Ƙaunataccen Annabina

SAMARTAKARSA DA AURENSA

Samartakarsa

Muhammadu alaihis-salam, mafi ɗaukakar mutane ta kowace fuska, tun a shekarun samartakarsa mutanen Makka sun fi son sa a kan tsararsa ƙwarai. An so shi saboda kyawawan ɗabi’unsa, kyakkyawar mu’amalarsa da mutane irin wadda ba a taɓa gani ba, nutsuwarsa, sanyin halinsa da sauran halayensa masu ɗaukaka. Mutane suna sha’awarsa saboda waɗannan halaye. Saboda gaskiyar magana da amana masu ban mamaki da suka gani a tattare da shi, mutanen Makka suka ba shi laƙabin “al-Amin”, wato “wanda ake amincewa da shi koyaushe”. Ta haka ya shahara da wannan suna tun a samartakarsa.

A shekarun samartakar Annabinmu, Larabawa suna cikin tsananin Zamanin Jahiliyya (jahilci). Bautar gumaka, shan giya, caca, zina, riba da wasu munanan ayyuka da yawa sun bazu a tsakaninsu. Muhammadu alaihis-salam yana ƙyamar waɗannan ɓatattun halayensu ƙwarai, koyaushe yana nisantar kowane sharrinsu. Dukkan mutanen Makka sun san wannan halinsa, suna mamaki. Saboda tsananin ƙyamar gumaka, bai taɓa kusantarsu ba ko kaɗan. Bai taɓa cin naman dabbobin da aka yanka wa gumaka ba. A yarintarsa da samartakarsa yakan yi kiwon tumakinsa a dutsen Jiyad da kewayensa, ta haka yake samun abin rayuwarsa. Ta haka yake nisantar wannan al’umma da ta lalace ƙwarai. Wata rana ya ce wa Sahabbai masu girma: “Babu wani annabi da bai yi kiwon tumaki ba.” Da suka ce: “Ya Manzon Allah! Kai ma ka yi kiwo?”, sai ya ce: “I, ni ma na yi kiwo.”

Lokacin da ƙaunataccen Annabinmu yake kusan shekara ashirin, zaman lafiya a Makka ya lalace gaba ɗaya. Zalunci ya bazu ƙwarai; babu sauran amincin dukiya, rai da mutunci. Mutanen Makka na asali suna zalunci da rashin adalci ga baƙin da suka zo kasuwanci da ziyartar Ka’aba. Waɗanda aka zalunta ba sa samun wurin da za su kai ƙara domin su karɓi haƙƙinsu. A lokacin wani mutumin Makka mai suna As ɗan Wa’il ya ƙwace da ƙarfi kayan wani ɗan kasuwa na Yaman, wanda ya zo Makka domin kasuwanci. Bayan haka mutumin Yaman ya hau dutsen Abu Ƙubais, yana kururuwa, ya nemi taimakon ƙabilu domin a karɓo masa haƙƙinsa. Bayan irin waɗannan al’amura, waɗanda suke nuna cewa zalunci ya kai iyakarsa, manyan ƴaƴan Hashim, ƴaƴan Zuhra da na sauran ƙabilu suka taru a gidan Abdullahi ɗan Jud’an. Suka yanke shawarar cewa ba za a yi wa kowa zalunci da rashin adalci ba, ɗan gari ne ko baƙo, za a hana zalunci, kuma za a karɓo wa waɗanda aka zalunta haƙƙoƙinsu. Da wannan manufa suka kafa ƙungiyar adalci.1

Wannan ƙungiya, wadda ƙaunataccen Annabinmu ya shiga tun yana ɗan ƙarami kuma ya ba da babbar gudummawa wajen kafa ta, ana kiranta Hilful-Fudul.

Kafin haka, wasu mutane biyu masu suna Fadl da wani mai suna Fudail ma sun kafa irin wannan ƙungiya. An sa mata wannan suna ne saboda ƙungiyar da su suka kafa a baya.

“Muhammadu alaihis-salam, wanda duniya baki ɗaya ta tabbatar da irin cikakken mutumin da yake, saboda tsananin gaskiyarsa da amincinsa, har manyan maƙiyansa, kafirai ɓatattu, suna kiransa Muhammadul-Amin (Muhammadu amintacce)” Hüseyin Hilmi bin Sa’îd (rahmatullahi alaihi)

Shahararrun bukukuwan kasuwanci da kasuwannin Ƙasar Larabawa da kewayenta

Mutum rabonsa yakan zo masa,
Ba a barin baƙo da hannu wofi.
Me ran Eyyübî zai yi,
Idan masoyin ransa bai yi murna ba?
Sarkina, Habib na Allah Mai girma,
Fuskarka maganin kowane ciwo ce.
Yaya za a cika alkawari gare ka,
In masoyi bai ba da ransa ba?

Wannan ƙungiya ta hana zalunci, ta sake kafa zaman lafiyar da ya lalace a Makka. Tasirinta ya daɗe na dogon lokaci. Bayan an sanar da shi annabta, Shugabanmu Manzon Allah ya ba Sahabbai masu girma labarin wannan, ya ce: “Ni ma na halarci rantsuwar da aka yi a gidan Abdullahi ɗan Jud’an. Na fi son wannan rantsuwa fiye da mallakar raƙuma masu jan gashi (dukiya). Ko a yanzu, da an kira ni zuwa irin wannan taro, da na amsa.”2

Sana’arsa ta kasuwanci

Mutanen Makka tun da daɗewa suna sana’ar kasuwanci, ta haka suke samun abin rayuwarsu. Baffan Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam), Abu Ɗalib, shi ma yana kasuwanci. Lokacin da ƙaunataccen Annabinmu yake kusan shekara ashirin da biyar, wahalar rayuwa a Makka ta ƙaru ƙwarai. Saboda haka mutanen Makka suka shirya wani babban ayarin kasuwanci domin zuwa Sham. A kwanakin nan Abu Ɗalib ya zo wurin Shugabanmu Manzon Allah ya ce: “Ya ɗan ɗan’uwana mai daraja! Talauci ya kai iyakarsa. Waɗannan shekaru na ƙarshe da muka shafe cikin yunwa da fama ba su bar mana kome a hannu ba. Ga shi, an shirya ayarin Ƙuraishawa, yana gab da tashi zuwa Sham. Nana Khadija ma za ta aika da kaya tare da ayarin. Babu shakka tana neman amintattun mutanen da za su yi wannan aiki. Lalle tana buƙatar mutum amintacce, mai tsabta kuma mai cika alkawari irinka. Zai yi kyau mu je mu yi magana da ita, mu sa ka tafi a matsayin wakilinta. Babu shakka za ta fifita ka a kan waɗansu. A gaskiya ba na son ka tafi Sham, domin ina tsoron kada Yahudawan da suke can su cutar da kai. Amma ban sami wata mafita ba.” Shugabanmu Annabi ya ce masa: “Ka yi yadda kake so.”

Nana Khadija mace ce mai babbar shahara a Ƙasar Larabawa da kyanta, dukiyarta, hankalinta, kamun kanta, kunyarta da ladabinta. Saboda haka akwai mutane da yawa daga kowane ɓangare da suke neman aurenta, suke kwaɗayinta. Amma saboda wani mafarki da ta gani, ba ta kula da kowa ba. A mafarkinta, wata ya sauko daga sama ya shiga ƙirjinta, nurin watan ya fito daga hammatarta ya haskaka dukkan talikai. Da safe ta ba ɗan’uwanta Waraƙa ɗan Naufal labarin wannan mafarki. Waraƙa ya ce: “Annabin ƙarshen zamani ya riga ya zo duniya. Zai aure ki, kuma a zamaninki wahayi3 zai sauko masa. Nurin addininsa zai cika talikai. Ke ce za ki fara yin imani da shi. Wannan Annabi daga Ƙuraishawa ne, daga Banu Hashim.”

Nana Khadija ta yi farin ciki ƙwarai da wannan amsa, ta fara jiran zuwan wannan Annabi.

Nana Khadija tana kasuwanci, tana haɗin gwiwa da mutanen da ta yi yarjejeniya da su. Abu Ɗalib ya ba uwarmu Nana Khadija labarin al’amarin. Bayan haka Nana Khadija ta gayyaci Shugabanmu Manzon Allah gidanta domin ta gan shi, ta yi magana da shi.

Da ya zo, ta tarbe shi da girmamawa mai yawa. Da ta ga ladabin Shugabanmu Annabi da fuskarsa tsarkakakkiya, mai tsabta, ta cika da sha’awa. Ta ce wa Shugabanmu Manzon Allah: “Na san cewa kai mai gaskiya ne, amintacce, abin dogaro kuma mai kyawawan ɗabi’u. Saboda wannan aiki zan ba ka ninkin ladan da ban taɓa ba wa kowa ba…” Bayan an tattauna adadin ladan kuma, uwarmu Nana Khadija ta ba Manzon Allah tufafin da za su zama dole a wannan hidima, ta yi masa rakiya daga gidanta cikin nutsuwar zuciya. Ban da haka, ta ba Maisara wasu tufafi masu daraja kuma domin Manzon Allah ya sa a hanya.

“Idan Musulmi ya nemi abin rayuwa na halal, bai zama mabuƙaci ga kowa ba, kuma ya taimaki maƙwabtansa da danginsa, a Ranar Ƙiyama zai zama mai haske, mai nuri kamar watan dare na goma sha huɗu” Hadisi mai daraja

Uwarmu Nana Khadija ta koyi alamomin annabta daga ɗan baffanta Waraƙa ɗan Naufal, Kirista masani. A wannan zuwan Shugabanmu Manzon Allah ma ta gane siffofin annabta a tattare da shi. Saboda haka ta ce wa bawanta mai suna Maisara: “Lokacin da ayari zai bar Makka, ka ba Muhammadu alaihis-salam ragamar raƙumi a hannunsa, domin mutanen Makka kada su yi wata gulma. Da kuka nisanci birni, ya ɓace daga gani, ka sa masa waɗannan tufafi masu daraja.”

Sannan ta ƙawata mafi kyawun raƙumanta yadda ya cancanci sarakuna, ta ce wa Maisara: “Ka hau shi a kan wannan raƙumi da babbar girmamawa, ka riƙe ragamar a hannunka, kuma ka ɗauki kanka a matsayin mai hidimarsa! Kada ka yi wani aiki ba tare da izininsa ba, kuma kada ka ji wa ranka tsoro wajen kare shi da tsare shi daga haɗari! A wuraren da kuka je kada ku daɗe, ku dawo da sauri, domin kada mu sha kunya a wurin ƴaƴan Hashim. Idan ka aiwatar da abin da na faɗa maka daidai yadda na faɗa, zan ƴanta ka, in ba ka dukiya gwargwadon abin da kake so.”

Aka shirya ayarin. Mutanen Makka suka taru jama’a-jama’a domin su yi bankwana da na kusa da su. Dangin ƙaunataccen Annabinmu, baffanninsa da manyan ƴaƴan Hashim ma suna nan. Lokacin da gwaggon Annabinmu ta ga Manzon Allahu Ta’ala (sallallahu alaihi wa sallam) cikin tufafin mai hidima, yana riƙe da ragamar raƙumi a hannunsa, sai gwiwoyinta suka yi sanyi. Ta yi kuka, ta yi kururuwa. Tana nishi, hawaye suna zuba daga idanunta, ta bayyana raɗaɗinta kamar haka: “Ya Abdulmuɗɗalib! Ya babban mutumin da ya haƙa rijiyar Zamzam! Ya Abdullahi! Ku tashi daga kaburburanku, ku juyo da kawunanku wannan gefe, ku ga halin da wannan mai albarka yake ciki!” Abu Ɗalib ma yana cikin irin wannan ji da irin wannan hali. Hawaye kamar lu’ulu’u suka zubo daga idanun Shugabanmu Manzon Allah masu albarka, waɗanda suke ganin Gaskiya, ya ce: “Kada ku manta da ni. Ku tuna cewa ina shan baƙin ciki da damuwa a ƙasar baƙunta.” Dukkan waɗanda suka ji waɗannan maganganu suka yi kuka. Mala’ikun sama ma suka shiga cikin wannan hali, suka ce: “Ya Ubangijinmu! Wannan Muhammadu alaihis-salam ne, wanda Ka riƙe habibinKa, Ka ba shi mafi girman matsayi. Mene ne hikimar wannan hali?” Allahu Ta’ala Ya ce musu: “I, shi HabibiNa ne. Amma ku ba za ku iya sanin sirrin ƙauna ba. Ba za ku iya fahimtar sirrikan da suke tsakanin ƙaunatacce da mai ƙauna ba. Babu wanda ya san wannan matsayi. Babu wanda ya fahimci kome daga wannan al’amari ɓoyayye.”

A ƙarshe, da ayarin ya tashi, Makka ta ɓace daga gani, Maisara, bisa umarnin da aka ba shi, ya sa wa ƙaunataccen Annabinmu tufafin nan masu daraja. Ya hau shi a kan raƙumin da aka rufe da yadudduka iri-iri, aka ƙawata ƙwarai. Ragamar kuwa ya riƙe ta a hannunsa.

A wannan tafiya, waɗanda suke cikin ayarin suka ga wani girgije yana yi wa ƙaunataccen Annabinmu, wanda aka aiko rahama ga talikai, inuwa a bisansa, da kuma mala’iku biyu a siffar tsuntsaye, suna tafiya tare da shi har zuwa ƙarshen tafiyar.4

A hanya, da ya shafa ƙafafun raƙuma biyu da suka gaji har suka kasa tafiya, suka rage a bayan ayarin, da hannunsa mai albarka, sai raƙuman suka yi sauri farat ɗaya. Da suka ga wannan da wasu al’amura da yawa irinsa, suka ƙaunace shi ƙwarai, suka fahimci cewa darajarsa za ta zama mai girma ƙwarai.

Da suka isa wurin da ake kira Busra, suka sake sauka kusa da gidan ibadar da yake can. Ruhubani Bahira, wanda ya fahimta daga alamomi da yawa da ya gani cewa shi zai zama annabi na ƙarshe, ya kuma faɗi haka, ya mutu, a gurbinsa kuma wani ruhubani mai suna Nasɗura ya zauna. Ruhubani Nasɗura, wanda yake kallon ayarin Ƙuraishawa da ya zo ya sauka kusa da gidan ibadar, da ya ga wani mutum ya zauna a ƙarƙashin wata busasshiyar bishiya da take kusa, kuma bishiyar ta yi kore a lokacin nan, sai ya tambayi Maisara: “Wane ne wancan mutumin da yake ƙarƙashin bishiyar?” Maisara ya ce: “Wannan wani mutum ne na ƙabilar Ƙuraishawa, daga mutanen Harami.” Ruhubanin ya ce: “Har yanzu babu wanda ya zauna a ƙarƙashin wannan bishiya sai annabi.” Sannan ya tambaya: “Akwai ɗan ja a idanunsa?” Maisara ya ce: “I, akwai, kuma ba ya gushewa daga idanunsa.” Sai Nasɗura ya ce: “Na rantse da Allahu Ta’ala, wanda Ya saukar da Injila ga Isa alaihis-salam, wannan mutum zai zama annabi na ƙarshe. Da ma na riski zamanin da aka umarce shi da annabta!”

Lokacin da Muhammadu alaihis-salam yake sayar da kayan Nana Khadija a kasuwar Busra, wani Bayahude da yake ciniki da shi, saboda bai yarda ba, ya ce: “Ka rantse da gumakan nan Lata da Uzza, sai in yarda.” Sai Muhammadu alaihis-salam ya ce: “Ba zan taɓa rantsuwa da sunan waɗannan gumaka ba! Idan na wuce kusa da su, ina juya fuskata wani gefe.” Bayahuden, wanda ya ga sauran alamomi a tattare da shi kuma, ya ce: “Magana taka ce. Wallahi wannan mutum shi ne wanda zai zama annabi”, ya kuma bayyana sha’awarsa da cewa: “Malamanmu sun sami siffarsa a littattafai.”

Maisara yana zana a zuciyarsa kowane abu da ya gani a tattare da Shugabanmu Manzon Allah da ya ji game da shi kamar zane, sha’awarsa gare shi tana ƙaruwa kullum. A zuciyar Maisara wata babbar ƙauna ga Shugaban Talikai ta kafu. Yanzu yana yi masa hidima da daɗi da girmamawa, yana aiwatar da ƙaramar alamarsa ma da babbar ƙauna. An sayar da kayan da aka kai, kuma saboda albarkar Shugabanmu Annabi an sami riba ninkin ta kowane lokaci. Ayarin ya kama hanyar komawa. Da suka isa wurin da ake kira Marruz-Zahran, Maisara ya ba ƙaunataccen Annabinmu shawarar ya kai labarin bushara Makka. Ya karɓa, ya rabu da ayarin, ya gaggauta raƙuminsa zuwa Makka.

Nana Nafisa ƴar Munya ta ba da labari: “Lokacin zuwan ayarin ya kusa. Nana Khadija kowace rana takan hau saman gidanta tare da masu hidimarta, tana jiran hanyar ayarin. A wata rana irin wannan ina wurin Khadija. Kwatsam wani mutum a kan raƙumi ya bayyana daga nesa. Wani girgije da mala’iku biyu a siffar tsuntsaye suna yi masa inuwa a bisansa, nurin da yake goshin Annabinmu mai albarka yana haskakawa kamar wata. Nana Khadija ta gane ko wane ne mai zuwan, zuciyarta ta ji daɗi. Amma ta yi kamar ba ta sani ba, ta tambaya: ‘Wane ne zai iya zuwa a wannan rana mai zafi?’ Masu hidimar suka ce: ‘Wannan mai zuwan kamar Muhammadu (alaihis-salam) ne’, kuma suka yi mamakin abin da suka gani.”

Ba a daɗe ba, Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya zo gidan uwarmu Khadija, ya ba da labarin al’amarin. Busharar da ya kawo ta faranta mata rai ƙwarai.

Bayan ɗan lokaci ayarin ya shiga Makka. Maisara ya ba uwarmu Nana Khadija labari ɗaya bayan ɗaya: yadda aka yi wa Shugabanmu Annabi inuwa a lokacin tafiya, abin da ruhubani Nasɗura ya faɗa, yadda raƙuma marasa ƙarfi suka yi sauri, da wasu al’amura masu ban mamaki da yawa irin waɗannan da ya gani. Ya yabi Shugabanmu Annabi gwargwadon abin da harshensa ya iya. Nana Khadija ta san waɗannan, amma waɗannan maganganu suka ƙara mata yaƙini. Ta yi wa Maisara kashedi: “Kada ka faɗa wa kowa waɗannan da ka gani!”5

“Ba zan taɓa rantsuwa da sunan waɗannan gumaka ba! Idan na wuce kusa da su, ina juya fuskata wani gefe” Hadisi mai daraja

Uwarmu Khadija ta tafi wurin Waraƙa ɗan Naufal domin ta sanar da shi abubuwan nan da ta ji. Waraƙa, wanda ya saurari abubuwan da suka faru da babbar sha’awa, ya ce: “Ya Khadija, idan waɗannan da kika faɗa gaskiya ne, Muhammadu alaihis-salam zai zama annabin wannan al’umma.”

Shugabanmu Annabi ya tafi har Busra tare da baffansa Abu Ɗalib domin kasuwanci yana da shekara 12, Yaman tare da baffansa Zubair yana da shekara 17, Sham tare da Sayyidina Abubakar yana da shekara 20, kuma yana da shekara 25 ya sake zuwa Sham domin sayar da kayan uwarmu Nana Khadija.6 Ya yi tafiya sau huɗu cif. Ban da waɗannan tafiye-tafiye, bai yi tafiya zuwa ko’ina ba.

Aurensa da uwarmu Nana Khadija

Uwarmu Nana Khadija, bayan busharar da Waraƙa ɗan Naufal ya ba ta, da kuma da ta ga kyawawan halayen ƙaunataccen Annabinmu, ta yi sha’awar zama matarsa, ta sami darajar yi masa hidima. Nafisa ƴar Munya ta lura da wannan hali, ta shiga tsakani. Da wannan niyya ta zo gaban Manzo Mafi Daraja mai ɗaukaka, ta tambaya: “Ya Muhammadu! Mene ne ya hana ka yin aure?” Annabinmu ya ce: “Ba ni da isasshen kuɗi a hannu domin in yi aure.” Nana Nafisa ta ce: “Ya Muhammadu! Idan kana son ka auri wata mace mai kamun kai kuma mai daraja, ma’abuciyar dukiya da kyau, ina shirye in yi maka hidima.” Ƙaunataccen Annabinmu ya tambaya: “Wace ce wannan mace?” Ta ce: “Khadija ƴar Khuwailid ce.” Da Shugabanmu Manzon Allah ya tambaya: “Wane ne zai zama sanadi a wannan al’amari?”, ta ce: “Ni zan yi wannan aiki”, ta bar gabansa. Ta tafi wurin Nana Khadija, ta ba ta bushara. Nana Khadija ta kira danginta Amr ɗan Asad da Waraƙa ɗan Naufal, ta ba su labarin al’amarin. Ta kuma aika wa Shugabanmu Manzon Allah labari, ta gayyace shi ya zo a wani lokaci ƙayyadadde. Abu Ɗalib da ƴan’uwansa ma suka yi shirinsu, suka tafi tare da Shugabanmu Annabi.

Uwarmu Nana Khadija ta gyara gidanta, ta ƙawata shi. A matsayin godiyar wannan rana ta ba masu hidimarta dukkan kayan adonta kyauta. Sannan ta ƴanta su. Shugabanmu Manzon Allah ya albarkaci gidan uwarmu Khadija da zuwansa tare da baffanninsa. Abu Ɗalib ya ce: “Godiya ta tabbata ga Mahaliccinmu, wanda Ya sanya mu daga ƴaƴan Ibrahim alaihis-salam da zuriyar Isma’ila alaihis-salam. Ya sanya mu masu tsaron Ɗakin Allah. Ya ba mu wannan gida mai albarka, wanda yake alƙiblar mutane kuma talikai suke yi masa ɗawafi, Harami mai daraja, wanda Ya kiyaye shi daga kowane sharri. Muhammadu, ɗan ɗan’uwana Abdullahi, mutum ne wanda, duk wanda ka kwatanta shi da shi daga cikin Ƙuraishawa, ya fi shi. Gaskiya ne dukiyarsa kaɗan ce, amma ba a kula da dukiya. Domin dukiya kamar inuwa ce: tana wucewa daga hannu zuwa hannu, ta tafi. Darajar ɗan ɗan’uwana da fifikonsa dukkanku kun san su. Yanzu yana neman Khadija ƴar Khuwailid a matsayin matarsa ta halal. Nawa kuke son a ba da sadaki7 daga dukiyata? Ina rantsuwa, lalle darajar Muhammadu za ta zama mai ɗaukaka.” Waraƙa ɗan Naufal ya tabbatar da waɗannan maganganu.

Baffan uwarmu Khadija, Amr ɗan Asad, ya ce: “Ku shaida: na ba da Khadija ƴar Khuwailid ga Muhammadu alaihis-salam a matsayin mata.” Ta haka ƙullin aure ya cika. Bisa wata riwaya sadakin misƙali 400 na zinariya ne, bisa wata riwaya kuma dirhami ɗari biyar, bisa wata riwaya daban kuwa raƙuma 20.8

Domin liyafar aure, Abu Ɗalib ya yanka raƙumi, ya yi liyafar da ba a taɓa ganin irinta ba har zuwa wannan rana. Auren ya tabbata. Uwarmu Nana Khadija ta ba Shugabanmu Annabi dukkan dukiyarta kyauta, ta ce: “Dukkan waɗannan dukiyoyi naka ne, ya mai girma. Ni kuma ina buƙatarka, kuma ina ƙarƙashin falalarka.”

Uwarmu Nana Khadija, a tsawon rayuwar aurensu, koyaushe tana yi wa Annabinmu Muhammadu alaihis-salam hidima, kuma ta zama mataimakiyarsa. Wannan auren Shugabanmu Annabi ya ɗauki shekara ashirin da biyar, har zuwa rasuwar uwarmu Khadija. Shekara goma sha biyar daga ciki kafin bi’isa ce, shekara goma kuma bayan bi’isa (sanar da annabta). Annabinmu Muhammadu alaihis-salam bai auri wata ba ko kaɗan a lokacin da matarsa ta farko Nana Khadija take da rai. Ya haifi ƴaƴa shida: biyu maza, huɗu mata. Su ne: Ƙasim, Zainab, Ruƙayya, Ummu Kulsum, Fatima da Abdullahi (Ɗayyib ko Ɗahir). Daga Nana Mariya, wadda ya aura a lokacin annabtarsa, ma ya haifi ɗa mai suna Ibrahim. Bai haifi ɗa daga sauran matansa ba. Zainab ita ce babbar ƴaƴansa mata. Ƙaramar ƴarsa Fatima ita ce ubanta ya fi so. An haife ta shekara goma sha uku kafin Hijira. Kamar yadda ƴaƴansa maza suka rasu suna ƙanana, haka ma dukkan ƴaƴansa mata, ban da Nana Fatima, sun rasu kafin sa. Uwarmu Fatima ma ta rasu wata shida bayan Shugabanmu Annabi. Zuriyar ƙaunataccen Annabinmu Muhammadu alaihis-salam ta ci gaba ta ƴaƴan Nana Fatima.9

Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya ci gaba da kasuwanci bayan ya auri uwarmu Khadija ma. Da ribarsu sukan karɓi baƙi, su taimaki marayu da matalauta.

Zaid ɗan Harisa

Zaid ɗan Harisa, yana ɗan yaro, ya tafi ziyartar danginsu tare da uwarsa Su’ada. A lokacin wata ƙabila dabam ta kai musu hari. Suka kama Zaid a matsayin fursuna. Suka kawo shi Makka, bikin kasuwanci da ake kira Suƙu Ukaz, suka fito da shi sayarwa. Hakim ɗan Hizam, ɗan ɗan’uwan Nana Khadija, ya sayi Zaid a kan dirhami 400. Hakim ɗan Hizam ya ba gwaggonsa Nana Khadija Zaid ɗan Harisa kyauta, ita kuma ta ba Shugabanmu Annabi shi kyauta. Shugabanmu Annabi ya ƴanta shi nan take, ya riƙe shi a wurinsa. Domin Zaid ɗan Harisa, wanda aka ƴanta, ba shi da inda zai je, kuma ba shi da wanda zai kula da shi fiye da Manzon Allah. Shi ma ya zauna a wurin Manzon Allah da yardar rai.

Shugabanmu Annabi, tun kafin a sanar da shi annabta, an halicce shi ne domin ya cika kowace irin kyakkyawar ɗabi’a, wadda ake gani da wadda ba a gani ba, wadda aka sani da wadda ba a sani ba, irin su adalci, sanin ya kamata, jin ƙai, son mutane, fara’a, karamci, kyauta, cika alkawari, kiyaye amana, taimako, sadaukarwa, amintaka, kare wanda aka zalunta, wanda ya faɗi da matalauci, nuna ƙauna da soyayya ga yara, gaskiya, faɗar gaskiya, ladabi, tawali’u, daidaito, kyakkyawan shugabancin mutane, ƙarfin hali da jarumta. Ya fi dukkan halittun da suka zo da waɗanda za su zo ta kowace fuska, kuma ya sami amincewar kowa har ya sami laƙabin “al-Amin”. Saboda kyakkyawar mu’amalar da ya gani daga gare shi, Zaid ɗan Harisa yana son Shugabanmu Annabi fiye da ubansa da uwarsa, ba ya son rabuwa da shi ko kaɗan.

“Dukkan waɗannan dukiyoyi naka ne, ya mai girma. Ni kuma ina buƙatarka, kuma ina ƙarƙashin falalarka” Khadijatul-Kubra (radiyallahu anha)

Uwarsa da ubansa ba su san inda aka kai ɗansu ba, ba su san abin da aka yi da shi ba. Ubansa Harisa yana ƙuna da wutar begen ɗa, yana yawo gari-gari yana neman ɗansa. Yakan yi wa danginsa da mutanen da ya sani, masu tafiya daga Yaman zuwa ƙasashe daban-daban, kashedi mai tsanani da su kawo masa wani labari game da ɗansa Zaid, yana faɗar waƙoƙi, yana zubar da hawaye:

Na yi kuka saboda Zaidna; ban san abin da ya same shi ba.
Yana da rai, ko ajali ne ya same shi?
Kada ki tambaya, ya zuciya, a banza game da shi!
Ba za ki iya sani ba: kabarinsa a fili yake, ko a dutse mai tsauri.
Wata waƙarsa kuma, da take bayyana begensa ga ɗansa, kamar haka take:
Zaidna, ɗana! Da na san mai tafiya zai dawo, kaito!
Wallahi ba na son wani ya dawo in ba kai ba.
Idan iska ta busa, na tuna shi, duk inda na ga wani yaro,
Rana kuma, kowace safiya idan ta fito, tana tunasar da ni kai.
Kururuwa, dubban kururuwa saboda ƙwayar idona,
Ina hawa dabbata ina nema, ko da halina ya yi muni.
Ni da dabbata ba mu san gajiya ko kasala ba,
Muddin akwai yiwuwar a sami ɗana, ya fito gabana.
Ko nawa bege ya yaudari mutum, a ƙarshe shi mai ƙarewa ne,
Ƴaƴana! Ƙais, Amr, Yazid, Jabal! Zaidna amana ne a gare ku.

A ƙarshe, kafin zuwan Musulunci, wasu daga cikin mutanen ƙabilar Banu Kalb da suka zo ziyartar Ka’aba suka ga Sayyidina Zaid, suka gane shi. Sayyidina Zaid ya ce musu: “Na san iyalina za su yi kururuwa da kuka saboda ni; ku isar musu da waɗannan baituka”, ya faɗi waƙar nan:

Zuciyata tana ƙuna; ina nesa da gidana,
Amma ni maƙwabcin Ka’aba ne, ko da ina nesa da uwata da ubana.
Kada baƙin cikinku ya ƙone zukatanku,
Kada kururuwarku saboda ni ta hau har zuwa Al’arshi.
Godiya ta tabbata ga Majiɓinci, ina cikin irin gidan
Da nake addu’a koyaushe saboda daraja da alherin da nake gani.

Harisa ya yi farin ciki ƙwarai da wannan labari. Nan take ya ɗauki kuɗi masu yawa tare da shi, ya zo Makka tare da ɗan’uwansa Ka’ab. Da ya isa Makka, ya nemi gidan Annabinmu, ya zo gabansa ya ce: “Ya shugaban al’ummar Ƙuraishawa, ya jikan Abdulmuɗɗalib, ya ɗan zuriyar Banu Hashim! Kai maƙwabcin Harami mai daraja ne. Kana karrama baƙi, kana yi wa fursunoni falala, kana kuɓutar da su daga bauta. Domin ƴanta ɗanmu, wanda yake bawa a wurinka, kuɗin da ka so mu ba ka; ka sake shi, muna roƙonka kada ka ƙi wannan buƙata tamu!” Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “Mu kira Zaid, mu sanar da shi al’amarin. Mu ba shi ƴanci. Idan ya zaɓi zuwa wurinku, kuna iya ɗaukarsa ku tafi ba tare da kun ba da wani kuɗi ba. Idan kuwa ya zaɓe ni, ya so ya zauna a wurina, ina rantsuwa da Allah, ba zan bar wanda ya zaɓe ni ga kowa ba, zai zauna a wurina.”

Harisa da ɗan’uwansa suka gamsu ƙwarai da wannan amsar Shugabanmu Annabi, suka ce: “Ka yi mana adalci da sanin ya kamata ƙwarai.”

Sai Shugabanmu Annabi ya kira Zaid zuwa gabansa, ya tambaye shi: “Ka san waɗannan?” Ya ce: “I, ɗaya ubana ne, ɗayan kuma baffana.” Sai ya ce: “Ya Zaid! Ka san ko wane ne ni, ka ga tausayina da jin ƙaina da mu’amalata gare ka. Waɗannan sun zo ne domin su ɗauke ka. To, ko ka zaɓe ni ka zauna a wurina, ko ka zaɓe su ka tafi.”

Ubansa da baffansa suna jira, suna tsammanin yanzu zai zaɓe su, su ɗauki Zaid su tafi. Zaid ya ce: “Ba na fifita kowa a kanka. Kai, a gare ni, kamar ubana da baffana ne. Ina son in zauna a wurinka.”

Ubansa da baffansa suka rikice saboda mamaki. Ubansa ya yi fushi, ya ce wa Zaid: “Kaitonka! Ashe kana fifita bauta a kan ƴanci, a kan uwarka, ubanka da baffanka!” Zaid ya amsa wa ubansa: “Baba, na ga irin tausayi da mu’amala daga wannan mutum, har ba zan iya fifita kowa a kansa ba.”

Shugabanmu Annabi yana son Zaid ƙwarai. Da ya ga wannan riƙonsa gare shi da ƙaunarsa, ya kai shi Hijr a wurin Ka’aba mai girma, ya yi wa waɗanda suke can jawabi: “Ku shaida: Zaid ɗana ne. Shi magajina ne, ni ma magajinsa ne.” Da ubansa da baffansa suka ga wannan hali, fushinsu ya huce. Suka koma ƙasarsu cikin farin ciki. Bayan haka Sahabbai masu girma suka fara kiran Zaid da Zaid ɗan Muhammadu (Zaid, ɗan Muhammadu). Daga baya, lokacin da Allahu Ta’ala Ya kawar da ɗaukar ɗa (riƙon ɗa) da umarnin aya ta biyar ta Suratul Ahzab: “Ku kira ƴaƴanku da sunan ubanninsu, wannan ya fi daidai a wurin Allah” da na aya ta arba’in: “Muhammadu (alaihis-salam) ba uban kowane namiji daga cikinku ba ne (kamar Zaid)”, aka fara kiran Sayyidina Zaid da sunan ubansa, wato “Zaid, ɗan Harisa” (Zaid ɗan Harisa).10

Zamansa mai yanke hukunci a al’amarin Ka’aba

Lokacin da Shugabanmu Manzon Allah yake kusan shekara talatin da biyar, ya zama mai yanke hukunci a al’amarin Ka’aba. A lokacin ruwan sama da rigyawa sun lalata bangwayen Ka’aba ƙwarai. Ban da haka, wata gobara da ta tashi ta ɓata Ka’aba.11 Ya zama dole a sake gina ginin. Saboda haka ƙabilar Ƙuraishawa suka rushe Ka’aba har zuwa harsashin da Ibrahim alaihis-salam ya gina, suka fara sake gina ta. Suka ba kowace ƙabila wani ɓangare, suka ɗaga bangwayen. Ƙabilun, waɗanda suka san cewa wannan aiki babbar daraja ne, ba su yarda da juna ba a kan wanda zai sanya dutsen Hajarul-Aswad a wurinsa. Saboda kowace ƙabila tana son samun wannan daraja, babban saɓani ya tashi a tsakaninsu. Ƴaƴan Abduddar suka yi alkawari suka ce: “Idan wani ba mu ba ya yi wannan aiki, za mu zub da jini.” Saboda wannan saɓani, wanda ya ɗauki kwana huɗu ko biyar, da ƙyar ba a zub da jini ba.

“Ba na fifita kowa a kanka. Kai, a gare ni, kamar ubana da baffana ne. Ina son in zauna a wurinka” Zaid ɗan Harisa (radiyallahu anhu)

Ranar Litinin ce. Huzaifa ɗan Mughira, kawun Abdulmuɗɗalib, wani tsoho mai daraja, ya nuna ƙofar Banu Shaiba da take buɗewa zuwa Ka’aba, ya ce: “Ya ku jama’ar Ƙuraishawa! Domin a yanke hukunci a kan al’amarin da ba ku yarda da juna a kansa ba, ku sanya mutumin da zai fara shiga ta wancan ƙofa mai yanke hukunci a tsakaninku.” Waɗanda suke wurin suka karɓi wannan shawara, suka fara jiran mutumin da zai fara shiga ta ƙofar Banu Shaiba, ya warware wannan al’amari a lokaci mafi tsanani na aikin, suna kallon ƙofar. A ƙarshe suka ga Muhammadu alaihis-salam yana shigowa ta ƙofar – wanda suke daraja gaskiyarsa da ɗabi’unsa masu ɗaukaka ƙwarai, kuma suke kiransa al-Amin, wato “wanda ake amincewa da shi koyaushe”. Suka ce: “Ga al-Amin. Mun yarda da hukuncinsa.”

Da aka ba ƙaunataccen Annabinmu Muhammadu alaihis-salam labarin al’amarin, ya cire mayafinsa ya shimfiɗa a ƙasa. Ya sanya Hajarul-Aswad a kan mayafinsa mai albarka, ya ce: “Daga kowace ƙabila mutum ɗaya ya riƙe gefe ɗaya.” Ta haka ya sa aka ɗaga dutsen har zuwa wurin da za a sanya shi.

Sannan shi da kansa ya rungumi dutsen, ya sanya shi a wurinsa da hannuwansa masu daraja. Ƙabilun, waɗanda suka ga yadda aka hana wani babban faɗa da yake gab da tashi ta haka, suka gamsu da wannan aiki. Suka ci gaba da gina bangwayen daga inda suka tsaya, suka kammala.12