Ƙaunataccen Annabina

GABATARWA

Muna godiya ga Allahu Ta’ala, wanda Ya halicci kowane mai rai, Yake tsayar da kowane abu a cikin wanzuwa a kowane lokaci, kuma Yake kare dukkansu daga tsoro da razana. Tsira (addu’a) da aminci daga gare mu su tabbata ga ƙaunataccen AnnabinSa, Muhammadu alaihis-salam, mafi kyau, mafi alheri kuma mafi ɗaukakar mutane ta kowace fuska; da alayensa (Âl), masu yaɗa ilimi, sani da kyawawan ɗabi’u, da danginsa; da kuma dukkan Sahabbansa1 (radiyallahu ta’ala anhum / Allahu Ta’ala Ya yarda da su), waɗanda suka sami darajar ganin kyakkyawar fuskarsa, mai warkar da rayuka, da jin maganganunsa masu amfani, har suka zama mafi daraja a cikin dukkan mutane; da waɗanda suke bin sawunsu.

Allahu Ta’ala, saboda jin ƙan dukkan mutane, Yana halitta abubuwan da suke amfanarsu a wannan duniya, Yana aiko musu da su. A Lahira kuma, Shi2, saboda falalarSa, Zai gafarta har ma wa muminan da ya kamata su shiga Wuta, Ya sa su kai ga Aljanna. Muhammadu alaihis-salam shi ne annabin3 Allahu Ta’ala, manzonSa da habibinSa (masoyinSa). Shi ne shugaban (sayyid) ƴaƴan Adamu. Waɗanda suka yi imani da Annabi mai daraja irin wannan, suka bi tafarkinsa, babu shakka, sun zama mafi alherin al’ummomi.

Allah Maɗaukakin Sarki, saboda jin ƙanSa, Ya sa mu kai ga mafi girman ni’imominSa ta hanyar sanya mu cikin al’ummarsa.4 Ya bayyana a sarari cewa dole ne a bi shi, a yi masa ɗa’a. Ko nawa muka gode wa Ubangijinmu, muka yi godiya saboda wannan ni’ima mai girma, kaɗan ne. Kafin Ya halicci kowane abu, Allahu Ta’ala Ya halicci nuri mai albarka na Jagoran Talikai (sallallahu alaihi wa sallam). A cikin Alƙur’ani mai girma, cikin magana da aka yi wa Shugabanmu Annabi, an ce: “Ba Mu aike ka ba face rahama ga talikai.” A cikin wani hadisi ƙudusi5 kuma an ce: “Da ba kai ba, da ba kai ba, da ban halicci halittu ba.”

Ainihin sharaɗin imani shi ne “hubb-i fillah wa bughd-i fillah”, wato son masoyan Allahu Ta’ala da ƙin maƙiyanSa. Ba tare da wannan ba, ba a karɓar wata ibada – ana mayar da ita a fuskar mai yin ta. Saboda haka ne son “Shugaban Talikai” ya zama farilla a gare mu, kuma aka umarce mu da mu dasa ƙaunarsa mai albarka a zukatanmu, mu yi ado da kyawawan ɗabi’unsa. Domin wannan ƙauna ta dawwama, tun ƙarnuka da dama ana rubuta littattafan da suke bayani a kan rayuwa mai albarka ta Shugabanmu Annabi – har yanzu kuma ana rubutawa. A gaskiya ma, ta hanyar sunansa mai albarka ne mutane suke samun albarka. Mu ma, domin mu sami rabo daga wannan albarka, kuma domin ƙaunarsa ta cika zukatanmu har ta mamaye su, muna ba da shawarar karanta rayuwa mai albarka ta Sarkin Halittu, Shugabanmu Manzon Allah – aikin da aka shirya bayan dogon bincike a cikin littattafan malaman Ahlus-Sunna. Allahu Ta’ala Ya yarda da dukkan waɗanda suka yi aiki a kansa. Allah Maɗaukakin Sarki Ya cika zukatanmu baki ɗaya da ƙaunar Shugabanmu Annabi, Ya tsayar da mu a kan tafarki madaidaici wanda malaman Ahlus-Sunna suka sanar! Amin.

Dr. Enver Ören

Ka’aba mai girma da Masallacin Harami Makka al-Mukarrama