Ƙaunataccen Annabina

SHEKARAR BAƘIN CIKI

Raɗaɗin rashin ƴaƴa

Babban ɗan Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam), Ƙasim, ya rasu yana da wata goma sha bakwai. Shekaru bayan wannan al’amari mai raɗaɗi, ɗayan ɗansa, Abdullahi, shi ma ya rasu. Shugabanmu Manzon Allah, hawaye suna zuba daga idanunsa masu albarka, ya juya ga dutse ya ce: “Ya dutse! Da abin da ya same ni ya same ka, da ba za ka iya jurewa ba, da ka rushe!”, ya bayyana baƙin cikinsa haka. Ga tambayar uwarmu Nana Khadija: “Ya Manzon Allah! Ina suke yanzu?”, ya amsa: “Suna cikin Aljanna.”

Da ƴaƴa biyu na Sarkin Halittu, ƙaunataccen Annabinmu, suka rasu, mushrikai suka yi farin ciki ƙwarai. Kafirai irin su Abu Jahal, suka ɗauki wannan a matsayin dama, suka yi ta hayaniya a ko’ina: “Yanzu Muhammadu abtar ne, zuriyarsa ta yanke. Ba shi da ɗa namiji da zai ci gaba da zuriyarsa. Idan shi ma ya mutu, sunansa da ambatonsa za a manta da su.”

Sai Allahu Ta’ala Ya saukar da Suratul Kausar, Ya ta’azantar da ManzonSa. A ma’ana: “(Ya MasoyiNa!) Haƙiƙa, Mun ba ka Kausar (tafkin Kausar, alheri mai yawan gaske). To, ka yi salla saboda Ubangijinka, ka yi yanka.. Haƙiƙa, wanda ba shi da alheri kuma zuriyarsa ta yanke, shi ne wanda yake zunɗen ka (yana cewa zuriyarka ta yanke). (Wanda yake kiranka abtar, shi da kansa ba shi da zuriya, ba shi da daraja, ba shi da ambato. Kai kuwa, ya MasoyiNa, zuriyarka tsarkakiya, ɗaukakarka da darajarka za su ci gaba har zuwa Ranar Ƙiyama. A Lahira ma an keɓe maka manyan darajoji da yawa da hankali ba zai iya tsammani ba.)”1

Rasuwar Abu Ɗalib

A kwanakin da suka biyo bayan rasuwar ƴaƴan Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), Abu Ɗalib ya kamu da rashin lafiya, kuma kowace rana rashin lafiyarsa yana ƙaruwa. Mushrikan Ƙuraishawa, da suka ji wannan, suka yi tunani: “Abu Ɗalib, a lokacin da yake raye, ya yi ƙoƙari ƙwarai wajen kare Muhammadu. Yanzu lokacin tafiyarsa daga wannan duniya ya kusa. Mu je mu ziyarce shi, ko da a lokacinsa na ƙarshe ne. Domin Hamza, jarumin Larabawa mara tamka, da Umar, wanda ƙarfinsa, jaruntakarsa da rashin tsoronsa suke bayyane kamar rana, su ma sun musulunta. Kowace rana mutane suna zuwa daga ƙabilun Larabawa, suna bin sa ƙungiya-ƙungiya. Ta haka Musulmi suna ƙaruwa kullum, muryarsu tana cika duniya. A wannan hali, ko mu bi su, ko kuwa mu shirya yaƙi da faɗa. Mu je wurin Abu Ɗalib, mu bayyana masa halin da ake ciki, ya sasanta tsakaninmu. Kada mu kai hari ga addininsa, shi ma kada ya kai hari ga addininmu.” Da wannan tunani suka zo wurin Abu Ɗalib. Sanannun mutane irin su Uƙba, Shaiba, Abu Jahal da Umayya ɗan Khalaf suka zauna a kan matasan da suke kusa da gadon Abu Ɗalib. Suka ce: “Mun yi imani da girmanka, mun yarda da fifikonka. Saboda haka ba mu taɓa saɓa maka ba. Muna tsoron kada, bayan ka mutu, Muhammadu ya yi ta faɗa da mu, ƙiyayya ta ci gaba a tsakaninmu. Ka sasanta mu, kada mu kai wa addinin juna hari.”

“Ya dutse! Da abin da ya same ni ya same ka, da ba za ka iya jurewa ba, da ka rushe!” Hadisi mai daraja

Hubbaren uwarmu Nana Khadija / Jannatul-Mu’alla

Kamar kaburburan manyan Musulunci da yawa, ƙubbar matar farko ta ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu ta’ala alaihi wa sallam), uwarmu Nana Khadija (radiyallahu anha), ita ma an rushe ta, an kawar da ita.

Abu Ɗalib ya sa aka kira Shugabanmu Annabi, ya ce: “Dukkan manyan Ƙuraishawa suna roƙonka kada ka tsoma baki a cikin addininsu. Idan ka karɓi wannan, za su yi aiki a ƙarƙashin umarninka, su zama mataimakanka.” Shugaban Talikai ya ce: “Ya baffa! Ni ina son in kira su zuwa ga kalma guda kawai; da wannan kalma dukkan Larabawa za su miƙa musu wuya, waɗanda ba Larabawa ba kuma za su biya musu jizya.” Ga manyan Ƙuraishawa ma ya ce: “E! Idan kuka faɗa mini kalma guda, da ita za ku mallaki dukkan Larabawa, waɗanda ba Larabawa ba ma za su miƙa muku wuya.” Abu Jahal ya ce: “To. Za mu faɗe ta sau goma. Wace kalma ce ita?” Da Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Idan kuka ce ‘La ilaha illallah’, kuka kuma kawar da gumakan da kuke bauta wa baicin Allahu Ta’ala, kuka yar da su”, mushrikai nan take suka ce: “Ka nemi wani abu daban daga gare mu, ba wannan ba!…” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ko da kun kawo rana kun sa ta a hannuwana, ba zan nemi wani abu daga gare ku ba sai wannan.”

Mushrikai suka ce: “Ya Abul-Ƙasim! Kana gabatar da wata shawara mai ban mamaki. Mu muna son mu kiyaye haƙƙinka; kai kuwa ba ka kiyaye namu!” Suka tashi suka tafi. Da suka tafi, Abu Ɗalib ya ce wa Shugabanmu Annabi: “Abin da ka nema daga Ƙuraishawa ya dace sosai. Gaskiya ka faɗa.” Wannan magana ta baffansa ta ba Shugabanmu Manzon Allah fata, ya fahimci cewa Abu Ɗalib zai iya yin imani, sai ya ce: “Ya baffa! Ka ce ‘La ilaha illallah’ sau ɗaya kawai!.. Domin in yi maka ceto a Ranar Ƙiyama.” Abu Ɗalib ya ce: “Ina tsoron kada mutane su zarge ni su ce: ‘Ya ji tsoron mutuwa ne, shi ya sa ya musulunta.’ In ba haka ba, da na kiyaye haƙƙinka”, ya bayyana cewa hakan ya yi wa ransa nauyi. Da rashin lafiyarsa ta ƙara tsananta, sai ya rasu.2

Rasuwar uwarmu Nana Khadija

A shekara ta goma ta bi’isa, kwana uku bayan rasuwar Abu Ɗalib, abokiyar baƙin cikin Shugabanmu Manzon Allah, abokiyar rayuwarsa ta shekara ashirin da biyar, uwarmu Nana Khadija mai albarka, ita ma, bayan kewayen shekara uku da ya wuce cikin baƙin ciki da damuwa, shekara uku kafin Hijira, a farkon watan Ramadan, ta rasu tana da shekara 65.3 Abin Alfaharin Halittu (sallallahu alaihi wa sallam) ya binne uwarmu Nana Khadija da hannuwansa masu albarka. Ya yi baƙin ciki ƙwarai saboda rabuwa da ita.

Rasuwar uwarmu Nana Khadija da baffansa Abu Ɗalib bi da bi a cikin shekara guda ta nutsar da Shugabanmu Annabi cikin baƙin ciki. Saboda haka aka kira wannan shekara “Sanatul-Huzn”, wato shekarar baƙin ciki.

Rasuwar uwarmu Nana Khadija ta girgiza ƙaunataccen Annabinmu, ta sa shi baƙin ciki fiye da kima. Domin ita ce ta fara yin imani, ta gaskata Shugabanmu Manzon Allah. Bugu da ƙari, ita ce babbar madogararsa kuma mai ta’azantar da shi. Lokacin da kowa yake maƙiyi, ita ta buɗe zuciyarta gaba ɗaya, ta cika da ƙaunar Annabinmu. Ta kashe dukkan dukiyarta da arzikinta, duk abin da take da shi, a tafarkin Musulunci; ta haɗa darenta da ranarta domin ta yi wa ƙaunataccen Annabinmu hidima. Ba ta taɓa sa Manzon Allah baƙin ciki ba, ba ta taɓa ɓata masa rai ba. Shugabanmu Annabi yakan faɗi wannan lokaci-lokaci, ta haka yake tuna falalolin matarsa mai albarka.

“Ya baffa! Ka ce ‘La ilaha illallah’ sau ɗaya kawai!.. Domin in yi maka ceto a Ranar Ƙiyama” Hadisi mai daraja

Wata rana, lokacin da Annabinmu yake waje, Nana Khadija ta fita domin ta neme shi. Jibrilu alaihis-salam ya bayyana ga Nana Khadija a siffar mutum. Uwarmu Nana Khadija ta so ta tambaye shi Shugabanmu Annabi, amma da ta yi tunanin cewa yana iya kasancewa ɗaya daga cikin maƙiya, sai ta koma. Da ta ga ƙaunataccen Annabinmu a gida, ta ba shi labarin abin da ya faru. Abin Alfaharin Halittu ya ce: “Kin san ko wane ne wancan mutumin da kika gani, kika so ki tambaye shi labarina? Jibrilu (alaihis-salam) ne. Ya ce in isar miki da sallamarsa. Ya kuma ce in sanar miki da wannan: a Aljanna an shirya miki wani gini da aka yi da lu’ulu’u. Tabbas a can ba za a sami abubuwa masu baƙin ciki, ƙunci, wahala da nauyi irin na nan ba.”

Hannun ɗaya ya tsaya cik a sama, ɗayan ya makance

Ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam) yakan yi wa Sahabbansa, waɗanda suke daga cikin mafi sa’ar mutane, zantuttuka marasa misali, ya haskaka zukatansu. Yakan bayyana ayoyi masu girma da aka saukar, ba ya barin kome ba tare da an faɗe shi, an fahimce shi ba. A wannan lokaci kuma, domin mushrikai ma su yi imani, yakan tafi wuraren da suke taruwa, ya kira su zuwa ga imani ba tare da gajiya ko karaya ba. Abu Jahal da Walid ɗan Mughira suna fushi ƙwarai da wannan, suna cewa: “Idan haka ta ci gaba, Muhammadu zai juya kowa zuwa addininsa, ba zai bar wanda yake bauta wa gumakanmu ba.” Wata rana suka yanke shawarar cewa hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen wannan al’amari ita ce kashe ƙaunataccen Annabinmu, Shugaban Talikai. Abu Jahal ya ɗauki Walid ɗan Mughira da wasu samari daga Banu Makhzum tare da shi, ya zo Ɗakin Allah. A lokacin ƙaunataccen Annabinmu yana salla. Abu Jahal, da wani dutse a hannunsa, ya fito gaba nan take. A lokacin da ya ɗaga hannunsa domin ya bugi Habibi Mafi Daraja, Annabi Mai Girma, da dutsen, sai hannuwansa suka tsaya cik a sama, ba motsi. Bai iya yin kome ba, ya rikice. A haka ya koma inda ya fito. Da ya isa wurin mushrikai, hannunsa ya koma yadda yake, dutsen ya faɗi ƙasa. Ɗaya daga cikin Banu Makhzum ya ƙwace wannan dutse, ya ce: “Za ku gani! Ni zan kashe shi!..”, ya nufi Shugabanmu Annabi. Da ya kusanto, nan da nan idonsa ya makance, ya kasa ganin kewayensa. Sai Banu Makhzum gaba ɗaya suka tunkari ƙaunataccen Annabinmu tare. A lokacin da suka kusanci Shugabanmu Annabi sosai, suka kasa ganinsa. Amma suna jin muryarsa mai albarka. Idan suka nufi inda muryar take fitowa, sai muryar ta fito daga bayansu; idan suka juya baya, sai ta sake fitowa daga wurin farko. Suka shaidi wannan hali sau da yawa. A ƙarshe suka rikice, suka bar wurin ba tare da sun iya yi wa Shugabanmu Manzon Allah kome ba.

Alƙawarin auren Nana A’isha da Nana Sauda

Da Nana Khadija (radiyallahu anha) ta rasu, ba a sami wanda zai kula da gidan Manzon Allah ba. Nana Khaula ƴar Hakim, da ta ga wannan hali, ta tafi gaban Jagoran Talikai. Ta ce: “Ya Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)! Kana buƙatar abokiyar zama da ta dace da kai, da mata da ta cancanci hidimarka. Idan ka so, in nema maka mata.” Manzon Allah ya ce: “Ya Khaula, ina ake samun matar da ta cancanci wannan hidima?” Khaula ta ce: “Idan kana son budurwa, ita ce A’isha, ƴar abokinka Abubakar. Idan kana son bazawara, Sauda ƴar Zam’a ta dace.” Manzo alaihis-salam ya ce: “Ki nema mini su biyun.” Manzon Allah ya fara ɗaura alƙawarin aure da Nana A’isha, sannan da Sauda. Ya ɗauki Nana Sauda zuwa gidansa a Makka. Bikinsa da Nana A’isha ya kasance a Madina, a watan Shawwal na shekara ta biyu bayan Hijira.

Ganawar Aƙaba

Ƙaunataccen Annabinmu, a kowace shekara, yakan kira ƙabilun da suke zuwa ziyarar Ka’aba zuwa ga addini, yana ƙoƙari su tsira daga wutar Jahannama, su sami farin ciki na har abada, kuma ba tare da ya kula da kowane irin wulaƙanci ba, yakan ci gaba da aiwatar da aikin annabta. Yakan tsaya a wuraren sauka na ƙabilu, ya ce wa masu zuwa: “Wane ne zai ba ni mafaka, ya taimake ni, har sai na aiwatar da aikin annabta da Allahu Ta’ala Ya ɗora mini? (Ta haka) a ba shi Aljanna.” Amma ba a sami wanda zai ba da mafaka, ko wanda zai taimaka ba.

Watan Zulhijja ne na shekara ta goma ta bi’isa. Shugabanmu Annabi, a kasuwa, ya haɗu da wani gungun mutanen Madina da suka zo ziyarar Ka’aba. Da ya tambaye su: “Su wane ne ku?”, suka ce mutanen Madina ne, daga ƙabilar Khazraj. Nana Salma, uwar Abdulmuɗɗalib, kakan Annabinmu, ita ma daga reshen Banu Najjar na ƙabilar Khazraj take. Annabinmu ya zauna da waɗannan mutum shida na Khazraj a Aƙaba na ɗan lokaci, ya karanta musu ayoyi masu girma na 35 zuwa 52 na Suratu Ibrahim, ya bayyana musu Musulunci. Ya kira su su shiga wannan addini.

A Madina, tun da daɗewa ƙabilun Aus da Khazraj maƙiyan Yahudawa ne, duk lokacin da suka sami dama sukan kai wa juna hari. Duk lokacin da wani faɗa ya faru a tsakaninsu, Yahudawa sukan ce: “Nan ba da daɗewa ba wani annabi zai zo. Ba a daɗe ba, yau ko gobe zai bayyana. Za mu bi shi, mu sami ƙarfi. Ku ma za mu yi muku gwargwadon abin da ya kamace ku.” Mutanen Aus da Khazraj kuwa sun yarda cewa, idan suka musulunta kafin Yahudawa, suka sami darajar Musulunci, za su rinjaye su, su fitar da su daga Madina.

Waɗannan mutane masu rabo, da suka ji daga manyan ƙabilarsu da kuma Yahudawan da suke zaune a Madina cewa wani annabi zai zo ba da daɗewa ba, suka ga alamomin annabta a jikin Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam). Da ya kira su zuwa ga addini, suka kalli juna. Sannan suka ce a tsakaninsu: “Annabin da Yahudawa suka ba da labarinsa, ga shi nan!”

Saboda haka nan take suka faɗi kalmar shahada a gaban Manzon Allah, suka musulunta. Suka ce wa Shugabanmu Annabi: “Ya Manzon Allah! Mun bar mutanenmu suna yaƙi da Yahudawa. Muna fatan Allahu Ta’ala Ya ba su ma darajar imani ta sanadinka. Da zarar mun koma, za mu kira su da mutanenmu su karɓi annabtarka. Abubuwan da muka karɓa na wannan addini za mu faɗa musu su ma. Idan Allahu Ta’ala Ya tara su, Ya haɗa su a kan wannan addini, babu wanda zai fi ka daraja da girma.”

Waɗannan mutum shida sun yi imani da gaske, sun karɓa, sun gaskata abin da Allahu Ta’ala Ya isar wa Annabinmu.

“Wane ne zai ba ni mafaka, ya taimake ni, har sai na aiwatar da aikin annabta da Allahu Ta’ala Ya ɗora mini? (Ta haka) a ba shi Aljanna” Hadisi mai daraja