BI’ISARSA1 DA KIRANSA
Lokacin da Shugaban Talikai (sallallahu alaihi wa sallam) yake da shekara talatin da bakwai, yakan ji muryoyi daga gaibu suna kiransa: “Ya Muhammadu!” Da ya shiga shekara talatin da takwas, ya fara ganin wasu nurori. Yakan ba uwarmu Nana Khadija kaɗai labarin halayensa. Lokacin da sanar da Muhammadu alaihis-salam annabta ya kusa (kamar shekara goma kafin haka), Ƙuss ɗan Sa’ida, ɗaya daga cikin shahararrun masu iya magana na zamanin, a cikin huɗubar da ya yi a kan raƙumi a gaban babban taron jama’a a bikin kasuwanci na Ukaz, ya yi bushara da zuwansa. Ƙaunataccen Annabinmu ma yana cikin waɗanda suka saurari wannan huɗuba. Ƙuss ɗan Sa’ida, a wani ɓangare na wannan shahararriyar huɗubarsa, ya ce:
“Ya ku mutane! Ku zo, ku saurara, ku jira, ku ɗauki darasi! Mai rai yana mutuwa, wanda ya mutu yana ƙarewa, abin da zai faru zai faru!… Ku kasa kunne, ku saurara da kyau! A sama akwai labari, a ƙasa akwai abubuwan ɗaukar darasi!… A wurin Allah akwai addini ɗaya!… Kuma Allah Yana da wani annabi da zai zo. Zuwansa ya kusa ƙwarai. Inuwarsa ta riga ta faɗa a kan kawunanku. Masu albarka ne ƙwarai waɗanda suka saurare shi, suka yi imani da shi! Kaiton marar sa’ar da ya yi masa tawaye, ya yi gaba da shi! Nadama ga al’ummomin da rayuwarsu ta shuɗe cikin gafala!…”
A lokacin, a Ƙasar Larabawa, mutane sun nisanci ma’aunan Allah, sun rarrabu zuwa ƙungiyoyi irin su mawadaci da matalauci, mai ƙarfi da mara ƙarfi, ubangida da bawa. Na farko suna danne na biyu a ƙarƙashin ikonsu, ba sa ƙidaya su a matsayin mutane. Ana ƙwace dukiyar marasa ƙarfi daga hannunsu da ƙarfi, kuma babu wani mai iko da zai hana haka. Saboda sun rasa kunya da tsoron da imani da Allahu Ta’ala yake bayarwa, sun nisanci falala ƙwarai. Kowace irin rashin ɗabi’a, da ayyuka marasa kyau irin su tattake mutunci da ƙima, ana yinsu a fili; caca, shan giya da taruwar shagali da nishaɗi ba a ganin su da wani abu mai ban mamaki. Kisan kai da ba ya yankewa, zina da hare-hare sun yi ƙamari a ko’ina, nishin mutane marasa laifi da kururuwarsu mai zafi suna ƙara har zuwa Al’arshi. Ta fuskar ɗabi’a, cikakkiyar faɗuwa take mulki, mutane suna nutsewa cikin tekun jahilci. Ana sayen mace ana sayar da ita kamar kaya mara daraja; ana binne ƴaƴa mata da ransu a ƙasa ba tare da tausayi ba. Mafi muni a cikin duka shi ne: waɗannan mutane masu taurin zuciya, masu taurin kai kuma nesa da jin ƙai, suna ɗaukar bauta wa gumakan da suka sassaƙa da hannuwansu, waɗanda ba sa amfani ba sa cuta, a matsayin babbar daraja.
Tun daga Adamu alaihis-salam ba a taɓa ganin irin wannan dabbanci, ɓata, rashin ɗabi’a, rashin imani da fasiƙanci a duniya ba. Mutane kamar sun ɗauki siffar namun daji ne. Kowa maƙiyin ɗan’uwansa ne, al’umma tana cikin halin da take shirye ta fashe a kowane lokaci. Domin mutane su sami nutsuwa, dole ne wata ranar farin ciki ta fito a cikin wannan duhu. Idan ta fito, imani zai ɗauki gurbin rashin imani, adalci gurbin zalunci, ilimi gurbin jahilci, kuma mutane za su sami farin ciki na har abada.
A ƙarshe, da farko aka fara nuna wa ƙaunataccen Annabinmu mafarkai na gaskiya. A hadisi mai daraja an sanar da cewa wahayi ya fara da farko da mafarki na gaskiya. Abin da yake gani a mafarki yakan faru daidai haka. Wannan hali ya ɗauki wata shida. Da zuwan wahayi ya kusa, muryoyin da suke cewa “Ya Muhammadu!” suka yawaita. Bayan haka ya fara son keɓewa, yana nisantar mutane, yana nutsewa cikin tunani (tafakkuri) a wani kogo a dutsen Hira. Wani lokaci yakan zo Makka, ya yi ɗawafin Ka’aba, ya tafi gidansa mai albarka. Bayan ya zauna na ɗan lokaci a gidansa mai albarka, yakan sake komawa kogon da yake dutsen Hira da ɗan abinci tare da shi, ya shagala da tunani da ibada. Wani lokaci yakan zauna a can kwanaki da dama. A lokacin kuma Nana Khadija takan aika masa da abinci ko ta kai masa da kanta.2
Muhammadu alaihis-salam ya sanya Hajarul-Aswad a kan mayafinsa mai albarka, ya ce: “Daga kowace ƙabila mutum ɗaya ya riƙe gefe ɗaya” Ƙaunataccen Annabinmu Muhammadul-Amin (sallallahu alaihi wa sallam)
Wahayi na farko
Lokacin da Shugabanmu Annabi yake da shekara arba’in, a wani watan Ramadan kuma, ya keɓe a kogon da yake dutsen Hira, ya nutse cikin tunani. A ranar 17 ga Ramadan, daren Litinin, bayan tsakiyar dare, ya ji wata murya tana kiran sunansa. Da ya ɗaga kansa ya duba kewaye, ya sake jin muryar nan karo na biyu, kuma ya ga wani nuri ya rufe ko’ina kwatsam. Bayan haka Jibrilu3 alaihis-salam ya zo gabansa ya ce: “Karanta!” Shugabanmu ya amsa masa: “Ban iya karatu ba!” Sai mala’ikan ya kama shi, ya matse shi har ƙarfinsa ya ƙare, ya ce: “Karanta!” Ya sake amsawa: “Ban iya karatu ba!” Ya sake matse shi, ya ce: “Karanta!” Da ya ce: “Ban iya karatu ba!”, ya matse shi karo na uku. Sannan ya sake shi, ya kawo ayoyi biyar na farko na Suratul Alaƙ, waɗanda ma’anarsu: “(Ya Muhammadu alaihis-salam!) Ka karanta da sunan Ubangijinka Allah, wanda Ya halicci kowane abu! Ya halicci mutum daga gudan jini (alaƙa)! Ka karanta, Allah Ma’abucin karamci mai girma ne. Shi Yake koyarwa da alƙalami, Yake koyar da abin da ba a sani ba.”4 Muhammadu alaihis-salam ma ya karanta tare da shi. Ta haka wahayi na farko ya zo, kuma haka ranar Musulunci, wadda take haskaka duniya baki ɗaya, ta fito.5
Shugabanmu Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya fito daga kogon da yake dutsen Hira cikin babban rawar jiki da motsin rai, ya fara gangarowa ƙasa. Da ya isa tsakiyar dutsen, ya ji wata murya. Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Muhammadu! Kai manzon Allahu Ta’ala ne, ni kuma Jibrilu ne”, ya buga ƙasa da diddigensa. Daga wurin da ya buga ruwa ya fito, ya fara alwala. Shugabanmu Annabi yana kallonsa a hankali. Da Jibrilu alaihis-salam ya gama alwalarsa, ya ce wa Shugabanmu Annabi ya yi alwala kamar yadda ya gani. Bayan ƙaunataccen Annabinmu ya gama alwalarsa, Jibrilu alaihis-salam ya zama limami6, suka yi salla raka’a biyu.
Bayan haka Jibrilu alaihis-salam ya ce: “Ya Muhammadu! Ubangijinka Yana gaishe ka!”, sannan ya faɗi abin da Ya ce: “Kai ManzoNa ne ga aljanu da mutane. To, ka kira su zuwa ga tauhidi.” Sannan ya rabu da shi, ya hau zuwa sama. Ta haka ƙaunataccen Annabinmu ya ga Jibrilu alaihis-salam, ya kuma yi magana da shi.
Sallamar duwatsu da bishiyoyi
Har zuwa lokacin da Shugabanmu Annabi ya isa gidansa mai albarka, ya ji kowane dutse da kowace bishiya da ya wuce kusa da su suna cewa: “Assalamu alaika ya Rasulallah!” Da ya isa gida, ya ce: “Ku rufe ni! Ku rufe ni!”, ya huta har rawar jikinsa ta lafa. Sannan ya ba uwarmu Nana Khadija labarin abin da ya gani, ya ce: “Jibrilu (alaihis-salam) ya ɓace daga idona. Amma kwarjininsa, tsananinsa da tsoron da ya kawo ba su tafi daga kaina ba. Na ji tsoron kada su ce mini mahaukaci, su tsawaita harshe su zage ni.” Nana Khadija, wadda take jiran waɗannan halaye da waɗannan kwanaki, kuma take a shirye don haka, ta ce: “Allahu Ta’ala Ya kiyaye. Allah Maɗaukaki Yana ba ka alheri, kuma ba Ya nufin kome a gare ka sai alheri. Na rantse da Allahu Ta’ala, na yi imani cewa za ka zama annabin wannan al’umma. Domin kai mai son baƙo ne. Kana faɗar gaskiya kuma kai amintacce ne. Kana taimakon gajiyayyu, kana kare marayu, kana taimakon baƙi. Kai mai kyakkyawan hali ne; mai waɗannan halaye ba shi da tsoro.”7
Sannan suka tafi wurin Waraƙa ɗan Naufal domin su tambaye shi game da wannan al’amari. Bayan ya saurari abin da Shugabanmu Manzon Allah ya faɗa, Waraƙa ya ce: “Bushara gare ka, ya Muhammadu alaihis-salam! Ina rantsuwa da Allahu Ta’ala, kai ne annabi na ƙarshe wanda Isa alaihis-salam ya ba da labarinsa. Mala’ikan da ya bayyana gare ka shi ne Jibrilu alaihis-salam, wanda ya zo wa Musa alaihis-salam kafin ka. Kaito! Da ma ina saurayi! Da na riski lokacin da za su fitar da kai daga Makka, in gaggauta taimakonka! Ba da daɗewa ba za a umarce ka da isar da addini da jihadi.” Ya sumbaci hannun Shugabanmu Annabi mai albarka. Ba a daɗe ba ya rasu.8
Zuwan umarnin isar da addini
Haka wahayi na farko da aka sanar da ƙaunataccen Annabinmu annabta a cikinsa ya zo. Sannan ya yanke, bai sake zuwa ba har shekara uku. A wannan lokaci mala’ika mai suna Isra’filu alaihis-salam ya zo, ya koya masa wasu abubuwa. Waɗannan ba wahayi ba ne. A cikin wannan lokaci, Shugabanmu Manzon Allah wani lokaci yakan shiga damuwa ƙwarai. Duk lokacin da ya yi baƙin ciki, Jibrilu alaihis-salam yakan bayyana ya ce: “Ya Habiballah! Kai annabin Allahu Ta’ala ne”, ya lafar da baƙin cikinsa. Shugabanmu Annabi ya ce: “A lokacin da wahayi ya yanke ne. Lokacin da nake gangarowa daga dutsen Hira, kwatsam na ji wata murya daga ɓangaren sama. Na duba sama. Na ga Jibrilu (alaihis-salam). Yana zaune a kan wata kujera a tsakanin ƙasa da sama. Tsoro ya kama ni. Na isa gida. Na ce: ‘Ku rufe ni da wani abu.’ Sai Allah Maɗaukaki Ya aiko da wahayi; Ya saukar da ayoyin farko9 na Suratul Muddassir, waɗanda ma’anarsu: ’Ya Muhammadu alaihis-salam, kai mai lulluɓe da mayafinka! Tashi ka yi gargaɗi (ga kafirai da azabar Allahu Ta’ala)! Ka girmama Ubangijinka, ka ɗaukaka Shi! Ka tsarkake tufafinka!’ Bayan haka wahayi bai ƙara yankewa ba.”
Abin Alfaharin Halittu (alaihi afdalus-salawat) ya fara kiran mutane zuwa Musulunci, yana isar da umarnin Allahu Ta’ala da haninSa. Lokacin da Jibrilu alaihis-salam yake kawo wahayi, wani lokaci yakan shiga siffar mutum, ya zo a siffar Dihya Kalbi, ɗaya daga cikin Sahabbai masu girma. Wani lokaci yakan jefa wahayin a zuciyar Shugabanmu Annabi; a lokacin Shugabanmu Manzon Allah ba ya ganinsa. Wani lokaci wahayi yakan zo ta mafarki, wani lokaci kuma da wata ƙara mai ban tsoro.
Wannan ita ce hanyar da ta fi nauyi, ta fi wuya, wadda wahayi yake zuwa ta ita ga Shugabanmu Annabi. A irin waɗannan lokuta, ko a rana mafi sanyi, zufa takan zubo daga goshin Manzon Allah mai albarka, kuma idan yana kan raƙumi, raƙumin yakan durƙusa a ƙasa saboda nauyin wahayin. Sahabban da suke tare da shi ma sukan ji nauyin wahayin. Jibrilu alaihis-salam ya zo sau da dama a siffarsa ta asali ma.
“Ya Muhammadu, kai mai lulluɓe da mayafinka! Tashi ka yi gargaɗi (ga kafirai da azabar Allahu Ta’ala)! Ka girmama Ubangijinka, ka ɗaukaka Shi!” Muddassir: 1–3
Allahu Ta’ala Ya kuma saukar wa Shugabanmu Annabi wahayi ba tare da mala’ika ba, ba tare da labule ba, wato ba tare da wani matsakanci ba. Wannan hali ya faru a daren Mi’iraji. Isar da Musulunci ta Muhammadu Mustafa (sallallahu alaihi wa sallam), wanda ya fara aikin annabta da zuwan wahayi na farko, ta ɗauki shekara ashirin da uku. Shekara goma sha uku na wannan lokaci a Makka suka shuɗe, shekara goma kuma a Madina. An saukar da Alƙur’ani mai girma aka kammala a cikin lokaci na shekara 22, wata 2 da kwana 22.
Muhammadu alaihis-salam ummiyyi ne, wato bai karanta littafi ba, bai rubuta rubutu ba, kuma bai ɗauki darasi daga wurin kowa ba. An haife shi a Makka, ya girma a can, ya tashi a tsakanin sanannun mutane. Duk da haka, ya ba da labarin ilimomi da al’amuran da suke cikin Attaura, Injila da littattafan da aka rubuta a zamanin Girkawa da Rumawa. Domin sanar da Musulunci, a ƙarshen shekara ta shida bayan Hijira da farkon shekara ta bakwai, ya aika da wasiƙu ga sarakunan Rum, Farisa da Habasha da sauran sarakunan Larabawa. Jakadun ƙasashen waje fiye da sittin sun zo gabansa. An sanar da wannan al’amari a Alƙur’ani mai girma, a ma’ana, kamar haka: “Kafin wannan Alƙur’ani mai girma ya zo, ba ka karanta wani littafi ba. Ba ka rubuta rubutu ba. Da ka iya karatu da rubutu, da sun ce ka koya daga wurin waɗansu.”10
A hadisi mai daraja kuma an ce: “Ni ne Muhammadu, annabi ummiyyi… Babu annabi bayana.”11 Haka kuma a Alƙur’ani mai girma an ce: “Shi (Muhammadu alaihis-salam) ba ya magana daga kansa. Maganganunsa, ana sanar da shi su, ana koya masa su ta wahayi.”12
Musulmin farko (Sabiƙunal-Islam)
Bayan wahayi na farko ya zo wa Shugabanmu Annabi (sallallahu alaihi wa sallam), wadda ta fara yin imani ita ce uwarmu Nana Khadija.13 Ba tare da wata shakka ba ta karɓi Musulunci nan take, ta sami darajar zama Musulma ta farko.
Shugabanmu Annabi ya koya wa uwarmu Nana Khadija yin alwala kamar yadda Jibrilu alaihis-salam ya koyar. Sannan Shugabanmu Annabi ya zama limami, suka yi salla raka’a biyu tare. Uwarmu Nana Khadija ta yi ɗa’a ga kowace magana da kowane umarni na ƙaunataccen Annabinmu ta hanya mafi kamala. Ta haka ta kai ga darajoji masu ɗaukaka ƙwarai a wurin Allahu Ta’ala. Idan Shugabanmu Manzon Allah ya yi baƙin ciki, ya sha wahala saboda izgilin masu musu, takan yi masa ta’aziyya, ta kawar da damuwarsa. Takan ce: “Ya Manzon Allah! Kada ka yi baƙin ciki ko kaɗan, kada ka damu. A ƙarshe addininmu zai sami ƙarfi, mushrikai za su halaka. Mutanenka za su yi maka ɗa’a…” Saboda waɗannan taimakon uwarmu Khadija, wata rana Jibrilu alaihis-salam ya zo ya ce: “Ya Manzon Allah! Ka isar wa Khadija da sallamar Allahu Ta’ala.” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ya Khadija! Ga Jibrilu (alaihis-salam) yana isar miki da sallamar Allahu Ta’ala.”14
Shugabanmu Annabi wata rana kuma ya ce: “Allahu Ta’ala Ya umarce ni da in yi wa Khadija bushara da wani gida na lu’ulu’u a Aljanna. A can babu rashin lafiya, babu baƙin ciki, babu ciwon kai.”
Bayan Nana Khadija, wanda ya fara zama Musulmi daga cikin manya shi ne Sayyidina Abubakar, ɗaya daga cikin abokan Shugabanmu Manzon Allah na kusa. Sayyidina Abubakar ya yi wani mafarki shekara ashirin kafin haka: “Cikakken wata ya sauko daga sama, ya zo Ka’aba mai girma, ya rarrabu guntu-guntu, kowane guntu ya faɗa a kan ɗaya daga cikin gidajen Makka, sannan guntuwan nan suka haɗu suka hau zuwa sama. Amma guntun da ya faɗa a gidan Abubakar bai hau zuwa sama ba. Sayyidina Abubakar, da ya ga wannan al’amari, nan take ya rufe ƙofar gidansa, kamar ya hana tafiyar wannan guntun wata.”
Abubakar ya farka daga mafarkin cikin motsin rai, kuma da gari ya waye, nan take ya ruga wurin ɗaya daga cikin malaman Yahudawa, ya ba shi labarin mafarkinsa. Malamin nan ya amsa: “Wannan ɗaya ne daga cikin mafarkai rikitattu, saboda haka ba a fassara shi.” Amma wannan mafarki ya ci gaba da damun zuciyar Abubakar, amsar Bayahuden ma ba ta gamsar da shi ba. A wani lokaci, lokacin da ya tafi kasuwanci, hanyarsa ta faɗa ƙasar ruhubani Bahira. Da ya nemi fassarar mafarkin da ya gani daga Bahira, Bahira ya ce: “Daga ina kake?” Da Sayyidina Abubakar ya amsa: “Daga Ƙuraishawa”, Bahira ya ce: “A can wani annabi zai fito, kuma nurin shiriya zai isa kowane wuri na Makka. Kai za ka zama waziri nasa a rayuwarsa, bayan rasuwarsa kuma halifansa.” Sayyidina Abubakar ya yi mamaki ƙwarai da wannan amsa. Bai faɗa wa kowa wannan mafarkinsa da fassarorinsa ba har zuwa lokacin da Shugabanmu Annabi ya bayyana annabtarsa. Lokacin da ƙaunataccen Annabinmu Muhammadu alaihis-salam ya bayyana annabtarsa, Sayyidina Abubakar nan take ya ruga wurin Shugabanmu Annabi, ya tambaya: “Annabawa suna da dalilai na annabtarsu, mene ne dalilinka?” Shugabanmu Annabi ya amsa: “Dalilin wannan annabta tawa shi ne mafarkin nan da ka nemi fassararsa daga wani malamin Yahudawa. Malamin nan ya ce: ‘Yana daga mafarkai rikitattu, ba a fassara shi.’ Sannan ruhubani Bahira ya fassara shi daidai”, sannan ya ce wa Sayyidina Abubakar: “Ya Abubakar! Ina kiranka zuwa ga Allah da ManzonSa.”
A kan haka Sayyidina Abubakar ya ce: “Ina shaida cewa kai manzon Allahu Ta’ala ne, annabtarka gaskiya ce, kuma nuri ne da yake haskaka duniya”, ya zama Musulmi.
Bisa wata riwaya kuma, kafin annabta ta zo wa Shugabanmu Annabi, Sayyidina Abubakar ya tafi Yaman domin kasuwanci. A wannan tafiyarsa ya haɗu da wani tsoho na ƙabilar Azd a Yaman, wanda ya karanta littattafai da yawa. Wannan tsoho ya dubi Sayyidina Abubakar ya ce: “Ina zaton kai daga mutanen Makka ne.” Sayyidina Abubakar ya ce: “I, haka ne”, kuma wannan tattaunawa ta gudana a tsakaninsu:
“Kai daga Ƙuraishawa ne?”
“I!”
“Daga Banu Tamim?”
“I!”
“Alama ɗaya ta rage.” “Wace ce?”
“Buɗe cikinka, in gani.”
“Faɗa mini, mene ne manufarka da wannan?”
“Na karanta a littattafai cewa wani annabi zai zo a Makka. Mutum biyu za su taimake shi. Ɗaya saurayi ne, ɗayan kuma tsoho. Saurayin zai mayar da matsaloli da yawa sauƙi, ya kawar da masifu da yawa. Tsohon kuwa fari ne, mai siririn ƙugu, kuma a cikinsa akwai wani baƙin tabo. Ina zaton mutumin nan kai ne. Buɗe cikinka, in gani.”
“Shi (Muhammadu alaihis-salam) ba ya magana daga kansa. Maganganunsa, ana sanar da shi su, ana koya masa su ta wahayi” Najm: 3–4
Sai Sayyidina Abubakar ya buɗe cikinsa mai albarka; da tsohon ya ga baƙin tabon da yake bisa cibiyarsa, ya ce: “Wallahi mutumin nan kai ne”, ya yi wa Abubakar wasiyyoyi da yawa. Da Sayyidina Abubakar ya gama aikinsa, ya zo wurin tsohon domin ya yi bankwana, ya roƙe shi ya faɗi ƴan baituka game da Shugabanmu Annabi. Sai tsohon ya karanta baituka goma sha biyu, Sayyidina Abubakar kuma ya haddace su.
Da Sayyidina Abubakar ya dawo Makka al-Mukarrama daga tafiya, manyan Ƙuraishawa irin su Uƙba ɗan Abu Mu’aiɗ, Shaiba, Abu Jahal da Abul-Bakhtari suka zo gidansa domin su ziyarce shi. Sayyidina Abubakar ya ce musu: “Shin wani al’amari ya faru a tsakaninku?” Suka amsa: “Shin akwai al’amarin da ya fi wannan ban mamaki: marayan Abu Ɗalib yana da’awar annabta, yana cewa ku da ubanninku da kakanninku kuna kan addinin ƙarya. Da ba don kai ba, da ba mu bar shi da rai ba har zuwa wannan lokaci. Kai abokinsa ne na kusa, ka warware wannan al’amari da kanka.”
Sayyidina Abubakar ya kawar da su, ya sami labarin cewa Shugabanmu Annabi yana gidan Nana Khadija. Ya tafi ya ƙwanƙwasa ƙofa. Da Shugabanmu Annabi ya tarbe shi, Abubakar ya ce: “Ya Muhammadu! Mene ne abin da ake faɗa game da kai?” Shugabanmu Annabi ya ce: “Ni annabin Allah Maɗaukaki ne. An aiko ni gare ka da ga dukkan ƴaƴan Adamu. Ka yi imani, domin ka kai ga yardar Allah Maɗaukaki, ka tsare ranka daga Jahannama.”
Da Sayyidina Abubakar ya ce: “Mene ne dalilin wannan?”, Manzo Mafi Daraja ya ce: “Dalili shi ne labarin tsohon nan da ka gani a Yaman.” Sayyidina Abubakar ya ce: “Na ga tsofaffi da samari da yawa a Yaman.” Shugabanmu Annabi ya amsa: “Tsohon nan da ya ba ka amanar baituka goma sha biyu, ya aiko su gare ni”, ya karanta dukkan baitukan nan. Da Sayyidina Abubakar ya ce: “Wane ne ya ba ka labarin wannan?”, Shugabanmu Annabi ya amsa: “Mala’ikan da ya zo wa annabawan da suka gabace ni ne ya ba ni labari.” Da zarar ya faɗi haka, Sayyidina Abubakar ya ce: “Ka ba ni hannunka”, ya riƙe hannunsa mai albarka, ya ce: “Ash-hadu an la ilaha illallah, wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu”, ya zama Musulmi.15 Da babban farin ciki da ya fara ji a rayuwarsa, Sayyidina Abubakar ya koma gidansa Musulmi. A hadisi mai daraja kuma an ce: “Duk wanda na gabatar wa da imani, sai ya tarƙe fuska, ya duba da shakka. Sai dai Abubakar as-Siddiƙ kaɗai bai yi wata shakka ko jinkiri ba wajen karɓar imani.”
Wata rana, lokacin da Shugabanmu Annabi yake salla tare da uwarmu Nana Khadija, Sayyidina Aliyu ya gan su. A lokacin yana da shekara goma ko goma sha biyu. Bayan salla ya tambaya: “Mene ne wannan?” Manzo Mafi Daraja (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “Wannan addinin Allahu Ta’ala ne. Ina kiranka zuwa ga wannan addini. Allahu Ta’ala ɗaya ne, ba Shi da abokin tarayya. Ina kiranka zuwa ga imani da Allah, wanda Yake ɗaya, ba Shi da kini ko abokin tarayya…” Sayyidina Aliyu ya ce: “Bari in fara shawara da ubana.” Manzon Allah ya ce masa: “Idan ba ka shiga Musulunci ba, kada ka faɗa wa kowa wannan sirri!” Washegari da safe Sayyidina Aliyu ya zo gaban Manzon Allah, ya ce: “Ya Manzon Allah! Ka koya mini Musulunci”, ya zama Musulmi.16
Sayyidina Aliyu shi ne na uku a cikin waɗanda suka zama Musulmi. Sadaukarwar da ya nuna a tafarkin Manzo Mafi Daraja da fifita shi a kan kansa kuwa sun fi kowace irin yabo.
Zaid ɗan Harisa yana daga cikin waɗanda suka fara yin imani. Ya sami darajar zama na huɗu bayan Nana Khadija, Sayyidina Abubakar da Sayyidina Aliyu, kuma Musulmi na farko a cikin bayin da aka ƴanta. Tare da shi, matarsa Ummu Aiman ma ta zama Musulma.17
Da Sayyidina Abubakar ya zama Musulmi, nan take ya tafi wurin abokansa da yake ƙauna ƙwarai. Ya rinjaye su, su ma suka zama Musulmi. Manyan mutanensa masu ɗaukaka, daga cikin manyan Sahabbai masu girma, irin su Usman ɗan Affan, Ɗalha ɗan Ubaidullahi, Zubair ɗan Awwam, Abdurrahman ɗan Auf da Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas, su ne mafi shahara a cikinsu.18 Waɗannan mutum takwas da suka zama Musulmi bayan uwarmu Nana Khadija ana kiransu Sabiƙunal-Islam, wato Musulmin farko. Sayyidina Usman ya ba da labarin zamansa Musulmi kamar haka: “Ina da wata ƴar’uwar uwata ƴar boka. Wata rana na ziyarce ta. Ta ce mini: ‘Za ka sami wata mata. Amma kai ba ka taɓa ganin wata mace kafin ta ba, ita ma ba ta taɓa ganin wani namiji kafin ka ba. Ita mace ce mai kyakkyawar fuska, mai tsoron Allah, kuma ƴar wani babban annabi ce.’
Na yi mamakin wannan maganar ƴar’uwar uwata. Ta sake ce mini: ‘Wani annabi ya zo. Wahayi ya sauko masa daga sama.’ Na ce: ‘Ya gwaggo! Irin wannan sirri ba a taɓa jin sa a birni ba. To, ki faɗi wannan magana a sarari.’ Sai ƴar’uwar uwata ta ce: ‘Annabta ta zo wa Muhammadu ɗan Abdullahi. Yana kiran mutane zuwa addini. A cikin ɗan lokaci talikai za su haskaka da addininsa, kuma za a yanke kawunan masu gaba da shi.’
Waɗannan maganganun ƴar’uwar uwata sun shiga zuciyata ƙwarai. Na shiga damuwa. A tsakanina da Sayyidina Abubakar akwai babbar abota; ba ma rabuwa da juna ko kaɗan. Domin tattauna wannan al’amari, bayan kwana biyu na tafi wurin Sayyidina Abubakar. Da na ba shi labarin abin da ƴar’uwar uwata ta faɗa, ya ce mini: ‘Ya Usman! Kai mutum ne mai hankali. Yaya wasu duwatsu, waɗanda ba sa gani ba sa ji, kuma suke nesa da amfanar da wani abu ko cutar da shi, za su cancanci zama abin bauta?’ Na ce: ‘Ka faɗi gaskiya, maganar ƴar’uwar uwata gaskiya ce.’”
Bayan Sayyidina Abubakar ya bayyana wa Sayyidina Usman Musulunci, ya kai shi gaban Shugabanmu Annabi, Rasulus-Saƙalain, wato annabin mutane da aljanu. Ƙaunataccen Annabinmu ya ce wa Sayyidina Usman: “Ya Usman! Allah Maɗaukaki Yana kiranka zuwa baƙunci a Aljanna. Kai ma ka amsa (ka karɓa). An aiko ni jagoran shiriya ga dukkan mutane.” Sayyidina Usman, a gaban halayen Manzon Allah masu ɗaukaka da maganganun da ya faɗa da fara’a, ya manta da kansa, kuma da babban shauƙi da sallamawa ya ce: “Ash-hadu an la ilaha illallah, wa ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu”, ya zama Musulmi.
Shugabanmu Manzon Allah, a shekaru uku na farko na annabtarsa, ya kira mutane zuwa Musulunci a ɓoye. Mutane suna zama Musulmi a hankali, ɗaya-ɗaya, biyu-biyu. A cikin wannan lokaci adadin Musulmi ya kai talatin kawai. Su ma suna yin ibadarsu a gidajensu, suna karanta ayoyin Alƙur’ani mai girma da aka saukar a ɓoye, suna haddace su.
“Sabiƙunal-Islam, wato Musulmin farko: Abubakar as-Siddiƙ, Aliyu ɗan Abu Ɗalib, Zaid ɗan Harisa, Usman ɗan Affan, Abdurrahman ɗan Auf, Sa’ad ɗan Abu Waƙƙas, Zubair ɗan Awwam da Ɗalha ɗan Ubaidullahi” (radiyallahu anhum ajma’in)
Kiran dangi na kusa
Shugabanmu Manzon Allah ya fara kiran mutane zuwa addinin Musulunci da saukar Suratul Muddassir. Yana yin wannan kira a ɓoye. Bayan ɗan lokaci kuma aya mai girma da ma’anarta: “Ka tsoratar da danginka na kusa da azabar Allahu Ta’ala, ka kira su zuwa ga addinin gaskiya” ta sauka.19 A kan haka Shugabanmu Annabi Muhammadu alaihis-salam ya aika da Sayyidina Aliyu domin ya kira danginsa zuwa addini, ya gayyaci dukkansu gidan Abu Ɗalib. Ya sanya a gabansu tasa ɗaya ta abinci da ƙoƙon madara ɗaya, da suke ishe mutum ɗaya kawai; da farko shi da kansa ya fara ci da basmala, sannan ya ce wa danginsa da suka zo: “Ku zo, ku ci.” Adadin waɗanda suka zo mutum arba’in ne. Amma abincin da aka sanya ya ƙosar da dukkansu, bai ragu ba ko kaɗan. Waɗanda suka zo suka yi mamakin wannan mu’ujiza. Bayan cin abinci Shugabanmu Annabi yana gab da fara magana domin ya kira danginsa zuwa Musulunci. Sai baffansa Abu Lahab, da ƙiyayya, ya ce: “Ba mu taɓa ganin sihiri irin na yau ba. Ɗan’uwanku ya sihirce ku da wani sihiri. Ya ɗan ɗan’uwana! Ban taɓa ganin wani mutum da ya kawo sharri da mugunta kamar yadda ka kawo ba”, ya ci gaba da maganganunsa na cin mutunci.
Annabinmu ya ce wa Abu Lahab: “Kai ka yi mini muguntar da Ƙuraishawa da dukkan ƙabilun Larabawa ba za su iya yi ba!” Suka watse ba tare da ko ɗayansu ya zama Musulmi ba. Ba a daɗe ba bayan wannan al’amari, ya sake gayyatar danginsa. Sayyidina Aliyu ya sake kiran dukkansu.
Kamar a baya, aka sanya musu abinci a gabansu. Bayan cin abinci Shugabanmu Annabi ya tashi tsaye ya ce: “Godiya ta keɓanta ga Allahu Ta’ala kaɗai. Daga gare Shi kaɗai nake neman taimako. Ina imani da Shi, ina dogara gare Shi. Babu shakka na sani kuma ina sanarwa: babu abin bauta sai Allahu Ta’ala, Shi ɗaya ne. Ba Shi da kini, ba Shi da abokin tarayya.” Sannan ya ci gaba da maganarsa kamar haka: “Ba zan taɓa yi muku ƙarya ba, gaskiya nake sanar muku… Ina kiranku zuwa ga imani da Allahu Ta’ala, wanda Yake ɗaya, kuma babu abin bauta sai Shi. Ni annabinSa ne da Ya aiko gare ku da ga dukkan ɗan’adam. Wallahi za ku mutu kamar yadda kuke yin barci, za a tashe ku kamar yadda kuke farkawa daga barci, kuma za a yi muku hisabi a kan dukkan abin da kuka aikata; za a saka muku da lada saboda ayyukanku na alheri, da uƙuba saboda munanan ayyukanku. Waɗannan kuwa ko dawwama ne a Aljanna, ko dawwama a Jahannama. Ku ne mutanen farko da na tsoratar da azabar Lahira.”
Bayan ya saurari waɗannan maganganu, Abu Ɗalib ya ce: “Ya ɗan ɗan’uwana mai daraja! Ban san wani abu da ya fi taimakonka daraja ba. Mun karɓi nasihohinka mun riƙe su, mun kuma tabbatar da maganganunka daga zuciya. Waɗanda suka taru a nan yanzu ƴaƴan kakanka Abdulmuɗɗalib ne. Babu shakka ni ma ɗaya ne daga cikinsu. Ni ne zan fara gaggauta zuwa ga abin da kake so a cikinmu. Ina yi maka alkawari ba zan daina kewaye ka in kare ka ba ko na ɗan lokaci. Ka ci gaba da abin da aka umarce ka. Amma a kan barin tsohon addinina, ban sami raina yana biyayya gare ni ba.”
Ban da Abu Lahab, danginsa da baffanninsa da suke wurin suka yi magana da sanyi. Amma Abu Lahab ya ce: “Ya ku ƴaƴan Abdulmuɗɗalib! Kafin waɗansu su kama hannunsa su hana shi, ku hana shi. Idan kuka karɓi abin da ya faɗa a yau, za ku shiga wulaƙanci da cin mutunci. Idan kuka tashi kare shi, za a kashe ku duka…”, ya faɗi maganganu na rashin kunya, ya yi barazana. A kan Abu Lahab, gwaggon Shugabanmu Annabi ta ce: “Ya ɗan’uwana! Shin ya dace da kai ka bar ɗan ɗan’uwanka da addininsa ba tare da taimako ba? Wallahi malaman da suke raye a yau suna sanar da cewa wani annabi zai zo daga zuriyar Abdulmuɗɗalib. Ga shi, wannan annabin shi ne wannan.”
A gaban waɗannan maganganu Abu Lahab ya ci gaba da munanan maganganunsa. Abu Ɗalib ya yi fushi da Abu Lahab, ya ce: “Ya matsoraci! Wallahi muddin muna da rai, mu ne mataimakansa da masu kare shi.” Ya juya ga Muhammadu alaihis-salam ya ce: “Ya ɗan ɗan’uwana! Ka sanar da mu lokacin da kake son ka kira mutane zuwa ga imani da Ubangijinka; za mu ɗauki makamai mu fito tare da kai.” Sannan Abin Alfaharin Halittu ya sake fara magana ya ce: “Ya ku ƴaƴan Abdulmuɗɗalib! Wallahi, a cikin Larabawa babu wani mutum da ya kawo wa mutanensa abin da ya fi abin da na kawo muku ɗaukaka da alheri, wanda yake alheri ne ga duniyarku da Lahirarku (wato wannan addini). Ina kiranku zuwa ga faɗar kalmomi biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a mizani. Su ne: ku shaida cewa babu abin bauta sai Allah, kuma ni bawanSa ne da manzonSa. Allahu Ta’ala Ya umarce ni da in kira ku zuwa ga wannan. To, wane ne a cikinku zai karɓi wannan kira nawa, ya zama mataimakina a wannan tafarki?” Ba a ji muryar kowa ba. Dukkansu suka sunkuyar da kawunansu. Shugabanmu Annabi ya maimaita waɗannan maganganunsa sau uku. A duk lokacin da ya faɗa, Sayyidina Aliyu yakan tashi tsaye. A karo na uku ya ce: “Ya Manzon Allah! Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar shekaru a cikin waɗannan, ni zan zama mataimakinka.” Sai Shugabanmu Manzon Allah ya riƙe hannun Sayyidina Aliyu.
Sauran suka watse cikin mamaki. Habibin Allahu Ta’ala (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi baƙin ciki ƙwarai saboda wannan halin danginsa.
Amma bai karaya ba, ya ci gaba da kira domin su kuɓuta daga Jahannama, su sami farin ciki.
A shekara ta huɗu ta bi’isa, aya ta casa’in da huɗu ta Suratul Hijr ta sauka. Da umarnin Allah ya zo, wanda ma’anarsa: “(Ya MasoyiNa!) Ka bayyana a fili abin da aka umarce ka da shi (umarni da hani). Ka kau da kai daga mushrikai! Kada ka kula da maganganunsu!”, ƙaunataccen Annabinmu ya fara kiran mutanen Makka zuwa Musulunci a fili. Wata rana ya hau tudun Safa ya ce: “Ya ku mutanen Ƙuraishawa! Ku taru a nan, ku saurari maganganuna!” Bayan ƙabilun sun taru, ya tambaya: “Ya ku mutanena! Kun taɓa jin wata maganar ƙarya daga gare ni?” Dukkansu gaba ɗaya suka ce: “A’a, ba mu taɓa ji ba.” Ya ce: “Allahu Ta’ala Ya ba ni annabta, Ya aiko ni gare ku annabi.” Sannan ya karanta aya ta ɗari da hamsin da takwas ta Suratul A’araf, wadda ma’anarta: “(Ya MasoyiNa!) Ka ce musu: ’Ya ku mutane! Ni manzon Allahu Ta’ala ne, Mamallakin ƙasa da sammai, wanda aka aiko zuwa ga dukkanku. Shi ne Yake kashe kowane mai rai, Yake rayarwa. Babu abin bauta (da ya cancanci bauta) sai Shi.’” Daga cikin masu sauraro, baffansa Abu Lahab ya yi fushi, ya yi ihu, yana nacewa a kan kafirci: “Ɗan ɗan’uwana ya haukace! Kada ku saurari maganar wanda ba ya bauta wa gumakanmu, wanda ya rabu da addininmu!” Waɗanda suke wurin suka watse, babu wanda ya yi imani. Duk da cewa sun san Shugabanmu Annabi mai gaskiya ne, mai ɗabi’u masu ɗaukaka, suka kau da kai daga gare shi, suka zama maƙiyansa.
“Ka tsoratar da danginka na kusa da azabar Allah, ka kira su zuwa ga addinin gaskiya” Shu’ara’i: 214
Wata rana kuma, bisa umarnin Allahu Ta’ala: “Ka bayyana abin da aka umarce ka da shi (umarni da hani)”, Shugabanmu Annabi ya sake hawa tudun Safa. Da murya mai ƙarfi kuma babba ya kira mutane: “Ya sabahah! Ku zo nan, ku taru, ina da wani muhimmin labari a gare ku!”20 Bayan wannan kira ƙabilun suka taru da gudu. Suka fara jira cikin mamaki da marmarin sani. Waɗanda ba su zo ba suka aika da mutanensu domin su san dalilin taruwar. Wasu daga cikin waɗanda suka zo suka fara tambaya: “Ya Muhammadul-Amin! Don me ka tara mu a nan, mene ne za ka sanar?” Shi kuwa ya fara maganarsa da kiran: “Ya ku ƙabilun Ƙuraishawa!” Kowa yana saurararsa da babbar kulawa. Ya ci gaba da maganarsa: “Halina da ku yana kama da halin mutumin da ya ga maƙiyi, ya ruga domin ya sanar da iyalinsa, kuma saboda tsoron kada maƙiyin ya riga shi isa ga iyalinsa ya cutar da su, ya yi ihu: ‘Ya sabahah!’ (Maƙiyi ya kewaye mu! Safiya ta zo! Ku shirya yaƙi da sauri!) Ya ku jama’ar Ƙuraishawa! Idan na ce muku: a bayan wannan dutse akwai wata rundunar maƙiya, tana gab da kai muku hari, za ku gaskata ni?” Suka ce: “I, za mu gaskata. Domin har yanzu ba mu taɓa shaida kome a tattare da kai ba sai gaskiya. Ba mu taɓa ganin ka yi ƙarya ba!…”
Sai ya lissafa sunayen dukkan ƙabilun Ƙuraishawa: “Ya ku ƴaƴan Hashim! Ya ku ƴaƴan Abdu Manaf! Ya ku ƴaƴan Abdulmuɗɗalib!”, ya ci gaba kamar haka: “Ni mai sanar da ku ne game da azaba mai tsanani, wadda zuwanta babu shakka. Allahu Ta’ala Ya umarce ni da in tsoratar da dangina na kusa da azabar Lahira. Ina kiranku zuwa ga imani da faɗar: La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu (Allah ɗaya ne, babu abin bauta sai Shi). Ni kuma bawanSa ne da manzonSa. Idan kuka yi imani da wannan, za ku shiga Aljanna. Muddin ba ku ce ‘La ilaha illallah’ ba, ba zan iya samar muku da wani amfani a duniya ba, ko wani rabo a Lahira.” Daga cikin ƙabilun da suke sauraro, Abu Lahab ya ce: “Saboda wannan ka tara mu?”, ya jefi ƙaunataccen Annabinmu da dutsen da ya ɗauka daga ƙasa. Daga waɗansu ba a sami irin wannan gaba ba; suka watse suna magana a tsakaninsu.21
Ko da sun ba ni rana a hannun dama!
Bayan waɗannan kirace-kirace, duk inda ƙaunataccen Annabinmu ya ga wani mutum ko wata jama’a, yakan bayyana musu Musulunci. Ya sanar da cewa tsira ta gaskiya tana yiwuwa ne kaɗai ta hanyar nisantar bin son rai, zalunci, rashin adalci da kowane irin mummunan aiki, da kuma yin imani da Allahu Ta’ala. Masu bin sha’awoyin ransu da sha’awoyinsu, masu danne marasa ƙarfi da masu wuce gona da iri a ɓata suka yi tsananin adawa da wannan. Da suka ga cewa za a kawo ƙarshen dukkan waɗannan ɓatattun ayyukansu, suka musanta abin da Muhammadu alaihis-salam ya sanar. Suka zama maƙiyansa da na masu imani. Mushrikai da farko suna izgili. Sannan suka yanke shawarar ƙara matsin lamba da azabtarwarsu. Suna son su tsoratar da muminai, su kashe da’awar Musulunci. A sahun gabansu akwai Abu Jahal, Utba, Shaiba, Abu Lahab, Uƙba ɗan Abu Mu’aiɗ, As ɗan Wa’il, Aswad ɗan Muɗɗalib, Aswad ɗan Abdu Yaghus, Walid ɗan Mughira…
Wata rana Utba, Shaiba da Abu Jahal suka ce wa Abu Ɗalib: “Kai babbanmu ne. Koyaushe muna girmama ka, muna ɗaukaka ka. Yanzu kuwa ɗan ɗan’uwanka ya kafa wani sabon addini. Yana zagin gumakanmu, yana zargin mu da kafirci. Ka yi masa nasiha. Ka hana shi wannan aiki. Idan bai daina ba, mun san yadda za mu yi da shi…”
Abu Ɗalib ya lallashe su, ya sallame su; domin kada Annabinmu ya yi baƙin ciki kuma, ya ɓoye masa al’amarin. Bayan ɗan lokaci mushrikai suka sake taruwa, suka zo wurin Abu Ɗalib, suka ce: “Mun riga mun zo wurinka a baya, mun sanar da kai halin da ake ciki. Ba ka kula da maganarmu ba. Shi kuwa har yanzu yana ci gaba da zagin gumakanmu. Yanzu haƙurinmu ya ƙare. Za mu yaƙe ku, ku biyu, har zuwa ɗigon jininmu na ƙarshe. A Makka, ko dai shi ko kuma mu, ɗaya zai ɓace.” Abu Ɗalib ya yi ƙoƙarin lallashe su, amma suka dage a kan taurin kansu.22
Kamar yadda Abu Ɗalib ba ya son a ɓata wa Shugabanmu Manzon Allah rai, haka kuma ba ya son wata ƙiyayya ta shiga tsakaninsa da mutanensa. Ya zo wurin Annabinmu ya ce: “Ya Muhammadu! Dukkan mutanen ƙabila sun haɗa kai a kan ƙiyayyarka, sun zo wurina da ƙara. Ƙiyayya a tsakanin dangi ba abu ne mai kyau ba. Suna son kada ka kira su kafirai, kada kuma ka ce suna kan ɓatacciyar hanya, ka riƙa zaginsu.” Sai Habibi Mafi Daraja ya ce:
“Ya baffa! Ka sani: ko da sun sanya rana a hannun damana, wata kuma a hannun hagu na (ko mene ne suka yi mini alkawari), ba zan taɓa barin wannan addini ba, ba kuma zan daina isar da shi ga mutane da sanar da shi ba. Ko dai Allahu Ta’ala Ya yaɗa wannan addini a dukkan duniya, aikina ya ƙare, ko kuma in sadaukar da raina a kan wannan hanya.” Sannan ya miƙe tsaye. Idanunsa masu albarka sun cika da hawaye.
Da Abu Ɗalib ya ga Shugabanmu Manzon Allah ya yi baƙin ciki, ya yi nadamar abin da ya faɗa, ya rungume shi a wuya, ya ce: “Ya ɗan ɗan’uwana! Ka ci gaba da hanyarka, ka yi abin da kake so. Muddin ina da rai, zan kare ka, in tsare ka.”23
Lokacin da mutane goma daga cikin manyan mushrikai suka fahimci cewa Abu Ɗalib yana kare Sayyidina Muhammadu, suka ɗauki Umara ɗan Walid tare da su, suka je wurin Abu Ɗalib. Suka yi masa wata shawara da ba za a iya karɓa ba: “Ya Abu Ɗalib! Ka sani, wannan Umara shi ne mafi kyau, mafi ƙarfi kuma mafi kyawun ɗabi’a a cikin samarin Makka. Ban da haka kuma mawaƙi ne. Mu ba ka shi, ka yi amfani da shi a ayyukanka. A madadin Umara kuma ka ba mu Muhammadu, mu kashe shi. Mutum a madadin mutum! Me kuma kake so?” Abu Ɗalib ya husata ƙwarai da wannan magana, ya ce: “Ku fara ba ni ƴaƴanku. Ni in kashe su. Bayan haka zan ba ku ɗan ɗan’uwana.” Da mushrikai suka fahimci tsananin al’amarin, suka ce: “Ai ƴaƴanmu ba sa yin abin da yake yi…” Abu Ɗalib ya ce: “Na rantse, ɗan ɗan’uwana ya fi dukkan ƴaƴanku gaba ɗaya alheri. Wato ku ba ni ɗanku in riƙa ciyar da shi, ku kuma ku ɗauki ƙwayar idona ku kashe shi, ko?!… Ko taguwa ma ba ta begen kowa, ba ta tausaya wa kowa, sai ɗanta. Wannan al’amari ya yi nisa da hankali da tunani. Yanzu al’amarin ya wuce iyaka. Duk wanda yake maƙiyin ƙwayar idona Muhammadu (alaihis-salam), ni ma maƙiyinsa ne. Ku san wannan haka, kuma ku yi duk abin da za ku iya!”24 Mushrikai suka tashi daga wurin cikin fushi, suka tafi. Nan take Abu Ɗalib ya tara ƴaƴan Hashim da ƴaƴan Abdulmuɗɗalib. Ya bayyana musu halin da ake ciki, ya rinjaye su su taimaki ƙaunataccen Annabinmu (sallallahu alaihi wa sallam). Hannuwan da za su ɗagu domin kashe Manzon Allah za a karya su. A kan wannan al’amari suka haɗa kai a kan mushrikai. Abu Lahab kaɗai bai shiga ba. Abu Ɗalib ya ce musu: “Ya ku jarumai! Gobe kowannenku ya rataya takobinsa a ƙugunsa, ya biyo ni!”
“Ya baffa! Ka sani: ko da sun sanya rana a hannun damana, wata kuma a hannun hagu na (ko mene ne suka yi mini alkawari), ba zan taɓa barin wannan addini ba, ba kuma zan daina isar da shi ga mutane da sanar da shi ba. Ko dai Allahu Ta’ala Ya yaɗa wannan addini a dukkan duniya, aikina ya ƙare, ko kuma in sadaukar da raina a kan wannan hanya” Ƙaunataccen Annabinmu Muhammadu alaihis-salam
Washegari Abu Ɗalib ya tafi gidan Shugabanmu Annabi, dukkansu tare suka nufi Harami mai daraja. Jaruman ƴaƴan Hashim suna biye da su. Suka isa Ka’aba, suka tsaya a gaban mushrikai. Abu Ɗalib ya ce wa mushrikai: “Ya ku jama’ar Ƙuraishawa! Na ji cewa kun yanke shawarar kashe ɗan ɗan’uwana. Shin kun san cewa waɗannan samari da suke bayana, hannuwansu a kan takubbansu, suna jiran alamata cikin rashin haƙuri? Na rantse, idan kuka kashe Muhammadu, ba zan bar ko ɗayanku da rai ba!…” Bayan haka ya fara karanta waƙoƙin yabon ƙaunataccen Annabinmu. Mushrikan da suke wurin, tun daga Abu Jahal, suka watse.
