Ƙaunataccen Annabina

Tafiyar Makka – Ɗa’if

Da niyyar sake zuwa a watan Zulhijja na shekara mai zuwa, suka nemi izini daga Annabinmu su koma ƙasarsu, suka tafi. Waɗannan mutum shida da suka musulunta sababbi su ne: Uƙba ɗan Amir, As’ad ɗan Zurara, Auf ɗan Haris, Rafi’ ɗan Malik, Ƙuɗba ɗan Amir da Jabir ɗan Abdullahi (radiyallahu anhum).1

Mutum shidan da suka musulunta, da suka koma Madina wurin mutanensu, nan take suka fara ba da labarin Musulunci da Annabinmu, suka fara kiran mutane su shiga addinin Musulunci. Sun yi haka da himma, har a Madina ba a bar gidan da ba a yi maganar Annabinmu da Musulunci a cikinsa ba. Ta haka, kamar yadda Musulunci ya yaɗu a cikin ƙabilar Khazraj, wasu mutane daga ƙabilar Aus ma suka musulunta.

Kiransa ga mutanen Ɗa’if zuwa ga imani

Mushrikai, duk da cewa sun ga mu’ujizozi masu yawan gaske daga ƙaunataccen Annabinmu, saboda taurin kansu ba su yi imani ba; har ma ba su daina azabtarwa da zaluntar ƴaƴansu, ƴan’uwansu, danginsu da abokansu da suka musulunta ba. Wannan zalunci da azaba tasu, waɗanda suke ƙara tsanani, sun sa ƙaunataccen Annabinmu baƙin ciki ƙwarai. Ya yi tunanin zuwa Ɗa’if, da take kusa da Makka, ya kira mutanenta zuwa Musulunci. Saboda haka ya ɗauki Zaid ɗan Harisa tare da shi, ya tafi Ɗa’if.

Ya gana da ƴaƴan Amr: Abdu Yalil, Habib da Mas’ud, daga cikin manyan Ɗa’if. Ya bayyana musu Musulunci, ya roƙe su su yi imani da Allahu Ta’ala. Su kuwa, ba ma yin imani ba, sai ma suka wulaƙanta shi, har ma suka ce: “Allahu Ta’ala bai sami wani da zai aiko annabi sai kai ba? Ko Allahu Ta’ala Ya kasa aiko wani annabi ba kai ba? Ka fita daga ƙasarmu, ka tafi duk inda kake so!.. Mutanenka ba su karɓi abin da kake faɗa ba, shi ya sa ka zo nan, ko ba haka ba? Mun rantse, mu ma za mu nisance ka. Ba za mu karɓi wata buƙata taka ba.”

Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya bar wurinsu cikin baƙin ciki. Kwana goma ko wata guda ya kira ƙabilar Saƙif zuwa Musulunci, amma babu ɗayansu da ya yi imani; har ma suka yi masa ba’a, suka azabtar da shi, suka yi masa ihu. Suka jera yara da samari a gefen hanyar da zai bi, suka sa suka jefe shi da duwatsu, suka kai masa hari. Sayyidina Zaid ya mayar da jikinsa garkuwa ga duwatsun da samarin Ɗa’if suke jefawa, yana ƙoƙarin hana wata cuta ta sami Annabinmu. Sayyidina Zaid yana kewaya ƙaunataccen Annabinmu, yana faman ƙoƙari domin kada duwatsu su same shi. Domin kada wata cuta ta sami jikinsa mai albarka, ba ya kula da duwatsun da suke zuwa kansa. Ashe ba yana jiran dama ne ya sadaukar da ransa a irin waɗannan kwanaki ba? Ga shi, suna jifan Shugaban Talikai, suna azabtar da shi, suna zaluntarsa, suna ƙoƙarin fitar da shi daga ƙasarsu.

Duk lokacin da Sayyidina Zaid ya yi gudu dama da hagu domin ya kare Shugabanmu Annabi, duwatsu suna samun kansa, jikinsa da ƙafafunsa bi da bi. Saboda haka ko’ina na jikin Sayyidina Zaid ya cika da jini. Yana ba da duk abin da yake da shi domin ya kare ƙaunataccen Annabinsa, yana ihu da dukkan ƙarfin muryarsa ga azzaluman da suke jifa: “Kada ku yi!.. Kada ku buga!.. Shi Shugaban Talikai ne! Manzon Allah ne shi!.. Ku yayyanka jikina guntu-guntu, amma kada wata cuta ta sami Annabinmu!..” Duwatsun da suka wuce Zaid ɗan Harisa suka iso ga Shugabanmu Manzon Allah sun bar ƙafafunsa masu albarka cikin jini.

Ƙaunataccen Annabinmu, cikin baƙin ciki, gajiya da rauni, ya kusanci gonar inabin wasu ƴan’uwa biyu masu suna Utba da Shaiba. A can, Shugabanmu Manzon Allah, wanda dukkan muminai suke son su sadaukar da rayukansu dominsa, ya shafe jinin da yake zuba daga ƙafafunsa masu albarka.

Ya yi alwala, ya yi salla raka’a biyu a ƙarƙashin wani itace. Sannan ya ɗaga hannuwansa masu albarka, ya yi roƙo ga Ubangijinsa.

Masu gonar suna kallon wannan hali. Sun ga abin da ya sami Shugabanmu Manzon Allah, sun shaidi kaɗaicinsa. Jijiyoyin tausayinsu suka motsa. Suka aika masa da inabi ta hannun bawansu mai suna Addas. Ƙaunataccen Annabinmu, lokacin da yake cin inabin, ya yi basmala. Bawan da ya kawo inabin Kirista ne. Da ya ji basmala, ya yi mamaki. Ya tambaya: “Shekaru da yawa ina nan, ban taɓa jin irin wannan magana daga kowa ba. Wace irin magana ce wannan?”

Manzon Allah ya ce: “Daga ina kake?” Addas ya ce: “Ni mutumin Ninawa ne.” Manzon Allah ya ce: “Ashe kai daga ƙasar Yunusa (alaihis-salam) kake.” Addas ya ce: “Ta ina ka san Yunusa? A nan babu wanda ya san shi.” Manzon Allah ya ce: “Shi ɗan’uwana ne. Shi ma annabi ne kamar ni.”

Addas ya ce: “Mai wannan kyakkyawar fuska, mai waɗannan zantuttuka masu daɗi ba zai iya zama maƙaryaci ba. Na yi imani cewa kai Manzon Allah ne.” Ya musulunta. Ya ce: “Ya Manzon Allah! Shekaru da yawa ina bautar waɗannan azzalumai, waɗannan maƙaryata. Suna cin haƙƙin kowa. Suna yaudarar kowa. Ba su da wani kyakkyawan ɓangare ko kaɗan. Domin su tara abin duniya su biya sha’awoyinsu, suna aikata kowane irin ƙasƙanci. Ina ƙyamarsu. Ina son in tafi tare da kai, in sami darajar yi maka hidima, in zama abin nufi ga rashin girmamawar da jahilai da wawaye za su yi maka, in sadaukar da raina domin in kare jikinka mai albarka.”2

Shugabanmu Manzon Allah, yana murmushi, ya ce: “Yanzu ka zauna a wurin iyayengijinka! Ba da daɗewa ba za ka ji sunana a ko’ina. A lokacin ka zo wurina.”

“Kada ku yi!.. Kada ku buga!.. Shi Shugaban Talikai ne! Manzon Allah ne shi!.. Ku yayyanka jikina guntu-guntu, amma kada wata cuta ta sami Annabinmu!..” Zaid ɗan Harisa (radiyallahu anhu)

Bayan sun huta kaɗan, suka kama hanyar Makka. Da ya rage tafiyar kwana biyu zuwa Makka, ya ga wani girgije yana yi musu inuwa. Da ya duba da kyau, ya fahimci cewa Jibrilu alaihis-salam ne. Wannan al’amari, ƙaunataccen Annabinmu ya ba uwarmu A’isha as-Siddiƙa labarinsa.

A cikin “Sahihul-Bukhari” da “Musnad” na Ahmad ɗan Hanbal an sanar da cewa: Wata rana uwarmu Nana A’isha ta tambaya: “Ya Manzon Allah! Shin wata rana mafi raɗaɗi fiye da ranar Uhud ta taɓa wuce kanka?” Shugabanmu Manzon Allah ya amsa kamar haka: “Wallahi, daga mutanenki na sha irin cutar da ban sha ba ko daga kafiran da suke Yaƙin Uhud. Lokacin da na gabatar da kaina ga Ibn Abdu Yalil ɗan Abdu Kulal (wato lokacin da na sanar da annabtata, na kira shi zuwa ga addini), bai karɓa ba. Na bar wurinsu da irin wannan babban raɗaɗi, har ban dawo hayyacina ba sai da na isa wurin da ake kira Ƙarnus-Sa’alib. A can na ɗaga kaina sama. Na ga wani girgije ya yi mini inuwa. Na duba, sai ga Jibrilu (alaihis-salam) a tsaye a cikin girgijen. Ya kira ni ya ce: ‘Ya Muhammadu! Allah Maɗaukaki Ya ji maganganun mutanenka a kanka. Ya kuma san cewa ba su so su kare ka ba. Ya aiko maka da wannan mala’ika da aka ɗora wa duwatsu, domin ka umarce shi da duk abin da kake so.’ Wannan mala’ika ma ya kira ni, bayan ya yi mini sallama ya ce: ’Ya Muhammadu! Kamar yadda Jibrilu ya faɗa, Allah Maɗaukaki Ya aiko ni, mala’ikan duwatsu, zuwa gare ka, domin ka umarce ni da duk abin da kake so. Ina shirye ga umarninka. Idan kana son waɗannan duwatsu biyu masu tsayi (dutsen Ƙu’aiƙi’an da dutsen Abu Ƙubais) su haɗu da juna har su rufe a kan mutanen Makka (su murƙushe mushrikai gaba ɗaya), ka yi umarni in haɗa su.’ Ban yarda ba, na ce: ’(A’a! An aiko ni rahama ga talikai.) Ina addu’a Allahu Ta’ala Ya fitar daga tsatson waɗannan mushrikai zuriya da za ta bauta wa Allah Maɗaukakin Sarki kaɗai, ba ta haɗa kome da Allahu Ta’ala.’”

Shugabanmu Annabi, lokacin da yake komawa Makka daga Ɗa’if, ya ɗan huta kaɗan a wurin da ake kira Nakhla. A wani lokaci ya tsaya salla. Wani gungun aljanun Nasibin, suna wucewa ta can, da suka ji ayoyin Alƙur’ani mai girma da ƙaunataccen Annabinmu yake karantawa, suka tsaya suka saurara. Sannan suka gana da Shugabanmu Annabi, suka musulunta. Shugabanmu Annabi ya ce musu: “Idan kun isa wurin mutanenku, ku sanar da su kirana zuwa ga imani. Ku kira su ma zuwa ga imani.”

Da waɗannan aljanu suka tafi wurin mutanensu suka sanar da wannan, dukkan aljanun da suka ji suka yi imani.3 Wannan al’amari an sanar da shi a cikin Alƙur’ani mai girma a Suratul Jinn, da kuma a cikin shahararrun littattafan hadisi mai daraja masu suna “Bukhari” da “Muslim”.

Da ya kusanci Makka, muminai suka aika wa Shugabanmu Manzon Allah labari: “Ƙuraishawa sun ji mummunar mu’amalar da ƙasƙantattun Ɗa’if suka yi maka. Idan ka zo yanzu, suna iya ƙara zaluncinsu.” Da Shugabanmu Annabi ya isa Hira, ya aika wani zuwa ga Suhail ɗan Amr, ya roƙe shi ya ɗauke shi ƙarƙashin kariyarsa. Da wannan marar rabo ya ƙi karɓa, ya aika da labari ga Mut’im ɗan Adiyy. Shi ya karɓi wannan roƙo. Habibi Mafi Daraja, Annabi Mai Girma, ya shiga Makka ƙarƙashin kariyar Mut’im ɗan Adiyy. Mut’im kuma ya sanar wa Ƙuraishawa wannan hali. Manzon Allah ya yi ɗawafin Ɗakin Allah mai daraja, ya sumbaci Hajarul-Aswad. Bayan kwanaki kaɗan ya ce wa Mut’im: “Ba zan ƙara zama a ƙarƙashin kariyarka ba.” Mut’im ma ya karɓi haka. Allah Maɗaukakin Sarki Ya kiyaye HabibinSa a ƙarƙashin kariyarSa.

Ku ce “La ilaha illallah”, ku tsira

Manzo alaihis-salam ya ci gaba da kiran mutane zuwa tafarkin gaskiya. Ganin wannan hali, sai mushrikai suka sake ɓarna, suka fara yin azaba da zalunci fiye da na baya. Sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya umarci Shugabanmu Annabi, a lokacin ziyarar Ka’aba, ya gana da ƙabilun Larabawa da suke zuwa ziyara, ya kira su zuwa Musulunci. Bisa wannan umarni, ƙaunataccen Annabinmu ya fara zuwa kasuwannin Zul-Majaz, Ukaz da Majanna, da ake kafawa a kewayen Makka.

Yakan tafi can akai-akai, ya kira ƙabilu zuwa ga kaɗaitakar Allahu Ta’ala da bauta maSa, ya ce su karɓi cewa shi annabi ne. Yakan sanar da cewa, idan suka karɓa, Allah Maɗaukakin Sarki Zai ba su Aljanna. Waɗannan kirace-kirace, da Shugabanmu Annabi yake yi kusan da roƙo, abin takaici, ba su sami mai saurara ba; wasu suna nuna rashin kunya, suna wulaƙanta shi, wasu kuma suna murtuke fuska, suna faɗar munanan maganganu. Mushrikan Ƙuraishawa ma suna bin sa, suna ɓata ƙabilun da ya je wurinsu.

Bisa abin da Imam Ahmad, Baihaƙi, Ɗabarani da Ibn Is’haƙ suka sanar, Rabi’a ɗan Abbad ya ruwaito kamar haka: “Ina saurayi. Mun tafi Mina tare da ubana. Manzo alaihis-salam yakan isa wurin da ƙabilun Larabawa suka sauka, ya ce: ‘Ya ku ƴaƴan wane! Ni manzon Allahu Ta’ala ne, wanda Yake umartarku da ku yar da waɗannan gumaka da kuke bauta wa, ku bauta wa Allahu Ta’ala ba tare da kun haɗa kome da Shi ba, ku yi imani da ni, ku gaskata ni, ku kare ni har sai na bayyana aikin da Allah Maɗaukaki Ya aiko ni da shi, na aiwatar da shi!…’

Wani mutum mai lauyayyun idanu, mai kitsen gashi, kuwa yana bin sa a baya yana cewa: ‘Ya ku ƴaƴan wane! Wannan yana hana ku bauta wa gumakanmu Lata da Uzza, yana kiran ku zuwa wani addini da ya ƙirƙira da kansa!.. Ku yi hankali! Kada ku saurare shi, kada ku bi shi!..’ Na tambayi ubana: ‘Wane ne wannan da yake bin wannan mutum?’ Ya ce: ‘Baffansa ne, Abu Lahab.’”

Ɗabarani ya ruwaito daga Ɗariƙ ɗan Abdullahi kamar haka: “Na ga Manzo alaihis-salam a kasuwar Zul-Majaz. Domin mutane su ji, yana kira da babbar murya: ’Ya ku mutane! Ku ce “La ilaha illallah” (babu abin bauta sai Allahu Ta’ala), ku tsira!’ Wani mutum kuma yana bin sa, yana jefa duwatsun da suka faɗa hannunsa a ƙafafunsa, yana cewa: ‘Ya ku jama’a! Kada ku yi imani!.. Ku yi hankali da shi! Domin shi maƙaryaci ne!..’ Har duwatsun da suka same shi sun zubar da jinin ƙafafunsa masu albarka, amma shi har yanzu yana ci gaba da kiransa, ba tare da karaya ko gajiya ba. Suka tambaya: ‘Wane ne wannan saurayi?’ Wani ya amsa: ‘Saurayi ne daga Banu Abdulmuɗɗalib.’ Da suka tambaya: ‘Wane ne mai jifan?’, ya ce: ‘Baffansa ne, Abu Lahab.’”

Imam Bukhari a cikin “Tarikhul-Kabir” nasa, da Ɗabarani a cikin “Mu’jamul-Kabir” nasa, sun ambata: Mudrik ɗan Munib ya ruwaito daga ubansa, shi kuma daga kakansa, ya ce: “Mun zo Mina tare da ubana, muka sauka. Muka haɗu da wata jama’a. Wani mutum yana ce musu: ‘Ya ku mutane! Ku ce La ilaha illallah, ku tsira!’ Daga cikin mutanen da suke kewaye da shi, wasu suna tofa masa yawu a kyakkyawar fuskarsa, wasu suna zuba masa ƙasa a kansa, wasu kuma suna zaginsa, suna wulaƙanta shi iri-iri. Wannan hali ya ci gaba har zuwa azahar. A lokacin wata yarinya ta zo wurin da tulun ruwa a hannunta. Da ta gan shi a wannan hali, ta fara kuka. Wannan mutum, bayan ya sha ruwa, ya juya ga yarinyar ya ce: ‘Ya ƴata! Kada ki ji tsoron cewa za a sa wa ubanki tarko a kashe shi, ko a ƙasƙantar da shi!’ Sannan muka tambayi waɗanda suke wurin: ‘Wane ne wannan mutum, wace ce kuma wannan yarinya?’ Suka ce: ‘Wannan Muhammadu ne, daga Banu Abdulmuɗɗalib, wadda take kusa da shi kuma ƴarsa ce, Zainab.’”

“Shi (Yunusa alaihis-salam) ɗan’uwana ne. Shi ma annabi ne kamar ni” Hadisi mai daraja

Sa’id ɗan Yahaya ɗan Sa’id al-Umawi, a cikin “Maghazi” nasa, ya ruwaito daga ubansa. Shi kuma daga Abu Nu’aim da Abdurrahman Amiri, shi kuma daga mutane da yawa ya ruwaito. Suka ce: Wata rana ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) ya tafi kasuwar Ukaz. Ya isa wurin ƙabilar Banu Amir, ya tambaye su: “Ya Banu Amir! Yaya kariyarku take ga waɗanda suka nemi mafaka a wurinku?” Suka ce: “Babu wanda zai iya faɗa mana wata magana, babu wanda zai iya jin ɗumin wutarmu ba tare da saninmu ba!..” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ni manzon Allahu Ta’ala ne. Idan na zo wurinku, za ku kare ni har sai na isar wa mutane aikin annabta da Ubangijina Ya ba ni?” Suka tambaya: “Kai daga wane gida na Ƙuraishawa kake?” Da Shugabanmu ya ce: “Daga Banu Abdulmuɗɗalib”, suka ce: “Tun da kai daga Banu Abdulmuɗɗalib kake, don me su ba sa kare ka?” Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Su ne suka zama na gaba a cikin masu ƙaryata ni.” Jama’ar Banu Amir suka ce: “Ya Muhammadu! Mu ba ma ƙin ka, ba ma kuma yin imani da abin da ka kawo. Amma za mu kare ka har sai ka isar wa mutane aikin annabtarka.”

Sai Shugabanmu Annabi ya zauna a wurinsu. A lokacin Baihara ɗan Faris, ɗaya daga cikin manyan Banu Amir, da ya gama cinikinsa a kasuwa, ya zo wurinsu, ya nuna Shugabanmu Annabi ga waɗanda suke wurin, ya tambaya: “Wane ne wannan?” Suka ce: “Muhammadu ɗan Abdullahi ne.” Da Baihara ya ce: “Me ya haɗa ku da shi, har kuka zaunar da shi a wurinku?”, suka ce: “Ya nemi mafaka a wurinmu, yana cewa shi manzon Allah ne, kuma yana son mu kare shi har sai ya isar wa mutane aikin annabta.” Sai Baihara ya juya ga Shugabanmu Annabi, ya ce: “Mu ɗauki nauyin kare ka yana nufin mu sa ƙirjinmu abin nufi ga kibiyoyin dukkan Larabawa.” Ga mutanensa kuma ya ce: “Babu wata ƙabila da za ta koma ƙasarta da abu mafi muni fiye da ku. Ashe za ku yaƙi dukkan Larabawa, ku sa jikinku abin nufi ga kibiyoyinsu, haka ne!.. Da mutanensa sun ga wani alheri a gare shi, da su da kansu sun fara kare shi. Ku kuna ɗaukar nauyin ba wa mutumin da mutanensa suka ƙaryata, suka kore shi daga wurinsu mafaka, ku taimake shi!.. Kun yi babban kuskuren tunani!…”

Sannan wannan shaƙiyi ya juya ga ƙaunataccen Annabinmu, ya ce: “Ka fice daga cikinmu nan take, ka koma wurin mutanenka!.. Na rantse, da ba a cikin mutanena kake ba, da yanzun nan na sare wuyanka!..” Bayan waɗannan maganganu, Shugaban Talikai, cikin babban baƙin ciki, ya hau raƙuminsa. Wannan Baihara mai rashin kunya ya faɗar da Shugabanmu Manzon Allah daga raƙuminsa. Wata mace daga cikin Sahabbai masu girma mai suna Duba’a ƴar Amir, da ta ga wannan al’amari, ta yi kururuwa, ta kira danginta: “Yaya kuke ganin ya dace a yi wa Habibin Allahu Ta’ala wannan abu? Shin babu wanda zai ceto Manzon Allah daga hannun waɗannan saboda ni?” Mutum uku daga cikin ƴaƴan baffanta nan take suka tunkari Baihara marar rabo. Mutum biyu daga mutanen Baihara suka so su taimake shi, amma waɗancan suka wulaƙanta Baihara da mataimakansa, suka doke su. Ƙaunataccen Annabinmu, wanda yake bibiyar wannan hali, ya yi addu’a ga waɗancan mutum uku da suka yi faɗa dominsa: “Ya Ubangijina! Ka ba waɗannan mutane albarkarKa!”, ga Baihara da mataimakansa kuma: “Ya Ubangijina! Ka nisanta waɗannan daga rahamarKa!”

Waɗanda ya yi musu addu’ar alheri suka sami darajar zama Musulmi, sauran kuma suka mutu kafirai. Mutanen ƙabilar Banu Amir, da suka koma ƙasarsu, suka ba wani tsoho na ƙabilarsu, wanda ya karanta littattafan sama, labarin abin da ya same su a Makka. Wannan mutum, da ya ji sunan Shugabanmu Annabi, ya zarge su yana cewa: “Ya Banu Amir! Me kuka yi? Babu ɗaya daga cikin ƴaƴan Isma’ila da ya taɓa yin da’awar annabta ta ƙarya har zuwa yau. Lalle, abin da ya faɗa gaskiya ne kuma haƙƙi ne. Wannan dama da aka rasa, yanzu gyara ta yana da wuya ƙwarai!..”

Yana zance da Jibrilu a lokacin,
Rafraf ta zo gabansa, ta yi sallama.
Ta ɗauki wancan sarkin duniya nan take,
Ta tafi Sidra, ta kai shi can da gaggawa.

“Ya ku mutane! Ku ce La ilaha illallah, ku tsira!” Hadisi mai daraja

Isra’i da Mi’iraji