki, alherai da kyautatawa da ake yi da dukiya, su kasance saboda Allahu Ta’ala).

“Allah Maɗaukaki bai halicci wanda ya fi ka daraja ba. Al’ummarka ma ta fi dukkan al’ummomi ɗaukaka” Azra’ilu alaihis-salam

Da farko Allahu Ta’ala Ya yi wa HabibinSa sallama, ba tare da ido, kunne, wata hanya ko wuri ba: “Assalamu alaika ayyuhan-nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuh” (Ya ManzoNa! SallamaTa, albarkaTa da rahamaTa su tabbata a kanka). Shugabanmu Annabi ya amsa: “Assalamu alaina wa ala ibadillahis-salihin” (Ya Ubangijina! Aminci ya tabbata a gare mu da kuma bayinKa salihai).

Mala’ikun da suka ji wannan suka ce da baki ɗaya: “Ash-hadu an la ilaha illallah wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluh” (Na sani kuma na yi imani kamar na gani da idona: babu abin bauta da ya cancanci ibada sai Allahu Ta’ala. Muhammadu alaihis-salam bawanSa ne kuma manzonSa).

Da Shugabanmu Annabi ya ce: “Assalamu alaina…”, Allahu Ta’ala Ya ce: “Ya MasoyiNa! A nan babu kowa sai Mu biyu. Don me ka ce ‘alaina’ (a gare mu)?” Shugabanmu Manzon Allah ya amsa kamar haka:

“Ya Ilahi! Jikunan al’ummata, haƙiƙa, ba tare da ni suke ba. Amma rayukansu tare da ni suke. Dubana na kulawa da cikakkiyar himmata ba su da nisa daga gare su. Ka yi mini sallama, Ka nisanta ni daga dukkan sharri. Yaya zan hana wancan al’ummata talakawa, masu damuwa, waɗanda fitinar ƙarshen zamani ta same su, wannan babban karimci da kyauta? Yaya zan bar su marasa rabo a irin wannan ni’ima?”

Allahu Ta’ala Ya ce: “Ya MasoyiNa! A daren nan kai baƙoNa ne. Ka roƙe Ni, me kake so?” Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “Ina son al’ummata (ya Ubangijina!).”

Bisa ruwaya, Allah Maɗaukaki Ya maimaita wannan tambaya haka sau ɗari bakwai. Shugabanmu Manzon Allah a kowanensu ya amsa: “Ina son al’ummata.” Da Allahu Ta’ala Ya ce: “Kullum al’ummarka kake so”, sai ya roƙa: “Ya Ubangijina! Mai roƙo ni ne, Mai bayarwa Kai ne. Ka yafe mini dukkan al’ummata.” Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: “Idan Na yafe maka dukkan al’ummarka a daren nan, rahamaTa da darajarka ba za su bayyana ba. Kashi ɗaya Na yafe maka a daren nan. Kashi biyu Na jinkirta. A Ranar Ƙiyama ka roƙa, Ni In yafe. Domin rahamaTa da darajarka (martabarka) su bayyana.”

Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce a cikin wani hadisi mai daraja: “A daren nan (daren Mi’iraji), na roƙi Allahu Ta’ala Ya danƙa mini hisabin dukkan al’ummata. Allah Maɗaukaki Ya ce: ‘Ya Muhammadu! Nufinka da wannan shi ne kada kowa ya san laifukan al’ummarka. NufiNa kuwa shi ne: kai annabi ne mai tausayi, laifukansu da munanan ayyukansu su kasance a rufe a gare kai ma, kamar yadda suke a rufe ga baƙi. Ya Muhammadu! Kai mai nuna musu hanya ne. Ni Ubangijinsu ne. Kai yanzu ka gan su. Ni tun fil-azal har abada Na dube su, kuma Ina dubansu. Ya Muhammadu! Da ba don Ina son yin magana da al’ummarka ba, da ba Zan yi musu hisabi a Ranar Ƙiyama ba. Da ba Zan tambaye su ko wani zunubi nasu ba, babba ko ƙarami.’”

“Allahu Ta’ala Ya ce: ‘Ya Muhammadu! Buɗe idonka mai albarka, ka dubi ƙarƙashin ƙafarka.’ Na duba, na ga tafin turɓaya guda. Allah Maɗaukaki Ya ce: ‘Dukkan abubuwan da suke samuwa turɓayar ƙafarka ce. Wannan turɓayaTa ka kawo ta gaban Masoyi? Yafe wa al’ummarka ya fi sauƙi a gare Ni fiye da yafe ƙurar da ta manne wa gefen rigar masoyi.’”

Na ba ka al’ummarka, ya Habibi!
AljannaTa Na ba su rabo a cikinta.
Ya MasoyiNa, mene ne abin da ka roƙa,
Shin tafin turɓaya ne kake roƙo?

Shugabanmu Annabi ya ce a cikin wani hadisi mai daraja: “Na yi wa Allah Maɗaukaki tambayoyi da dama. Na ji amsarsu. Na yi nadamar tambayar. (Wasu daga cikinsu su ne:)

‘Ya Ubangijina! Ka ba Jibrilu fikafikai dubu ɗari shida. A gaban wannan, mene ne kyautarKa a gare ni?’ Allah Maɗaukaki Ya ce: ‘Gashi guda naka ya fi fikafikai dubu ɗari shida na Jibrilu soyuwa a gare Ni. Saboda gashi guda naka, a Ranar Ƙiyama Zan ƴanta dubban masu saɓo, masu zunubi. Ya Muhammadu! Idan Jibrilu ya buɗe fikafikansa, zai cika tsakanin gabas da yamma. Idan ka yi ceto, ko da tsakanin gabas da yamma ya cika da masu saɓo, Zan yafe maka su duka.’ Na ce: ‘Ka sa mala’iku suka yi wa ubana Adamu (alaihis-salam) sujada. A gaban wannan, mene ne karimcinKa a gare ni?’

Allah Maɗaukaki Ya ce: ‘Sujadar da mala’iku suka yi wa Adamu, saboda nurinka ne da yake a goshinsa. Ya Muhammadu! Na ba ka abin da ya fi wannan. Na kusanta sunanka da sunaNa, Na rubuta shi a saman Arsh-i A’la. A lokacin ba a halicci Adamu ba, ba shi da suna ko alama. Na rubuta sunanka a ƙofofin sammai, a kan hijabai, a ƙofofin Aljanna, a fadoji da itatuwa, a kowane wurin Aljanna. A Aljanna babu wani abu da ba a rubuta “La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah” a kansa ba. Wannan matsayi ya fi matsayin da aka ba Adamu ɗaukaka.’

Da na ƙaunace ka, ya mai daraja!
Duniya da Lahira ba naka ba ne, ya mai laushi?
Na mayar da zatinka madubin ZatiNa,
Na rubuta sunanka tare da sunaNa.

‘Ya Ubangijina! Ka ba Nuhu (alaihis-salam) jirgin ruwa. A gaban wannan, me Ka yi mini na kyauta?’ Ya ce: ‘Na ba ka Buraƙ, Na isar da kai daga ƙasa zuwa Al’arshi a dare guda. Ka ga Aljanna da Wuta. Al’ummarka kuma Na ba su masallatai; a Ranar Ƙiyama al’ummarka za su hau waɗannan masallatai kamar yadda ake hawa jiragen ruwa, su ƙetare Siraɗi a cikin lokacin ƙiftawar ido, su tsira daga Wuta.’ ‘Ya Ubangijina! Ka saukar wa Bani Isra’ila manna da naman tsuntsu mai kama da makwarwa.’ Allah Maɗaukaki Ya ce: ’Na ba ka da al’ummarka ni’imar duniya da Lahira. Siffofin Bani Isra’ila Na canza su daga siffar mutum zuwa siffar beyar, biri da alade. Ban yi wa ko ɗaya daga cikin al’ummarka haka ba. Ko da sun yi aiki irin ayyukansu, ban ga wannan bala’i ya dace da su ba. Ya Muhammadu! Na ba ka wata sura da babu kamarta a cikin Attaura da Injila. Wannan sura Suratul Fatiha ce. Duk wanda ya karanta wannan sura, jikinsa ya zama haram ga Wuta. Ina sauƙaƙa azabar uwar wannan mutum da ubansa. Ya Muhammadu! Ni ban halicci wanda ya fi ka akram (daraja, ɗaukaka, girma) ba. Na farlanta maka da al’ummarka salla hamsin a dare da rana.

“A daren nan (daren Mi’iraji), na roƙi Allahu Ta’ala Ya danƙa mini hisabin dukkan al’ummata” Hadisi mai daraja

Ya Muhammadu! Duk wanda ya karɓi kaɗaitakaTa, bai haɗa kome da Ni ba, Aljanna tasa ce. Ga al’ummarka irin waɗannan Na haramta Wuta. RahamaTa ga al’ummarka ta rinjayi fushiNa.

Ya Muhammadu! A wuriNa kai ne akram, mafi daraja, a cikin dukkan halittu. A Ranar Ƙiyama Zan yi maka karimci har dukkan talikai su yi mamaki. Ya MasoyiNa! Har sai ka shiga Aljanna, an hana sauran annabawa da al’ummominsu shiga. Har sai al’ummarka ta shiga, wata al’umma ba za ta shiga ba. Ya Muhammadu! Kana son ka ga abin da Na shirya maka da al’ummarka?’ Na ce: ‘Ina so, ya Ubangijina!’ Ya yi magana da Isra’filu Ya ce: ‘Ya Isra’filu! Ka faɗa wa Jibrilu, bawaNa, amintacceNa kuma manzoNa, ya kai MasoyiNa Aljanna, ya nuna masa abin da Na shirya a Aljanna domin MasoyiNa da al’ummarsa. Domin zuciyarsa mai albarka ta kuɓuta daga damuwa.’”

Ƙaunataccen Annabinmu, Shugaban Talikai, ya zo wurin Jibrilu alaihis-salam tare da Isra’filu alaihis-salam. Domin ya aiwatar da umarnin Allahu Ta’ala, Jibrilu alaihis-salam ya kai Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) Aljanna. Mala’iku suna jira da faranti a hannuwansu: a ɗaya akwai hulla (tufafin Aljanna), ɗayan kuma cike yake da nuri. Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Manzon Allah! Waɗannan an halicce su shekara dubu tamanin kafin Adamu alaihis-salam. A wannan maƙami, suna rashin haƙurin watsa abin da yake cikin farantan a kanka da al’ummarka. A Ranar Ƙiyama, lokacin da kai da al’ummarka, bisa umarnin Allahu Ta’ala, kuka taka ƙofar Aljanna, waɗannan mala’iku za su watsa jauharin da yake cikin farantan a kanku.” Mala’ika mai aiki a Aljanna, mai suna Ridwan, ya tarbe su. Ya ba Shugabanmu Annabi bushara, ya ce: “Allah Maɗaukaki Ya raba Aljanna kashi uku, domin Ya ba al’ummarka biyu, ɗaya kuma ga al’ummomin sauran annabawa.” Ya zagaya da shi ko’ina a Aljanna. Habibi Mafi Daraja ya ce: “Na ga wani kogi a tsakiyar Aljanna.

Yana gudana a saman Al’arshi. Daga wuri guda ruwa, madara, giya da zuma suke fitowa. Ba sa taɓa haɗuwa da juna. Gaɓar wannan kogi ta zabarjad ce. Duwatsun da suke cikinsa jauhari ne, laƙarsa ambar, ciyawarsa za’afaran. An sa ƙoƙunan azurfa a kewayensa, yawansu ya fi taurarin sama. A kewayensa akwai tsuntsaye, wuyoyinsu kamar wuyan raƙumi. Duk wanda ya ci namansu, ya sha daga wannan kogi, zai sami yardar Allah Maɗaukaki. Na tambayi Jibrilu: ‘Mene ne wannan kogi?’ Ya ce: ‘Kausar ne. Allah Maɗaukaki Ya ba ka shi. Daga wannan Kausar ne ruwa yake gudana zuwa lambunan da suke cikin Aljanna takwas.’ Na ga alfarwai a gaɓar wannan kogi. Dukkansu na lu’ulu’u da yaƙutu ne. Na tambayi Jibrilu. Ya ce: ‘Wuraren zaman matanka ne.’ A cikin waɗancan alfarwai na ga hurul-aini. Fuskokinsu suna haskakawa kamar rana, dukkansu suna rera waƙoƙi iri-iri da muryoyinsu. Suna cewa: ’Mu masu farin ciki ne, masu nishaɗi. Baƙin ciki ba ya zuwa gare mu ko kaɗan.

Mu ƙawatattu ne, ba ma taɓa zama tsirara. Mu matasa ne, ba ma taɓa tsufa. Mu masu kyawawan ɗabi’u ne, ba ma taɓa fushi. Mu kullum haka muke, ba ma taɓa mutuwa.’ Waƙoƙinsu da muryoyinsu suna isa fadojin farin ciki da itatuwansa, suna rufe ko’ina. Suna da muryoyi masu daɗi yadda, da waɗannan waƙoƙi sun zo duniya, da ba a sami mutuwa da wahala a duniya ba. Jibrilu ya ce: ‘Kana son ka ga fuskokinsu?’ Na ce: ‘Ina so.’ Ya buɗe ƙofar wata alfarwa. Na duba. Na ga kyawawan siffofi yadda, ko da na bayyana kyawunsu tsawon rayuwata, ba zan gama ba. Fuskokinsu sun fi madara fari, kumatunsu sun fi yaƙutu ja, sun fi rana haske. Fatunsu sun fi alharini taushi, masu haske kamar wata, ƙanshinsu ya fi miski daɗi. Gashinsu baƙi ƙirin: na wasu a kitse, na wasu a tattare, na wasu a sake; idan ta zauna, yakan zama kamar alfarwa a kewayenta, idan ta tashi, yakan kai har ƙafarta. A gaban kowannensu wata mai hidima tana tsaye. Jibrilu ya ce: ‘Waɗannan saboda al’ummarka ne.’”

Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “Na ga lambuna da gonakin Aljanna takwas da kowace irin ni’imarsu. Sai ya zo mini a rai in ga Wuta ma da darajojinta. Jibrilu ya kama hannuna, ya kai ni wurin Malik, babban mala’ikan Wuta. Ya ce: ‘Ya Malik! Sayyidina Muhammadu yana son ya ga wuraren maƙiya a cikin Wuta, ka nuna masa Wuta.’” Da Malik ya buɗe murfin Wuta daga samanta, Wuta ta fara tafasa da kumbura da tsanani, har Shugabanmu Annabi (alaihis-salatu was-salam) ya ga da idanunsa yadda Wuta take kama kome ta ƙone shi, azabobin ƙishirwa da suke cikin Wuta, sarƙoƙin azaba, macizai da kunamomin azaba, da wasu daga cikin azabobin da suke can.

“Malik ya buɗe ɗabaƙoƙin Wuta. Na ga ɗabaƙoƙi bakwai (duka). Ɗabaƙa ta bakwai ana kiranta Hawiya. Azabarta ta ninka ta sauran ɗabaƙoƙi sau da yawa. Na tambayi Malik: ‘A wannan ɗabaƙa wace jama’a ake azabtarwa?’ Malik ya ce: ‘Fir’auna da Ƙaruna da munafukan al’ummarka ake azabtarwa.’ Ɗabaƙa ta shida Laza ce. A can ana azabtar da mushrikai (waɗanda ba su da wani addini ko kaɗan). Ɗabaƙa ta biyar Huɗama ce. A can ana azabtar da masu bauta wa wuta da bijimi, da mabiya Buddanci.

Ɗabaƙa ta huɗu Jahim ce. A can ana azabtar da masu bauta wa rana da taurari. Ɗabaƙa ta uku Saƙar ce. A can ana azabtar da Kiristoci. Ɗabaƙa ta biyu Sa’ir ce. A can ana azabtar da Yahudawa. Ɗabaƙa ta farko Jahannama ce. Azabarta ta gaza ta sauran ɗabaƙoƙi. (Duk da haka) a can na ga tekuna dubu saba’in na wuta. Kowane teku yana da girma yadda, da an jefa ƙasa da sammai a cikin teku guda, aka umarci wani mala’ika, ko da ya nema shekara dubu, ba zai yiwu ya same su ba. Zabaniya (mala’ikun da suke aiki a Wuta) suna da girma yadda, da ɗayansu ya sa ƙasa da sammai a gefe guda na bakinsa, ba za a gane ko kaɗan ba. Waɗancan tekuna suna hauhawa da raƙuman ruwa, suna fitar da sautuka masu ban tsoro. Da ɗan kaɗan daga wannan sauti ya zo duniya, da dukkan masu rai sun halaka.

Na tambaya: ‘Wannan ɗabaƙa ta wace jama’a ce?’ Malik bai amsa ba. Na sake tambaya. Ya yi shiru… Jibrilu ya ce wa Malik: ‘Yana jiran amsa daga gare ka.’ Shi kuma ya nemi gafara: ‘Ka yi mini uzuri.’ Na ce: ‘Ko mene ne, ka ba da amsa, domin a sami yin tanadinsa yau.’ Malik ya ce: ‘Ya Manzon Allah! Ta masu saɓo na al’ummarka ce. Ka yi musu nasiha, domin su kare kansu daga wannan wuri mai ban tsoro. Su nisanci abubuwan da za su ja jikunansu zuwa irin wannan azaba. A ranar nan ba zan ji ƙan masu saɓo ba. Ba zan tausaya wa tsofaffinsu masu farin gemu ba, ba kuma matasansu ba.’”

“Mi’iraji shi ne wurin da hankali ya ƙare, imani ya fara” Hadisi mai daraja

Shugaban Talikai ya fara kuka. Ya cire rawaninsa daga kansa mai albarka, ya fara ceto da roƙo (ga Allahu Ta’ala). Yana faɗar raunin al’ummarsa da cewa ba za su iya jure irin wannan azaba ba, ya yi kuka ƙwarai, har Jibrilu alaihis-salam da dukkan mala’iku suka yi kuka tare da shi. Sai magana ta zo daga Allahu Ta’ala: “Ya MasoyiNa! Girmanka da darajarka a wuriNa manya ne, addu’arka ta karɓu. Ka kwantar da hankalinka. Na isar da kai ga abin da kake so. Zan ba ka irin maƙamin da Zan yafe masu saɓo masu yawan gaske saboda cetonka. Har sai ka ce ya isa. Ya MasoyiNa! Duk wanda ya riƙe umarniNa, zai tsira daga azaba da uƙuba, ya sami rahamaTa. Zai sami darajar ganiNa a Aljanna. Na farlanta maka da al’ummarka salla hamsin a dare da rana.”

Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya ci gaba yana cewa: “(Bayan) wannan maƙami na isa Al’arshi. Na wuce ta sammai, na zo maƙamin da Musa (alaihis-salam) yake. Ya ce mini: ‘Me Allah Maɗaukaki Ya farlanta maka da al’ummarka?’ Ni kuma na ce: ‘Ya farlanta mini yin salla hamsin a kowace rana da dare.’ Ya ce: ‘Ka koma wurin Ubangijinka, ka roƙe Shi Ya sauƙaƙa kaɗan. Domin al’ummarka ba za ta iya ɗaukar wannan ba. Ni na gwada Bani Isra’ila, na jarraba su.’ Bisa haka, na koma wurin Ubangijina, na ce: ‘Ya Ubangijina! Ka sauƙaƙa wa al’ummata (wannan umarni) kaɗan!’ Bisa haka Ya rage salla biyar kaɗai daga hamsin. Na koma wurin Musa (alaihis-salam), na faɗa (cewa Ya rage biyar). Ya ce: ‘Ka koma wurin Ubangijinka! Ka roƙe Shi Ya ƙara sauƙaƙawa kaɗan. Domin al’ummarka ba za ta iya ɗaukar wannan ba.’ Ta haka na yi ta kai-kawo tsakanin Musa (alaihis-salam) da Ubangijina, a ƙarshe Allahu Ta’ala Ya ce: ‘Na rage wannan salla zuwa biyar. Kowace salla tana da lada goma. Ta wannan fuska, a ƙarshe ta sake zama salla hamsin. Domin duk wanda ya yi niyyar lada ɗaya bai iya aikatawa ba, ana rubuta masa lada ɗaya. Amma idan ya aikata, ana rubuta lada goma cif a madadin ɗaya. Amma idan ya yi niyyar zunubi ɗaya bai aikata ba, ba a rubuta kome. Idan ya aikata, ana rubuta shi zunubi ɗaya kawai.’ Sannan na sauka wurin Musa (alaihis-salam), na ba shi labarin halin da ake ciki. Ya sake cewa: ‘Ka koma, ka roƙe Shi Ya ƙara sauƙaƙawa kaɗan.’ Bisa haka na ce masa: ‘Saboda yawan roƙon da na yi wa Ubangijina, yanzu ina jin kunya.’”5 Ta haka Allahu Ta’ala Ya ta’azantar da zuciya mai albarka ta ƙaunataccen Annabinmu, da wahalhalun da ya sha suka raunata. Ya ba shi ni’imomin da bai ba wata halittarSa ba, da babu wanda zai iya sani ko fahimta.

Zo nan, ya mai ƙonewa a wutar ƙauna,
Wanda yake ɗaukar kansa masoyin Masoyi.
Zo ka saurari Mi’irajin wancan Sarki a fili,
Idan masoyi ne kai, kada ka tsaya, ka ƙone a wutar ƙauna.
Daren Litinin ne, labari tabbatacce,
Ashe daren nan Lailatul-Ƙadri ce.
Wancan mai sa’a mai albarka, mai daraja maɗaukakiya,
A gidan Ummu Hani yake a daren nan.
Waɗanda suka zo kafinsa ba su kai wannan matsayi ba,
Babu wanda ya sami wannan ɗaukaka.
Domin ya ga dukkansu, ya wuce gaba,
Ya je, ya isa ga wancan Mai Girma.
Mai Girma da Buwaya, Wanda Ya tsarkaka daga fuskoki shida,
Ba tare da yaya ko nawa ba, Ya nuna masa kyawunSa.
A fili ya ga Ubangijin buwaya,
A Lahira haka al’ummarsa za ta gan Shi.
Kai da ka hau Mi’iraji, ka yi roƙo,
Mi’irajin al’ummarka Na mayar da shi salla.

“Ya MasoyiNa! Duk wanda ya riƙe umarniNa, zai tsira daga azaba da uƙuba, ya sami rahamaTa. Zai sami darajar ganiNa a Aljanna” Hadisi ƙudusi

Na yi imani! Raina fansa a gare ka, ya Manzon Allah

Sannan Shugaban Talikai, a ƙiftawar ido, ya zo Ƙudus, daga can kuma ya hau Buraƙ, da aka ɗaure a ƙofar Masallacin Aƙsa, domin ya tafi Makka al-Mukarrama, ya koma Makka. Shugabanmu Annabi, lokacin da yake zuwa Makka daga Ƙudus, ya haɗu da ayarin Ƙuraishawa. Wani raƙumi a cikin ayarin ya firgita, ya faɗi. Shugabanmu Manzon Allah ya zo gidan Ummu Hani a Makka al-Mukarrama. Wurin da ya kwanta bai yi sanyi ba tukuna, motsin ruwan alwala da yake cikin ƙwaryar bai tsaya ba tukuna. Ummu Hani, da take kewayawa a waje, gyangyaɗi ya ɗauke ta, ba ta san kome ba.

Da safiya ta yi, Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), bayan ya ba Ummu Hani labarin Mi’irajinsa, ya ce: “Da safe zan je Ka’aba in ba da labarin wannan.” Nana Ummu Hani ta ce: “Ya ɗan baffana! Kada ka faɗa wa Ƙuraishawa wannan! Za su ƙaryata ka, su ɓata maka rai. Masu raunin imani ba za su yarda da wannan ba, za su fita daga addini. Mushrikai ma wannan suke jira, za su ɓata imaninsu. A yanzu Musulmi kaɗan ne.

Idan ka ba da labari lokacin da Musulmi suka ɗan sami ƙarfi, suka ƙarfafa, yaya zai kasance?” Amsar tarihi da Shugaban Talikai, Sarkin Halittu, ya bayar ita ce: “Wallahi, zan faɗa musu wannan. Abin da yake ruɓaɓɓe yau, gobe ma ruɓaɓɓe ne. Zan gina wannan Musulunci da waɗanda imaninsu yake da ƙarfi. Idan akwai wanda har yanzu yake da shakku a kaina, ya rabu ya tafi. Ba ni da wani abu da su. Ruɓaɓɓe kullum ruɓaɓɓe ne. In ba yau ba, gobe zai ruɓe. Maimakon ya ruɓe daga baya, ya ruɓe tun yanzu, domin kada mu kama hanya muna dogara da shi. Ƙarfafa sun ishe mu.”

Da safe kuma ya tafi Ka’aba, ya fara ba da labari… Kafirai suka yi ba’a suna cewa: “Muhammadu ya rasa hankalinsa, ya ɓace gaba ɗaya.” Waɗanda suke da niyyar musulunta ma suka shiga shakku. Wasu daga cikin mushrikai suka zo gidan Abubakar cikin farin ciki. Domin sun san sarai cewa shi ɗan kasuwa ne mai hankali, mai gogewa, mai lissafi. Da ya fito ƙofa, suka tambaya: “Ya Abubakar! Ka sha zuwa Ƙudus ka dawo. Ka sani sosai. Zuwa Ƙudus daga Makka da dawowa yana ɗaukar lokaci nawa?” Sayyidina Abubakar ya ce: “Na sani sosai. Fiye da wata guda.” Gungun kafiran da suka yi farin ciki da wannan magana suka ce: “Maganar mutum mai hankali, mai gogewa haka take.” Suna dariya, suna ba’a, suna kuma fatan Sayyidina Abubakar ma zai yi tunani irin nasu, suka ce: “Shugabanka yana cewa ya je Ƙudus ya dawo a dare guda, yanzu ya ɓace gaba ɗaya.” Suka nuna wa Sayyidina Abubakar ƙauna da girmamawa, suka dogara da shi.

Sayyidina Abubakar, da ya ji sunan Shugabanmu Manzon Allah mai albarka, (ba tare da ya auna da hankalinsa da tunaninsa ko kaɗan ba) ya ce: “Idan shi ne ya faɗa, gaskiya ne. Ni ma na yi imani cewa ya je ya dawo a ƙiftawar ido”, ya shiga ciki. Kafirai cikin rikicewa suka koma suna cewa: “Kai, Muhammadu wane irin babban masihirci ne! Ya yi wa Abubakar sihiri.”

Sayyidina Abubakar nan take ya zo wurin Shugabanmu Manzon Allah. A tsakanin babban taron jama’a, da babbar murya ya ce: “Ya Manzon Allah! Mi’irajinka ya kasance mai albarka! Ina godiya marar iyaka ga Allahu Ta’ala saboda Ya ɗaukaka mu da sanya mu masu hidima ga babban Annabi irinka, Ya kuma ni’imta mu da ganin fuskarka mai albarka da jin zantuttukanka masu daɗi, masu kama zukata, masu jan rayuka. Ya Manzon Allah! Kowace maganarka gaskiya ce. Na yi imani. Raina fansa a gare ka!” Maganganun Sayyidina Abubakar suka ba kafirai mamaki. Suka rasa abin da za su ce, suka watse. Sun ƙarfafa zukatan wasu mutane kaɗan ma da suka shiga shakku, masu raunin imani. A wannan rana Shugabanmu Manzon Allah ya kira Abubakar “Siddiƙ”. Da samun wannan suna, darajarsa ta ƙara hawa mataki ɗaya.6

Kafirai, da suka yi fushi ƙwarai da wannan hali, suka kasa jure wa ƙarfin imanin muminai, yadda suke gaskata kowace maganar Annabinmu nan take, yadda suke kewaye shi kamar asu a kewayen fitila. Domin su kunyata Shugabanmu Manzon Allah su rinjaye shi, suka fara jarraba shi.

Suka yi tambayoyi irin su: “Ya Muhammadu! Kana cewa ka je Ƙudus. Faɗa mana, masallacin yana da ƙofofi nawa, tagogi nawa?”

“Dole ne in ba da labarin Mi’iraji, wanda ba zai yi imani ba daga baya ma zai bari, ba a gina gini a kan ruɓaɓɓen tushe, wanda zai rabu ya rabu tun yanzu, ƙarfafa su zauna” Hadisi mai daraja

Masallacin Bai’a, da aka gina a wurin da aka yi mubaya’ar Aƙaba

Shugabanmu Manzon Allah ya amsa kowannensu ɗaya bayan ɗaya. Lokacin da Shugabanmu yake amsawa, Sayyidina Abubakar yakan ce: “Haka ne, ya Manzon Allah.” Alhali kuwa Shugabanmu Manzon Allah, saboda ladabinsa da kunyarsa, ko fuskar wanda yake gabansa ba ya kallo. Ya ce: “A Masallacin Aƙsa ban dubi kewayena ba. Ban ga abubuwan da suke tambaya ba. A lokacin nan Jibrilu (alaihis-salam) ya kawo mini Masallacin Aƙsa a gaban idona. Ina ganin tagoginsa ina ƙirgawa, ina amsa tambayoyinsu nan take.” Shugabanmu Manzon Allah ya faɗa cewa ya ga matafiya masu raƙuma a hanya, ya ce: “In sha Allahu, za su zo ranar Laraba.” Ranar Laraba, lokacin faɗuwar rana, ayarin ya isa Makka. Da aka tambayi waɗanda suke cikin ayarin, suka faɗa cewa an yi kamar guguwa, wani raƙumi kuma ya faɗi. Wannan hali ya ƙarfafa imanin muminai. Ƙiyayyar kafirai kuma ta ƙara ƙaruwa.7 Wannan mu’ujiza, da ta faru shekara ɗaya kafin Hijira, a daren Juma’a, 27 ga watan Rajab, ana kiranta Mi’iraji. Manzon Allah ya hau Mi’iraji da ransa da jikinsa, a farke. A daren Mi’iraji an nuna masa haƙiƙanin al’amuran Allah da yawa, kuma salloli biyar an farlanta su a wannan dare. Bugu da ƙari, an ba shi ayoyi masu girma biyu na ƙarshe na Suratul Baƙara. Mi’iraji an sanar da shi a cikin Alƙur’ani mai girma, a aya ta 1 ta Suratul Isra’i, a ayoyin farko na Suratun Najm, da kuma a wasu hadisai masu daraja.8

Ƙaunataccen Annabinmu, bayan Mi’iraji, lokacin da yake ba Sahabbansa labarin Aljanna, ya ce: “Ya Abubakar! Na ga fadarka. Ta jan zinariya ce. Na shaidi ni’imomin da aka shirya maka.” Sayyidina Abubakar kuma ya ce: “Wannan fada da mai fadar fansa a gare ka, ya Manzon Allah.”

Shugabanmu ya juya ga Sayyidina Umar ya ce: “Ya Umar! Na ga fadarka. Ta yaƙutu ce. A wannan fada akwai hurul-aini da yawa. Amma ban shiga ciki ba. Na yi tunanin kishinka.” Sayyidina Umar ya yi kuka ƙwarai. A cikin hawaye ya ce: “Uwata da ubana da raina fansa a gare ka, ya Manzon Allah! Shin ko a gare ka ma akwai kishi?” Daga baya ya ce wa Sayyidina Usman: “Ya Usman! Na gan ka a kowace sama. Na ga fadarka a Aljanna, na yi tunaninka.” Ya ce wa Sayyidina Aliyu: “Ya Aliyu! Na ga siffarka a sama ta huɗu. Na tambayi Jibrilu. Ya ce: ‘Ya Manzon Allah! Mala’iku sun yi shauƙin ganin Sayyidina Aliyu. Allah Maɗaukaki Ya halicci wani mala’ika a siffarsa. Yana a sama ta huɗu, mala’iku suna ziyartarsa, suna neman albarka.’ Sannan na shiga fadarka. Na shaƙi ƙanshin ƴaƴan wani itace. Daga ciki wata hurul-aini ta fito, ta rufe fuskarta da labule. Na ce: ‘Wace ce ke, kuma ta wane ne ke?’ Ta ce: ‘An halicce ni saboda Aliyu, ɗan baffanka, ya Manzon Allah!’”

Da safiyar daren Mi’iraji, Jibrilu alaihis-salam ya zo, ya yi wa Shugabanmu Manzon Allah limancin salloli biyar a lokutansu. An ce a cikin hadisi mai daraja: “Jibrilu (alaihis-salam) ya yi mini limanci kwana biyu a kusa da ƙofar Ka’aba. Mu biyu mun yi sallar asuba lokacin da alfijir ya keto, azahar lokacin da rana ta karkata daga tsakiyar sama, la’asar lokacin da inuwar kowane abu ta kai tsawonsa, magariba lokacin da rana take faɗuwa (lokacin da gefenta na sama ya ɓace), isha’i kuma lokacin da shafaƙi ya yi duhu. A rana ta biyu kuma mun yi sallar asuba lokacin da gari ya waye, azahar lokacin da inuwar kowane abu ta kai ninki biyu na tsawonsa, la’asar nan da nan bayan haka, magariba a lokacin buɗa baki, isha’i kuma lokacin da sulusin dare ya wuce. Sannan ya ce: ‘Ya Muhammadu! Lokutan sallarka da na annabawan da suka gabata su ne waɗannan. Al’ummarka su yi kowace salla daga cikin salloli biyar a tsakanin waɗannan lokuta biyu da muka yi.’”9 Bayan an sanar da lokutan salla haka, aka aika da labari zuwa Habasha ma, aka sanar da su su yi salloli biyar, su kuma rama sallolin da suka wuce tun daga lokacin da aka farlanta su har zuwa lokacin da suka fara yi.

“(Ya ku mutanen Madina!) Kuna yi mini alkawarin cewa za ku faɗi gaskiya a tafarkin Allah saboda Allah, za ku taimake ni kamar yadda kuke kare kanku da mutuncinku?” Hadisi mai daraja